Connect with us

WASANNI

Dole Sai Mun Hana Ronaldo Sakat Idan Muna Son Doke Real Madrid -Klopp

Published

on

 

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liberpool, Jugen Klopp ya bayyana cewa idan har suna son samun nasara akan Real Madrid dole sai sun hana Ronaldo motsi domin idan yasamu dama baza suji da dadi ba.

Klopp ya bayyana hakane a ranar Lahadi a shirye shiryen da kungiyarsa takeyi na fafata wasan karshe da Real Madrid a wasan karshe da za su fafata na cin kofin zakarun turai a ranar Asabar a babban birnin Ukraine wato Kieb.

Ronaldo dai yana kan ganiyarsa wajen zura kwallo a raga bayan daya zura kwallaye 30 daga watan Janairun wannan shekarar zuwa yanzu kuma ya taimakawa kungiyar tasa ta kare a matsayi na uku.

Har ila yau, Ronaldo yana shirin lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya karo na shida a jere duk da cewa yana takara da Messi da Muhammad Salah na Liberpool

Klopp ya ce Ronaldo yafi Salah saboda yakai kusan shekara goma tauraruwarsa tana haska kuma yanada wata irin zuciya wadda ba kowanne dan wasa bane yake da ita.

Ya ce za su yi kokarin ganin sun dakatar da Ronaldo a wasan karshen da za su buga duk da cewa ba shi kadai bane dan wasa mai hatsari a kungiyar kuma yanada baiwa wadda ba kowane yake da ita ba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: