Mahaifin Fasihin Marubuci Lawan Prp Ya Kwanta Dama — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

ADABI

Mahaifin Fasihin Marubuci Lawan Prp Ya Kwanta Dama

Published

on


A safiyar ranar Asabar ne 19-5-2018 mahaifin marubucin ya yi bankwana da wannan duniyar zuwa gidan gaskiya. Malam Muhammad Sani Prp, shi ne mahaifin fasihin marubuci Lawan Muhammad Prp. Ya rasu bayan gajeriyar jinya sakamakon ciwon hanta da yake fama da shi. Ya kwanta a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano tsawon makonni Uku kana ya koma gida don ci gaba da shan magani daga nan Allah ya dauki ransa.

Marigayin ya rasu yana da shekaru Saba’in (70) a duniya, ya rasu ya bar mace Daya, ‘ya’ya Bakwai da kuma jikoki Ashirin. Daga cikin ‘ya’yan nasa akwai Lawan Muhammad Prp wanda shi ne sakataren kungiyar marubutan Hausa ta ‘Hausa Authors Forum’, kuma dai shi ne zakaran da ya lashe gasar zauren marubuta ta 2018, da kuma Abdurrahman Muhammad, Ahmad Muhammad ma’aikata a rundunar ‘yan sanda ta kasa.

Duka a yammacin ranar Asabar din ta 19 ga Mayu, 2018, Allah ya dauki ran mahaifiyar marubucin nan Malam Aminu Salisu Giginyu, ta rasu bayan ta yi fama da rashin lafiya, wanda ya tsananta makonni Biyu kafin rasuwar tata, inda likitoci ke ta faman aikin gwaje-gwaje a kanta, amma ba su kai da gano abun dake damunta ba har Allah ya dauki ranta.

Ta rasu tana da shekaru Sittin (60) a duniya, ta bar ‘ya’ya Bakwai da kuma jikoki Goma Sha Biyar. Daga cikin ‘ya’yan nata akwai marubuci Malam Aminu Salisu Giginyu, memba na kungiyar marubuta ta kasa reshen jahar Kano (ANA KANO), ya taba rike matsayin jami’in yada labarai na kungiyar, kuma shi ne ya fara gabatar da filin ‘Duniyar Marubuta’ wanda gidan Radio Kano FM ke gabatarwa.

Fatan Allah ya ji kan su da gafara, ya ba iyalansu juriya da hakurin rashinsu, in tamu ta zo ya sa mu cika da imani Ameen.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!