Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Kotu Ta Tsare Dan Shekara 24 Saboda Ya Dabawa Abokinshi Wuka

Published

on

Kotum majistare wadda tayi zamanta a Ile- Ife ranar Jumma’a ta tsare wani mutum maisuna Olaleye Suyi , mai shekaru 21 da haihuwa saboda ya dabawa abokinsa  Oladele Kayode wuka, afuskar shi lokacin da yake barci.

Wanda ke gabarta da masu laifi Insifekta Sunday Osanyintuyi ya bayyanawa kotu cewar, wanda ake zargin ya aikata laifin ne ranar 15 ga watan Mayu, da misalin karfe 11 da 30 a layi na 3 a titin Aladanla Ile- Ife.

Osanyintuyi ya kara bayyana cewar wanda ake zargi da aikata laifin Kayode ya Sassari abokin nashi da wuka, wurare da yawa, saboda rashin jituwa tsakaninsu.

Donhaka laifin daya aikata ya sabawa dokar sashe na 355 na dokar masu aikata laifi ta jihar Osun, shekara ta 2002.

Wanda ake zargi daikata laifin yaki yarda da laifin da ake cewar ya aikata na ji ma abokin shi rauni.

Mai kare wanda ya aikata laifin Mr Olalekan Babatunde ya yi kira da kotun cewar, ta ba, wanda yake karewar bali saboda jinkan shi.

Ya ce, wanda yake karewar ba zai gudu ba, bayannan kuma zai kawo wadanda zasu yi ma shi beli mutanen kirki.

Majistare Olalekan Ijiyode duk da hakan sai  ya bukaci lauyan dake kare wanda ake zargi da aikata laifin, ya rubuto takarda ta neman beli.

Ijiyode har ila yau ya bada umarnin aci gaba da tsare wanda ake zargi da aikata laifin, a kurkukun Ile –Ife, har sai an saurari maganar neman belin na shi.

An dage sauraren karar har zuwa 13 ga watan Yuli kamar yadda kamfanin dillanci labarai na Nijeriya ya bayyana.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: