Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Kotu Ta Yanke Wa Tsohuwar Muhutin Kotu Zaman Gidan Yari Na Shekaru 7

Published

on

Kotu ta yakewa mataimakin mahutin babbar Kotun dake jihar Oyo Mutiat Omobola Adio hukuncin zaman gidan Yari na shekaru bakwai saboda aikata almundaha.

Mutiat Omobola Adio Hukumar yaki da cin hanci da rashawa(EFCC) ce ta bukaci a yankewa matar tsohuwar ma’aikaciyar babbar kotun dake jihar Oyo  Mutiat Omobola Adio hukuncin zaman gidan Yarin.

Mai Shari’a Aklalin babban kotun ta Oyo O. M. Olagunju dake da zama a garin Ibadan, ta samu Mutiat Adio akan zargi guda biyu.

Zargin guda biyu su ne na karbar naira miliyan 9.2 a bisa tabka karya daga wurin wani mai suna  Abiodun Olonade dan Nigeriya mazaunin kasar Ireland.‎

Wacce aka yankewa hukuncin Adio, an yake masa hukuncin ne ba tare da biyan wata tara ba kuma Kotun ta umarci ta data maida wa da Abiodun Olonade kudin sa.

Wadda aka yankewa hukuncin, ta damfari Abiodun Olonade ne a ranar 19 ga watan Disambar 2016 ta hanyar wani mai suna Alhaji Yekini Olonade Kunle Abimbola a bisa cewar, kudin aikin gini ne dake lamba 10, Block DDLB na sashen rukunin gidajen dake  Bashorun a cikin karamar hukumar Lagelu dake garin Ibadan.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: