Hana Shan ‘Kodin’ Kadai Ba Zai Magani Ba — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

Hana Shan ‘Kodin’ Kadai Ba Zai Magani Ba

Published

on


Kafin gwamnatin tarayya ta shelanta haramta shigowa da hada maganin tarin nan na Kodin kimanin makwanni biyu da suka shige, yanda ake kauce hanya wajen kwankwadar sa ya kai matuka, musamman a tsakankanin matasa. Gargadi kan hadarin da ke tattare da yanda ake kauce hanya wajen shan Kodin din da nufin a gusar da hankali ya taso ne bayan da gidan talabijin na BBC mallakin gwamnatin kasar Ingila, ya shirya wani shiri na musamman kan yanda ake sha da rabawa gami da mummunan hadarin da ke tattare da yanda ake amfani da maganin tarin na Kodin ta muguwar hanya a Nijeriya. Wannan shirin na gidan talabijin din ne ya kara fito da hadarin da ake ta kara fuskanta kan Kodin din a sarari, ta yanda al’umma suka yi ta sharhi a kafofin sadarwa na yanar gizo kan wannan masifar ta shan Kodin din a Nijeriya.

Kodin, magani ne wanda likita kan rubuta wa wanda yake fama da matsalar zafin jiki da mura. Yawanci yakan zo ne a kwayar sa, sannan kuma sai hada shi da ainihin sinadaran da ke maganin tari na ruwa. Tylenol 3, shi ma wani maganin kashe radadin ciwo ne, Kodin ne da ake hada shi da sinadarin acetaminophen. Kwararru sun ce, duk da kasancewar Kodin bai kai karfin ainihin kwayar sa ba, morphine, amma duk da hakan yana tattare da sinadarai masu karfin gaske wadanda kan iya jefa masu kwankwadar sa ta hanyar da ba ta dace ba cikin wani irin mawuyacin hali. Da farko dai a kan fara shan sa ne sannu a hankali tare da yarjewar likita a matsayin maganin tari. Saboda ya fi sauki kan wasu nau’ukan na shi da ake masu ganin hadari ne (kamar su, morphine and Odycontin), wadanda samun su da kuma kauce hanya wajen shan su yake da sauki.

A duk lokacin da aka sha shi ba bisa ka’ida ba, yakan sanya a ji alamun jiri, gajiya, mutuwar jiki da neman hutawa. Yakan kai ga masu shan na shi zuwa wani yanayin da za su ji ba sa iya rayuwa sai da shi. Duk kuma da cewa, mutane da yawa su na shan Kodin din ne ta halastacciyar hanya domin neman magani, amma a mafiya yawan lokuta ana shan sa ne don neman buguwa. Masu shan sa da yawa, su na sha ne don neman samun saukin radadin wani ciwo ko damuwa da ke tattare da su. Amma fa wasu mutanan gani suke ai maganin ba shi da wata illa, daga cikin matsalolin da yakan haddasa akwai ciwon bacci, buguwa, makanta da gazawar zuciya. Matukar aka kwankwade shi da yawa, tabbas Kodin yana iya zama hadarin gaske. Ana iya cutuwa da shi ta hanyar kwankwadar ruwan maganin shi ko kuma kwayar na shi. A shekarar da ta gabata, hukumar hana yin tu’ammuli da muggan kwayoyi (NDLEA), ta yi gargadi kan yawaitan shan haramtattun kwayoyi a kasarnan.

Hukumar ta NDLEA, wacce aka kafa ta a shekarar 1990, masu sukan ta cewa suke yi, ta gaza sauke nauyin da aka dora mata, na kawar wa kwata-kwata da safara da kuma yin tu’ammuli da kowane irin haramtacciyar kwaya ko ruwa ne ko kuma hayaki ko duk dai wani abin da amfani da shi kan iya jirkitar da hankali ko ya kai ga cutarwa, gami da kwato dukiyar da aka tara ta ta wannan haramtacciyar hanyar ta sayar da muggan kwayoyin. Sukan da hukumar ta jima tana musanta wa, inda take yin nu ni da kokarin da take na ganin ta takaita lamarin.

A shekarar 2015 kadai, hukumar ta yi nu ni da cewa, ta kama muggan kwayoyin da kimar su ya kai Naira bilyan 3.7, a tashar tashi da saukar Jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas kadai. Muggan kwayoyin da ta kama sun hada da, kilo gram 172 tabar Wiwi, kilo 160 na ephedrine, kilo 114 na, methamphetamine, kilo 96 na cocaine, kilo 45 na, tramadol da kilo 5k na, heroin.

A cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan muggan kwayoyi, Nijeriya ce kasa ta uku, wacce aka kwace Koken mafi yawa a cikin ta a duk duniyar nan. Inda akalla kashi 50 zuwa kashi 70 na tabar Koken din duk ta Jiragen sama ne ake yin safarar su. Rahoton ya nu na yadda kasar tamu ke kara zama mai hadarin gaske a matsayin ta na cibiyar shiga da fitar da tabobin masu matukar hadarin gaske na Heroyn da Koken zuwa kasashen Turai, gabashin Asiya, da kuma kudancin Amerika.

Ma’aikatan lafiya da na zamantake sun nu na irin kalubalen da ke tattare da kokarin ganin an iya raba al’umma da muggan kwayoyi kwata-kwata. Sai dai kuma, masu ruwa da tsaki kan lamarin su na ganin har yanzun gwamnatoci ba sa taka rawar da ta dace wajen magance matsalar. A nan Arewacin kasarnan misali, an fara Ankara da hatsarin da muggan kwayoyin ke ta jefa al’umma ciki ne bayan da kungiyar matan gwamnoni suka shirya wani taro shekaru biyu da suka shige domin wayar da kai da ba da darussa kan yin tu’ammuli da muggan kwayoyin, wanda yafi kamari a wannan sashen na Arewacin Nijeriya, wanda kuma Matasa da Mata ne suka fi tsunduma a cikin sa.

A ra’ayin wannan Jaridar, har sai an gano musabbabin abin da kan kai mutanan da ke fadawa cikin wannan hadarin an kuma yi maganin shi kafin a iya zargan masu tu’ammuli da muggan kwayoyin kan munanan ayyukan na su, matukar kuwa ba hakan ba, duk wani mataki da za a iya dauka, a karshe yana iya zama aikin banza. Babban matsalar ita ce na yadda gwamnati ba ta dauka tare da aiwatar da matakan da suka dace kan masu sayar da muggan kwayoyin, wadanda kuma su na nan a cikin al’umma duk an san su ba.

A namu fahimtar, ya kamata a kara tsananta yin fadakarwa kan hadarin da ke tattare da yin tu’ammuli da muggan kwayoyin hatta a wurare da cibiyoyin da aka ke~e na farfado da wadanda suka fada cikin wannan muguwar dabi’ar, sannan duk inda ake da irin wadannan cibiyoyin kamata ya yi a kula da su sosai ta yadda za su dace da zamani, a kuma kafa sabbi.

Muna murna da maraba da kafa dokar shigowa, hadawa da sayar da Kodin, amma fa hakan bai isa ya iya magance wannan masifar da take cin mu ba. yanzun ne kuma lokacin da ya kamata mu yi wani abu a kai.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!