Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 15 Tare Da Ceto Mata Da Yara 49 A Borno — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 15 Tare Da Ceto Mata Da Yara 49 A Borno

Published

on


A Laraba makon jiya ne Rundunar sojojin Nijeriya ta samu nasarar hallaka wasu mayakan Boko Haram su sha biyar, hade da cuto mata da yara su arba’in da tara da ‘yan Boko Haram suka yi awun gaba da su a Kudancin Tafkin Chadi.

Mukaddashin jami’in hulda da jama’a ta rundunar  Operation Lafiya Dole, Konal Onyema Nwachukwu, shine ya shaida hakan a garin Maiduguri ta cikin sanarwar manema labaru da ya fitar.

Ya bayyana cewar wasu daga cikin mayawan Boko Haram din sun bakwanci lahira ne a lokacin da suka yi tozali da sojojin a Chad Island inda wasu kuma suka hadu da fushin sojojin a Kudancin Borno a ranar Talata.

Ta bakinsa, “Sojojinmu sun gamu da mayakan ne a moboyarsu, sun samu nasarar kashe ‘yan Boko Haram 11 a kauyen Gomaran da ke Kudancin tafkin Chadi,” In ji Kakakin Soji.

Ya ci gaba da bayanin cewar sun kuma samu nasarar kashe wasu mayakan hudu a lokacin da suka kubuce daga hanun sojoji suka arci na kare inda suka kuma bakwanci lahira a Kudancin Borno.

Nwachukwu ya bayyana cewar sojojinsu ba su kuma tsaya haka ba, sun kuma fuskacin mayakan Boko Haram a Firgi da Moula, dukkaninsu da suke Bama  da Dikwa.

Ya bayyana cewar a yayin samamen da suka kai din, sun yi nasarar kwato wasu muggan bindigogi daga hanun mayakan Boko Haram din da suka kunshi bindigogi samfuri daban-daban, motoci Babura da sauran ababen da suka kwato.

Ya kuma shaida cewar nasararsu ba ta tsaya haka ba, sun kuma samu nasarar kubutar da wasu da ‘yan Boko Haram din su yi garkuwa da su, “Maza hudu, mata 33 da kuma yara 16 dukkaninsu sojojinmu sun samu nasarar kubutar da suka daga maboyar Boko Haram. Yanzu haka muna kokarin hannata su ga hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira domin ci gaba da tallafo rayuwarsu,”Inji Nwachukwu.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!