Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Mutum Biyar Sun Yi Ma ’Yanmata Fyade A Jihar Ondo

Published

on

Rundunar ‘yansandan jihar Omdo ta kama mutane saboda zarginsu da ake yi da yi ma, wasu ‘yanmata biyu fade a Odoside a  babban birnin Ondo na jihar Ondo.

Mai magana da yawun rudunar ‘yansandan na jihar ya tabbatar da aukuwar shi al’amarin ranar Lahadi, ya kuma bayyana cewar su wadanda ake zargi da aikata laifin sun jima su ‘yan mata rauni da kuma yi masu fade, bayan nan kuma sai suka daukio hoto na bidiyo na yadda suka yi lalartar, suka aika ta hanyar sakonsu na Facebook ta yanar gizo.

Wadanda ake zargi da aikata laifi sun hada da Bode Akinsuku, Olabenji Femi, Abiodun Ayodele, Fadairo Wahab, da kuma Adebayo Adedayo.

Su daiwadanda ake zargin sun aika da sakon hoton bidiyon da suka dauka, na yadda suka yi lalata dasu ‘yanmatan, suka kuma sa a shafukansu na Facebook, an kuma kamasu ne , bayan da ka shigar da korafin abinda suka aikata a ofishin ‘yansanda.

Dasuke bayyana wahalar da suka sha ‘yanmatan biyu sun ce tun farko su hudu ne, an kuma gaiyace su ne zuwa, wani gidan daya daga cikin wadanda ake zargin, wanda yayi karyar, yana bikin tuna ranar haihuwar  ‘yar shi. Amma sai biyu daga cikinsu suka gudu.

Daya daga cikin wadda abin ya rutsa da ita ta bayyana cewar ‘’Sun yi mana tsindir suka kuma kwace man kayanmu, sun kuma dauki hotonmu na bidiyo, bayan ko wannensu yayi lalata damu, daya bayan daya, sun ma yi barazanar kai mu waje tsirara, mun yi kuka, muka kuma rokesu su kyale mu mu tafi bayan sun yi mana fade’’.

‘’Sun yaudaremu ne muke je gidan wajen karfe sha daya da rabi na rana, sun tsare mu na awonni masu yawa, daga baya kuma sai suka debo mana ruwa muka yi wanka, sun sawo mana shinkafa, daga nan kuma suka barmu muka tafi gida. Mun fadawa daya daga cikin ‘yanuwanmu, wanda ya sha alwashin sai ya samu bidiyon, ya kuma sanarwa ‘yansanda.

‘’Koda yake dai daga cikin ‘yanuwan wadanda suka aikata laifin sun rokemu da cewar zasu bamu kudi, amma sai danuwana ya samu bidiyon, daganan kuma ya sanar da ‘yansanda.’’

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ;’yansandan ya bayyana cewar sai sun faya aya zaki, za kuma a kai su kotu, saboda laifin da suka aikata wanda suka abin bai dace ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: