Connect with us

Uncategorized

Gwamnatin Bauchi Ta Rushe Ofishin Jam’iyyar Adawa Ta NNPP

Published

on

A Jiya Lahadi ne aka ayi gari hukumar kula da tsara birane SDB ta jihar Bauchi ta rushe daya daga cikin ofis din jam’iyyar adawa ta NNPP da ke cikin garin Bauchi, inda aka yi rugu-rugu da ofishin.

Jam’iyyar Adawa ta NNPP ta zargi gwamnati mai ci ta (APC) a jihar da fito da adawarta karara a kan jam’iyyar ta NNPP a bisa rushe mata daya daga cikin ofishohinta da gwamnatin jihar ta yi.

Ofishin da gwamnatin ta rushe wacce ke da matsuguni a kwanan shataletalen Jos da ke cikin Bauchi wacce gwamnatin ta rushe a sakamakon aikin hanya ta biyo ta ofishin.

Har-ila-yau, jam’iyyar ta kuma yi zargin cewar gwamnatin APC ta rushe mata ofishin ne domin ta yi mata barazana da kuma hana ta katabus wanda kuma hakan bai zai razanar da ita ba kamar yadda ta shaida.

A wani taron manema labaru da su jam’iyyar ta kira a ranar Asabar, Sakataren jam’iyyar ta NNPP a jihar Bauchi Mahmood Baba Ma’aji ya bayyana cewar wannan sakatariyar da gwamanti ta ruguza musu shi ne mafi girma na biyu da suke da shi a jihar, yana mai bayanin cewar sun karbi hayan ofishin ne a wajen mamallakinta Alhaji Musa Dan Kyarana.

Ya ke cewa, “Mun damu matuka gaya a bisa yadda hukumar tsara gine-gine ta jihar Bauchi ‘Bauchi State Debelopment Board’ ta nemi rushe mana ofis a bisa cewar suna ci  gaba da gudanar da aikin hanya,”

Ya bayyana cewar tuni gwamnatin ta kammala aikin titin har ma da kwalbati-kwalbati da aka tsara za a yi kuma bai shafi jikin ofishin nasu ba.

Ya bayyana cewar yunkurin rushe musu ofishin da gwamnatin ke shirin ya saba wa doka, domin tun kawo yanzu suna kotu a tsakanin NNPP da hukumar SDB inda suka gurfanar da hukumar a gaban babban kotu mai lamba ta 7 a bisa shirye-shiryen da gwamnati ke yi na tushe musu ofishin.

Kamar yadda ya shaida, ya bayyana cewar Alkalin kotun ya shiga tsakaninsu da gwamnatin inda ya bukaci a jira hukuncin kotu kan lamarin.

Baba Ma’aji ya ci gaba da shaida wa manema labaru cewa, “Bayan shigar da su kotu da muka yi, kuma mun rubuta takardar korafi zuwa ga kwamishinan ‘yan sanda na jihar a bisa abun da ake shirin yi mana, muna nemi sa da ya yi kokarinsa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a tsakanin jama’an jihar ya yi duk mai iyuwa wajen dakatar da gwamnati daga wannan manufar nata wacce ta saba wa doka,” In ji NNPP

Jam’iyyar ta yi shelan cewar a sakamakon sanuwa da kuma tashen da take yi a jihar Bauchi ne ya sanya gwamnati mai ci ta sanya ido hade da neman musguna mata domin durkufa da ci gabanta a jihar.

Baba Ma’aji ya bayyana cewar jam’iyyar NNPP tana matukar mutunta doka, kuma mafiya yawan ‘ya’yan jam’iyyarsu masu kiyaye doka ne, don haka ya bayyana cewar za su ci gaba da bibiyar hakkinsu a kotu domin ganin adalci ya kasance jagora a garesu.

Da muke hira da shi ta wayar tarho, Kakakin Jam’iyyar NNPP a jihar Bauchi Alkasim Idris ya bayyana cewar wannan lamarin abun mamaki ne, yana mai bayanin cewar gwamnati mai ci ta fara razana da irin dumbin masoya da magoya baya da jam’iyyar ke da shi a jihar, yana mai cewa hakan ba zai rage musu komai ba illa kara musu himma da kokarin kwace mulki daga hanun APC.

Ta bakinsa “Mu da muke kotu da gwamnati amma abun takaici yau sai muka wayi gari gwamnati ta je tana rushe mana ofishi wai ya hau kan hanya, alhalin ofishinmu jimammen waje ne. wannan lamarin karan tsayene wa doka,”

Alkasin ya ci gaba da shaida mana cewar, “Ba wani laifi wajen ya yi ba, illa kawai don ya kasance ofishin jam’iyyar NNPP. Saboda a tarihi wannan wajen ya fi shekara 50 a gine kuma ana ci gaba da amfani da shi, hasalima wajen shine super market na farko da jihar Bauchi ta taba mallaka a tarihi, ka ga wajen ba wai sabon waje ne da wannan zai zama wani abun da za a ce mun shiga doka da kan hanya ba,” In ji Kakakin NNPP

Jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar, ya bayyana cewar ba za su yi wani abu da ya kauce wa doka ba, don haka za su ci gaba da neman hakkinsu a kotu, “Matakinmu ba zai wuce kotu ba, yanzu haka muna kotu kuma za mu ci gaba da bibiyar hakkinmu a kotu ba wai za mu zauna muna gani ana ci mana fuska ba,”

Kakakin Jam’iyyar ya bayyana cewar wannan lamarin ba zai basu tsoro ko firgici ba, don haka ne ya bayyana cewar dukkanin talakawa da masu kishin jihar suna karkashin jam’iyyarsu “Don mun kasance ‘ya’yan NNPP ne kawai gwamnati take amfani da siyasa wajen musguna mana. Adawace kawai ta siyasa, gwamnatoci nawa aka yi babu gwamnatin da ta rushe wajen sai gwamnatin APC don haka muna masu bayanin cewar wannan adawace kawai ta siyasa, kuma jama’a sun gane mene ne ake nufi a nan,” In ji Kakakin NNPP na jihar Bauchi.

Duk kokarin da muka yi don jin ta bakin hukumar tsara birane na jihar Bauchi hakan ya citura domin kuwa a tsakanin ranakun Asabar da Lahadi ne lamarin ya kunnu kai wanda kuma basu aikin gwamnati a wadannan ranakun, amma da zarar muka ji wani kit daga bangarensu za mu shaida muku domin ku ci bangaren ita gwamnatin.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: