Soja Sun Kusa Kawo Karshen Yaki Da Kungiyar Boko Haram -Tijjani Gamawa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Soja Sun Kusa Kawo Karshen Yaki Da Kungiyar Boko Haram -Tijjani Gamawa

Published

on


An bayyana samun gagarumar nasara a shiyyar Arewa maso gabas game da lamarin da ya Shafi yaki da kungiyar boko haram mai gwagwarmaya da makamai a Nigeria.
Air kwamando Ahmed Tijjani baba Gamawa mai ritaya shine ya bayyana haka cikin hirarsa da manema labarai a Bauchi, Inda ya bayyana cewa an samu gagarumar nasara a karkashin sojan hadin guiwa na nijeriya da nijer da Kamaru da Chadi, ya kara da cewa abin da ke faruwa a halin yanzu na tayar da bama baman kunar bakin wake lamari ne ya yaki ya gaji haka, amma a zahiri an ci karfin kungiyar boko haram kakkabe gyauron su ya rage kuma wannan tirjiyace ta abokan gaba.
Tijjani baba Gamawa ya yaba game da kwazon kwamkndojin sojan nijeriya da babbkn hafsan kasa T. Yusuf burutai da kwamandan askarawan sojan sama air bice Marshal Baba Abubakar sadik game da kokarin da suka yi na wannan yaki. Don haka ya bukaci jamaa su ci gaba da yin adduah da kuma tona asirin miuagu don a samu nasara kakkabe miyagun mutane masu tayar da hankalin jamaa a kasar nan.

Advertisement
Click to comment

labarai