Connect with us

WASANNI

Watakila Arteta Ya Zama Kociyan Arsenal A Wannan Makon

Published

on

Bayanai sun ce mataimakin mai horar da kungiyar Manchester City, Mikel Arteta na kan gaba, a tsakanin takwarorinsa da ake fatan ganin sun karbi ragamar horar da kungiyar Arsenal.

Arteta wanda tsohon dan wasan tsakiya na Arsenal ne, ya bugawa kungiyar wasanni 150, kafin daga bisani ya zama mataimakin mai horar da kungiyar Manchester City a shekarar 2016.

Har yanzu dai babu tabbacin wanda zai maye gurbin Arsene Wenger daga hukumar Arsenal, sai dai kungiyar ta jaddada kwarin gwiwar bayyana sabon mai horar da ita kafin fara gasar cin kofin duniya a ranar 14 ga watan Yuni mai zuwa.

Sauran wadanda ake dangantawa da karbar horar da kungiyar ta Arsenal sun hada da tsohon mai horar da Barcelona Luis Enrikue, da kuma mai horar da Jubentus Massimiliano Allegri.

Shima tsohon kociyan kungiyar ta Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana cewa Arteta ya cancanta ya zama wanda zai gajeshi saboda kwarewarsa da kuma iya shugabancinsa.

 

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: