Connect with us

WASANNI

Iniesta Da Torres Sun Yi Bankwana Da Kungiyoyin Su

Published

on

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Andres Iniesta, da takwaransa na Atletico Madrid, Fernando Torres sun yi bankwana da kungiyoyinsu cikin yanayi na kewa.

Iniesta ya kammala aikin bugawa  Barcelona wasa da nasarar da ta samu akan Real Sociedad daci 1-0 a wasan karshe na gasar La Liga a ranar Lahadin data gabata.

Iniesta mai shekaru 34 kuma dan asalin kasar Sipaniya zai raba gari da Barcelona baki daya nan da karshen kakar da muke ciki bayan ya lashe ma ta manyan kofuna har 22 cikin shekaru 16 da ya dauka yana buga wasa a kungiyar.

Ko da dai kofin da suka daga na La Liga a bana, shi ne na 32 da Iniesta ya lashe a Barcelona gabanin wasan da suka doke Real Sociedad a jiya, magoya bayan Barcelona sun yi bikin bankwana da dan wasan.

Dan wasan ya yi ta rungume abokan wasansa na Bareclona, tare da zubar da hawaye saboda rabuwa da Camp Nou.

Shi ma dai Fernando Torres ya jefa kwallaye biyu a wasansa na karshe da ya buga wa Atletico Madrid duk da cewa sun tashi ne 2-2 da Eibar a gasar La Liga a ranar Lahadin.

Gabanin wasan na Lahadi, Torres mai shekaru 34 wanda kuma ya buga kwallo a Liverpool da Chelsea, ya samu kyakkyawan tsaron ban-girma.

A ranar Larabar da ta gabata ne Torres ya lashe kofinsa na farko a Atletico Madrid a gasar Europa League bayan sun doke Marseille.

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: