Matsalar Aure A Garinmu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MUKALA

Matsalar Aure A Garinmu

Published

on


A garinmu ba a san mene ne so ba. Ba a san mece ce soyayya ba. Idan mace na son mijinta har ta kai tana yi masa biyayya sosai, sai a ce ya mallake ta. Idan miji yana yi wa matarsa hidima fiye da yadda aka saba, sai a ce ta sanya shi a minjaye. Aure a garinmu bai doru akan soyayya ba, kuma soyayya bayan aure sai dai ka ji a labarai ko litattafan almara. Aurenmu akan wasu abubuwa ake dora shi marasa karko. Kullum sai ka ji aure ya mutu ko ya gurgunce saboda da ma ba shi da tushe mai kyau.

Mafi yawan abokaina sun fi damuwa da kyakkyawa. Mafi yawan makotana suna tursasa mata aure ko ba su shirya ba, saboda ana ganin sun girma. Gudun abin kunya ne yake janyo wani abin kunyar a inda nake. Da yawan iyaye ba su damu da ’yarsu ta auri mai tarbiyya ba. Sun fi damuwa akan ta aure mai hawa BMW, Lamborghini ko Prado. Ba a fiye damuwa da bincike ba, an fi damuwa da a yi auren kawai.

Malaman addininmu da can muke fakewa agun su idan matsala ta samu, su ma ba su doramu akan falsafar aure kyakkyawa ba. Na karanta litattafan Fikihun aure, daga Risala ta Ibn Abi Zaid har zuwa Almuhalla na Ibn Hazam, duka sai na ga suna dora aure akan cewa hanyar halatta jima’i ne. Ba ina cewa ba hakan a ciki bane, ina ganin muhimmanta hakan shi ne kuskuren. Sun yi ijtihadinsu, mu ma yanzu ya kamata malamanmu su sake sabon ta’arifin aure bisa ginshikan da Alkur’ani ya dora su. Ginshikan Rahama da tausayi da suke sanya nutsuwa a tsakanin ma’aurata ba na halatta jima’i ba.

Na dade ina tunanin, me ya sa Allah ya sanya aure akan ginshikan “kauna” (mawadda) da “tausayi” (rahama) maimakon kyau da jima’i tare da cewa mafi yawan mutane akan haka suke aure? Mafi yawan mutane, duk da za su gayamaka cewa dabi’u sun fi kyau, amma a zahiri sun fi damuwa da kyakkyawa fiye da mai kyawawan dabi’u. Na kuma tabbatar da har bayan wannan rubutu sai wani ya ji banbarakwai saboda na ce ba akan jima’i ya kamata a dora falsafar aure ba.

Wani bai ma taba gane Allah ne ya ce a yi aure akan rahama da tausayi ba. Wani kuma zai ce na raina malamai tunda na ce sun yi kuskure a wani gurin. Ana gayamana babu ma’asumi sai Manzon Allah amma kuma an rabawa wasu malaman wannan matsayi a zahiri. Ba raina malamai bane idan ka ce sun yi kuskure, musamman idan akan abinda Allah ya yi bayaninsa idon su bai kai gun ba. Abubuwa nawa ne na baya suka barwa na gaba?

Daga baya, bayan abinda na sani na “Anthropology” da “ebolution”, na gane cewa yana da wuya mutane su iya watsar da abinda suka gada tun asalin kakaninmu daga “Homo Erectus”, “Homo Habilis” har zuwa “Homo Sapiens”. Har yanzu halayyarmu tana dogara da zaman da kakaninmu (primitibe men) suka yi acikin daji tare da dabbobi. A kowane mataki muna aikata wani abu da yake katangemu daga zuwa matakin da Gotama Buddha ya kira “Nirbana”, Aristotle ya kira “ideal man”, Nietschez ya kira “Superman”, Rumi ya kira “Insanil Kamil” ko kuma abinda ake kira da cikakken mutum.

Addini yana so ya rabamu da halayyar dabbobi, mu kuma rayuwa tun tale-tale ta saba mana da halayyar dabbobi saboda zama da kakaninmu suka yi dasu. Canjin halitta ya ratsamu ta hanyar “genetic mutation”. Aure saboda jima’i ko kyau alamace ta dabbobi. Idan dawisu yana so macen dawisu ta kulashi don su yi “mating” (auren dabbobi) sai ya baza wannan gashin ta gan shi da kyau don ta zabe shi. Haka zakara sai ya yi cara mai karfi, biri sai ya yi fada da yan uwansa, da sauransu dayawa da suke nuna “surbibal of the fittest” a bangaren aure. Wannan ta sa babu wani cikakken aure na zama din-din-din a cikin dabbobi kamar yadda ake bukatarsa a mutane. Turawa sun dade da gane haka sai suka raba auren mutum suka kira shi “marriage” kuma suka kira na dabbobi “mating”.

Wanda ya yi aure don sha’awa ko don kyau, yana nuna halayyar dabbobi ne. Idan ya dade da matarsa sha’awar za ta ragu kuma zai dena ganin kyan. Ka lura ko da mace (kanwa ko yaya) a gidanku duk kyanta sai dai wani ya fada amma kai ba ka ganinsa saboda kullum sai ka ganta. To haka wanda ya yi auren sha’awa shi ma tasa zata kare. Ko dai ya tafi nemo karo wata don ya dena ganin kyan ta gida ko kuma ya saki wacce yake da ita tunda ya dena ganin abinda ya aurota saboda shi.

Wadanda suka yi auren hakuri kuma suna mataki na biyu ne. Tare da cewa hakuri yana da muhimmanci a aure amma bahaushe ya yi kuskure da yake dora falsafar aurensa akan hakuri. Wannan kuskure ne da ake babba. Duk ango sai a ce masa zaman hakuri ne, duk mata sai a ce zaman hakuri ne! Idan fa aka ce zaman hakuri ake to dama fa cutar daya ake kawai! Idan kuwa ana ta cutarka tun kana hakuri to fa watarana sai hakurin ya kare. Ana nan za ku ji kun gaji da hakurin nan, kawai kowa ya yi nasa gaba duk a huta.

Auren yan zamani masu ji da boko shi ma akwai kuskure a ciki. Aure ne da matar ta yi digiri biyu shi kuma mijin ya yi uku. Tana aiki a Abuja shi kuma yana aiki a Lagos. Ba ruwan kowa da sha’anin kowa tunda yana ganin bai kamata daya ya shiga rayuwar daya ba. Ya yi dare a meeting da turawa a “Hilton” ita kuma ta tafi Sheraton “seminar”.

Ana haka watarana duka za su ji ba fa wani amfani zamansu yake da shi ba. Idan suna da ‘ya’ya sai su zauna don yayansu amma idan ba su da yaya sai kowa ya dinga harkar gabansa. Ba abinda yake tsakaninsu sai jima’i sau daya a wata saboda kowa bai da lokacin kowa. Daga nan, idan Allah ba kiyayewa ya yi ba, sai kowa ya zama dan barikin da zai zama sababin barewar auren.

Aure na gaskiya mai karko shi ne wanda akai don “soyayya” mai hade da “tausayi”. Ka aureta don duka kuna son juna da abinda kowa yake yi sannan da tausayin zamantakewar da kuke yi. Ya zamana duk abinda take sai ka ji kana so kuma duk abinda ba ta yi ba za ka auna da tausayin da kakemata. Idan ka dawo gida ka tarar ba ta yi girki ba kuma ga shi kana jin yunwa, maimakon masifa sai ka ji kana tausayinta, ka dauketa ku tafi KFC. Duk abinda ta yi kana kallonsa ta fuskar tausayi da soyayya. Ita ma tana kallonka ta haka. Za ta baka uzuri 100 idan ka yi mata laifi har sai an yi zaton mallaketa ka yi.

Irin wannan auren Manzon Allah (saw) ya yi da Nana Khadija (ra). Shi da yake cikakken mutum ne (Insanil Kamil). Ya auri Nana Khadija ba don kyau ba don ta girmeshi ma. Sun zauna cikin zaman lafiya, tausayi da soyayya har sai da ya zama ba ma ita ba, har kawayenta yana farin cikin gani da son jin muryarsu saboda ita har bayan mutuwarta! Ta tausayamasa sosai bayan soyayyar da take tsakaninsu har ya kira shekarar mutuwarta da shekarar bakin ciki. Saboda jin dadin zama ko tunanin yi mata kishiya bai yi ba har sai bayan mutuwarta ya sake wani auren amma bai manta ta ba. Wannan ita ce soyayya da tausayin da Allah yake bayani akai.

Allah ne mafi sani!

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!