Connect with us

WASANNI

Ramos Ya Yi Wa Salah Fatan Samun Sauki

Published

on

Mai koyar da yan wasan  Liberpool Jurgen Klopp ya ce raunin da Salah ya ji a gasar Zakarun Turai ya yi muni sosai, a yayin ake fargabar dan wasan ba zai buga gasar cin kofin duniya ba.

Ko da yake hukumar kwallon kafar Masar na da tabbacin cewa dan wasan zai murmure kafin soma gasar cin kofin duniya da za a fara a 14 ga Yuni.

Salah ya fice fili yana kuka bayan Sergio Ramos yayi masa keta a wasan karshe da Real Madrid ta doke Liberpool 3-1 a babban birnin kasar Ukraine wato Kieb.

Klopp yace”Raunin ya yi muni sosai kuma tuni Salah yana kwance a asibiti za a yi hoton kafadarsa saboda raunin ya yi muni.”

Amma a sakon data wallafa a shafinta na twitter, hukumar kwallon Masar ta ce an yi wa Salah hoto, kuma ya nuna ya samu targae ne a kafadarsa, tare da bayyana cewa tana da tabbacin zai murmure kafin gasar cin kofin duniya.

Salah wanda ya ci wa Liberpool kwallaye 44 a bana, ya yi kokarin ya ci gaba da wasa bayan ketar da Ramos ya yi masa ana minti 26 da fara wasa amma dole daga bisani ya fice fili, inda Adam Lallana ya karbe shi.

Daga baya Ramos ya wallafa sakon fatan alheri ga Salah tare da masa fatan samun sauki, inda ya ce kwallo ta gaji haka.

Salah wanda ya fi yawan cin kwallaye a firimiya ya samu farin jini a kakar bana kuma magoya bayan dan wasan musamman a kasarsa Masar hankalinsu ya tashi, inda suke fatar dan wasan zai murmure da wuri domin jagorantar tawagar kasar a Rasha.

Masar za ta tafi gasar cin kofin duniya a karon farko bayan shekaru 28, kuma ‘yan kasar na ganin Salah zai jagoranci kasar ga nasara.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!