Connect with us

LABARAI

Zamfara: Bangaren Sanata Marafa Ya Ayyana Shugaban Jam’iyya

Published

on

Sakamakon rahotannin da aka samu kan yadda aka gudanar da taron Jam’iyyar APC a sassa biyu a karshen makon nan, inda magoya bayan Dan Majalisar Dattijai mai wakiltar Zamfara ta tsakiya, Sanata Kabiru Marafa, magoya bayan Sanatan sun shelanta cewa, Alhaji Surajo Garba ne halastaccen shugaban Jam’iyyar ta APC a Jihar ta Zamfara da suka sani.

Cikin bayanin da magoya bayan sanatan suka fitar ga manema labarai a Abuja, ta bakin shugaban taron na su, Alhaji Abdulkadir Gusau, sun ce, Surajon ne ya sami nasarar zama shugaban Jam’iyyar ta APC a Jihar ta Zamfara, sakamakon taron da Jam’iyyar ta yi ranar Asabar din da ta gabata.

Ya kuma ce, Alhaji Rabi’u Emir, Bello Soja, Nafisa Ahmed da Shehu Ibrahim, su ne suka sami nasarar zama, Shugaban matasa, Jami’in yada labarai, Shugabar mata, da kuma Sakataren Jam’iyyar a Jihar bi-da-bi.

Ya kara da cewa, an kuma zabi mutane 26 bisa mukamai daban-daban na Jam’iyyar a wajen taron na su.

Gusau, ya bukaci sabbin Shugabannin Jam’iyyar da su yi aiki tare da kowa, su kuma yi duk abin da zai kawo hadin kan ‘ya’yan Jam’iyyar domin tunkarar babban zaben kasa na 2019.

A cewar Gusau din, “Shugaban sashen na su, Sanata Kabiru Marafa, ya bukaci sauran magoya bayan Gwamnan Jihar, Abdul’aziz Yari , da su baiwa sabbin shugabannin hadin kai, domin ciyar da Jihar ta Zamfara gaba.

“Marafa, wanda shi ne shugaban kwamitin Majalisar ta Dattawa kan sha’anin Man Fetur, ya shawarci Gwamnan da cewa ya sani, yin amfani da kariyar da tsarin mulki ya ba shi a matsayin sa na Gwamna a halin yanzun tare da karya doka ba zai kai shi ko’ina ba.

“Ya kuma bukaci sabbin shugabannin da su hada kansu, su kuma gyara fasalin Jam’iyyar domin tunkarar babban zaben kasa da yake tafe.

“Ba da jimawa ba za a fitar da jadawalin sunayen sabbin shugabannin domin a rantsar da su,” in ji Gusau.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: