Connect with us

WASANNI

Buffon Ya Yi Bankwana Da Juventus Bayan Shekaru 17 A Kungiyar

Published

on

Mai tsaron raga na Jubentus Gianluigi Buffon, dan kasar Italiya, ya samu kyaututtuka da karramawar magoya bayan kungiyar, bayan da ya kawo karshen wasa a cikinta a fafatawar da suka yi da Berona.

Ya yin wasan da Juvbentus ta lallasa Berona da 2-1, an canza Buffon a mintuna na 63, domin bashi damar ganawa da magoya bayansa, wadanda suka karrama shi ta hanyar mikewa tsaye baki daya.

A shekarar 2001 Buffon ya sauya sheka daga kungiyar Parma zuwa Juventus akan fam miliyan 32, wanda a waccan lokacin ya kafa tarihin zama mai tsaron raga mafi tsada a duniya.

Tuni dai kungiyar Paris St-Germain ta yi wa Buffon tayin buga mata wasa, ya yinda a Juventus ta yi masa tayin mukamin zama daga cikin mataimakan masu horarwa.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: