Connect with us

LABARAI

Faduwar WAEC Da NECO A Arewancin Najeriya!

Published

on

07066366586                             ibrahimba182@gmail.com

*Me ye sababi?

*Laifin waye?

*Ina mafita?

Na jima Ina nazari a game da yadda dalibai ke faduwa a jarabawar hadakar yammacin Afrika (WAEC) da babbar jarabawar ‘Kasa ta (NECO), wanda a kowace shekara al’amarin kara ta’azzara yake yi. Tun a shekaru kusan goma sha da suka shud’e dalibai suka samu kansu cikin takaicin rashin samun nasara a jarabawowin, musamman WAEC. Na kai makura wajen nazarin sababin faruwar hakan, amma haka ba ta cimma ruwa ba, in da a karshe na koma ga laluben dalilan da zan iya dogaro da su. Da yawa cikin mutane suna nuna nadamar rubuta jarabawar a duk yayin da sakamako ya bayyana, domin sakamako ne marar kyau.

Da yawa cikin mutane suna ta lalube cikin sabuban dake jawo wannan faduwa, inda suke dora alhakin akan malaman makarantu, domin suna ganin malaman ne ba sa koyarwa bisa ka’ida, hakan sai ya sanya dalibai rashin sanin amsoshin da ake tambaya a jarabawar. Wasu kuwa na ganin gazawar gwamnati ce a matakin jihohi, domin gwamnatin ce ba ta bayar da gudumawar da ya kamata tun a mataki na farko a sakandare, sannan ta fuskar malamai ba sa bayar da horo na musamman ga dalibai, musamman a yayin da suke shekaru biyun karshe na kamala makarantunsu na sakandare. Duk wadanda ke ganin wannan ne dalili to sun kuskure, domin akwai masu maimaita rubuta jarabawar (edternal student), wadannan kuma ba daliban makarantar ba ne na asali. Wasu na ganin laifin iyaye ne, domin ba sa horon yaransu da su yi karatu. Shi ma dalilin can da na kawo zai kore wannan tunani. A iya nazari na, tun daga lokacin dana samu kai na a matsayin Principal na d’aya daga cikin makarantun kudin (Pribate School) dake garin mu, na ga cewar laifin na shugabanni ne da kuma iyaye. Na san za a yi mamakin hakan, tabbas kowa ya yi tarayya cikin laifin, tun daga malamai, iyaye da hukumomin ilimi, amman hakkin ya fi karkata ga shugabanni ne.

Za ku yarda da ni idan kuka ga yadda makarantu kudi ke cin jarabawowin a kowace shekara. Kamar yadda bayanai ke yawo a tsakanin al’umma makarantun kudi kan bi jarabawar dalibai kai tsaye zuwa wurin da ake makin domin dalibansu su ci jarabawowin, wannan ne ya sa duk rashin kokarin ka matukar ka rubuta a nan za ka ci, a wasu makarantun ma za a tsadance ne da kai, fefa nawa kake so? Wannan shi ne abin da yakamata gwamnatocinmu su yi domin samarwa da ‘ya’yansu makin. Idan kuwa haka ne, me zai hana a gyara harkar ilimin gaba d’aya, ma’ana a yi tankad’e da rairaya ga wadanda ke rubuta jarabawa a duk shekara, sannan a tantance wadanda za su koyar, wadanda ba su cancanta ba a tura su makaranta domin ‘karo ilimi, a sabunta (kundi) syllabus wanda zai dace da kwakwalwar dalibai. Uwa-uba, a samu kayan aikin ingiza koyarwa a kowace makaranta. Na tabbata idan an yi hakan za a samu raguwar fad’uwar jarabawar. Domin faduwar jarabawar na da illoli ga al’umma wanda hankalin shugabanni bai kai ga ganowa ba. Kadan daga ciki: mayar da matasa ‘yan daba ko kalare ko ecnmog ko sara-suka, mayar da su ‘yan maula, ‘yan zaman kashe wando da dumama benci, mayar da su marasa manufa a rayuwa, mayar da su ‘yan ‘kwaya, mayar da su mabarata, a wasu lokutan ma ya kan kai su ga tabin hankali. Wannan kuwa, babbar illa ce da za ta zagwanyar da dukkanin al’ummar da ta samu kanta cikin wannan hali, al’ummar da matasanta suka shiga wannan hali, to ta gama zagwanyewa, don matasanta ba su da manufa sakamakon rashin tsarin matasanta.

Wajibin kowacce gwamnati ne ta samar da ingantaccen ilimi ga matasanta, wanda zai zama madafa ta rayuwarsu da kuma ci gaba da gina wannan al’umma. Sannan dukkanin dalibin da ya fadi, to wajibi ne a samar da wani aji na musamman domin maimaici na tsawon shekara guda, san
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: