Connect with us

NISHADI

Fim Din Juyin Sarauta Ya Zama Zakaran Gwaji Dafi *Mu Na Fata Ya Karbu A Kasuwa Kamar Yadda Ya Karbu A Gasa –Ramat

Published

on

A fagen shirin fim na kannywood kusan za a iya cewa fim din Juyin Sarauta ya zama zakaran Gwajin dafi wajen samun kyaututtuka musamman idan aka yi duba da cewar har yanzu fim din yana mataki ne na shirin shiga kasuwa, domin kuwa har yanzu ba a riga an sake shi a kasuwa ba, amma fim din shi ne ya lashe kambun kyautar Best Nigerian Language a Zuma Award na 2017, yayin da kuma a wannan shekarar ya lashe kyautuka har guda shida bayan da ya samu fitowa gasa 14 cur a gasar AMMA Award da aka yi a Katsina a satin da ya gabata. Hakan ya nuna cewar fim din ya samu nasarar da ake ganin babu wani fim din Hausa da bai kai ga fitowa a kasuwa yanzu ba da ya samu gagarumar wannan nasara, wanda hakan ta sa ake ganin fim din zai kafa tarihi a cikin finafinan Hausa da su ka fi tasiri da jan hankali.

Balaraba Ramat Yakubu ita ce marubuciya kuma mai daukar nauyin shirin fim din. Wakilinmu ya ji ta bakinta a game da irin nasarar da fim din ya ke samu da kuma ko wanne irin buri ta ke so ta cimma a game da fim din Juyin Sarauta, inda ta fara da cewa, “to muna godiya ga Allah duk da cewar Juyin Sarauta bai shiga Kasuwa ba yadda jama’ar gari za su gan shi,amma sai ga shi ya samu kambun karramawa har guda 7 kuma ya samu damar kaiwa ga matakin shiga gasa har guda 9. Kuma a can baya a gasar karramawa ta Afirka wato ZUMA AWARD fim din ya samu cin gasa a matakin harshe kuma mun samu nasarar kaiwa ga matakin shiga gasar fitaccen jarumi.”

Ta ci gaba da cewa, “a yanzu a AMMA AWARD da aka yi yanzu mun samu kaiwa ga matakin shiga gasar har a waje 14 kuma mun yi nasara mun dauki kambu guda 6 mun samu a matakin rubuta labari wadda ni ce na rubuta kuma a matakin jarumi Ado Ahmad Gidan Dabino ya zo na daya, sai mai daukar hoton mu  shi ma ya samu sai wajen sutura nan ma fim din Juyin Sarauta ya yi nasara, haka nan wajen tsara wajen da za a yi fim din nan ma mun samu cin gasa ka ga wannan babbar nasara ce.

“Duk da cewar mun san cewar idan fim ya samu shiga matakai da yawa har suka kai 14 kuma babu wani fim da ya samu kamar Juyin Sarauta amma dai ba mu samu kaiwa ga gwarzon fim na shekara ba kuma mafi yawan mutane suna da ra’ayin idan fim yasamu nasara da yawa  to shi ne yake zama gwarzon fim na shekara. Sai dai kuma a AMMA AWARD sai abin ya canza amma dai duk da haka abubuwan da muke samu ya nuna wa mutane cewar mun taka muhimmiyar rawa.”

Ta kara da cewa, “kuma a yanzu abin da muka sa a gaba,  shi ne kokarin nuna  fim din a Sinima kafin ya shiga kasuwa. Kuma fatan mu  shi ne yadda fim din ya samu karbuwa  da cin kyautuka to a Sinima ma ya samu karbuwa da ta wuce haka don haka ma muna son mu ga an fara nuna shi a wannan karamar salla mai zuwa amma dai har yanzu ba mu tsayar da gari ko Sinimar da za a fara nuna shi ba.

“Muna fatan yadda muka zuba kudi a fim din to kudin ya dawo har ya linka mu ci ribar da za mu samu damar yin wasu masu yawa nan gaba. Saboda mun kashe wa fim din kudi sosai, an ba mu kyauta,  mun debo namu mun zuba, mun ci bashi. Don haka muke fatan fim din ya samu karbuwar da kwalliya za ta biya kudin sabulu.”

Daga karshe Hajiya Balaraba Ramat ta yi kira ga masu gudanar da harkar fim da su cire kyashi da son zuciya su zamo abu guda ta yadda in mutum dayk ya yi nasara a cikin su su rinka kallon su ne suka yi nasara, ba wai a koma gefe ana yin kananan maganganu ba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: