Connect with us

KIWON LAFIYA

Masu Ciwon Sankarar Jini Suna Iya Ajiye Azumi –Badiyya

Published

on

Hajiya Badiyya Magaji Inuwa sananniya ce a jihar Kaduna musamman wajen tallafawa masu fama da Sikila kyuta a karkashin kungiyar mai suna: Sickle Cells Promotion Center dake da babban ofishin ta a anguwar Dosa cikin Kaduna. A hirar ta da ABUBAKAR ABBA, ta yi bayani akan yadda masu larurar ke sha wahala in suna yin Azumin watan Ramadan da kuma lokacin damina da kuma sauran kalubalen da kungiyar tata take fuskanta.

Gashi yanzu damina ta fara kankama, shin a wannan yanayin ya ya rayuwar masu fama da larurar take shiga?

Assalamu Alaikum Warahamatullahi Wabarakatuhu. Kamar yadda ka yi wannan tambayar a cikin wannan lokacin na damina da muka shiga, babban abinda za a lura dashi shi ne, maleriya tafi tayar masu da ciwon, kuma dama in ana damina ana samun sauro, shi yasa wani lokaci mukan raoki gwamnati cewar in suna da gidan sauro, su tainaka mana don mu rabawa masu larurar domin a kiyaye.

Haka kuma yara masu larurar da suke zuwa makaranta, ya kamata iyaye su kiyaye cewar su fadakar da ‘yayan su idan ana ruwan sama yaran su samu inda za su fake bawai su shiga gidajen mutane ba domin wani gidan ba a san gidan da za su shiga ba, ko da bakin titi ne da suka ga mutane sun fakewa ruwan sama suma suna iya rabawa su fake har sai ruwan ya dauke bawai suyi ta shiga cikin ruwan suna tsalle ba, dole wannan aikin iyaye su fadakar da ‘ya’yan su.

Idan kuma da safe aka tashi da ruwan sama da bai daukewa da wuri kuma akwai sanyi sosai, mai makon a tura su makarantar kuma ruwan ya bige su wanda zai iya janyo su kwanta rashin lafiyar da za su har kwanan bakwai in aka hana su zuw makarantar wannan ranar kawai, toh kila washe gari za su iya zuwa makarantar. Haka suma malaman makarantun da yaran ke zuwa ya kamata a fadakar dasu cewar koda yaran sunyi latti ko basu zo ba a wannan ranar don Allah iyaye suyi masu bayani cewar saboda larurar sune yasa basu zo makarantar ba domin likitoci sunce aki yaye shi yasa aka kiyaye kada malaman su yi zafin zuciya su ce za su ba su wani horo domin shi kanshi horon, zai iya tayar masu da hankali.

Idan watan Ramadan ya zo ki kan yi kiraye-kiraye, musamman don malamai su rika yin bayani wajen wayar wa iyayen da ‘yayansu ke fama da larurar, wanne shiri ki ka yi a wannan Azumin na bana wajen kiraye-kirayen?

Farkon janairun wannan shekarar muka cika shekaru goma da fara wannan aikin na taimakawa masu fama da larurar kyauta, in kuma akwai larurar data fi karfin mu sai mu tura ga likitoci, toh abinda na lura shekaru na biyu dana fara, sai naga in an gama salla bayan Azumi, sai yara su dade basu zo karbar maganin wata-wata ba in na tambaye su sai suce ai suna asibiti tun cikin azumi ko bayan azumi, in na tambaye su kwanan su nawa wasu su ce mako biyu wasu uku, sai in tambaye dama haka suke?

sai su ce a’a suna yin kwana biyar ko uku an sallame su, ai shekara ta daya har ta biyu na gani, sai na tambayi kaina kodai rashin shan ruwa ne saboda yaran suna Azumi tunda ruwa bai ishe su ba tunda mu munsan ko asibiti aka kaisu taimakon farkon nan shi ne ayi masu karin ruwa.

Toh ni dai ba likita bace sha’awa ce ta sani kuma nima uwar ‘yaya ce masu sikila na shiga don in tallafa don a nemo duk hanyar data dace don yaran nan su zamo a cikin koshin lafiya, sai na ga in na yi magana za a ce na soki addini cewar na hana yara suyi Azumi sai na je wurin Sheikh

Ahmad Gumi na gaya mashi na lura idan yaran sunyi Azumin suna shan wuya me ya kamata a yi? Sai ya yi shiru ya ce, ba zan ce komai ba amma, ki je ki samu likita musulmi su yi bayani akan me addinin Musulunci ya ce akan mararar lafiya.

Sai na je na samu Farfesa Indo Mamman, ita ce shugabar kwayar jini a asibitin Shika muka yi magana na fada mata ga yadda muka yi da Shekh Ahmad sai ta yi min bayani cewar gaskiya in son so ne su huta, masu yi, musamman sikila na wani yafi na wani, suna iya bari, amma in

sun matsa domin sha’ani ne na addini ba za mu iya gamsar da mutane akan komai ba.

Ta ce shawarar data ke son ta bayar idan sikila yana son yin Azumi a gaya masu daga Magariba su tabbatar da sun sha ruwan robar Swan uku su shaye shi kafin asuba, in har sun shaye ma ba garanti ne za su zauna cikin koshin lafiya ba, in kuma har sun kai Azumin ranar, amma basu ji dadi ba toh kar su dauki na gobe su tsaya su huta, in ba haka ba kuwa

rashin yin Azumin yafi masu ko kuma in suka yi daya, a kwana daya ba’a yi ba yadda baza su sha wahala ba.

Na koma wajen Malam na ce masa ga abin da likitar ta ce, ya ce toh shi ma ya gamsu a yi masu bayani domin Allah ya ce idan ba a da lafiya ba sai an yi azumin ba.

Kin yi maganar ruwan gora, to talaka mai fama da larurar in baida kudin sayen ruwan gorar fa?

Zai iya shan na leda ‘Pure Water’ yana iya shan kamar guda goma a cikin daren, idan ma ruwan famfo ne zai iya sha sai ya auna kamar yawan ruwan leda ‘Pure Water’ goma ya sha daga magriba zuwa Asuba, domin wannan ruwan ana fatan zai tsaya a cikin tsokar jikin sa ba zai ji ya bushe ba, wato ya kafe yadda jinin ba zai rika gudana ba.

Wacce shawara za ki ba iyaye da ‘yayan su ke fama da larurar?

Iyaye musamman maza suna bayar da hadin kai wasu kuma basa bayar da hadin kai musamman wajen sayen kayan da ya kamat yayan su masu larurar ya kamata iyayen su saya masu. Shi wannan ciwon ba’a gadon shi ya kamata kafafen yada labarai su

dinga fadakar da alumma ko kuma masu hannu da shuni su dauki nauyin kafafen yada labari don a dinga wayarwa da alumma kai.

Wacce shawara za ki ba wanda suke shirin yin aure don su san jinsin su kafin yin auren?

Akwai wata hallitar jini wato kwayar haliita ce ta jini guda biyu da Allah ya halitta, in kai sa’a ka samu A/A wato lafiyayyar kwayar jinni ke nan in kuma baka yi sa’a ba, ka samu daya mai kyau daya maras kyau wato A/S. Saboda haka ya kamata wadanda za su yi aure suje asibiti don su san menene jinsu don gudun kada su haifi yariri ko jaririyar da za su jefa su a cikin matsala harda su kansu iyayen.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: