An Bukaci A Yawaita Yi Wa Kasa Addu’a A Cikin Wannan Watan Na Ramadan — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Bukaci A Yawaita Yi Wa Kasa Addu’a A Cikin Wannan Watan Na Ramadan

Published

on


A halin da kasar nan take ciki babu abin da take bukata ga al’ummar musulmai baki daya shi ne su kara jajircewa a wannan wata da muke ciki mai tsarki na watan azumin Ramadan  wajen yi mata addu’oin samun zaman lafiya da karuwar arziki, domin sai da zaman lafiya kasa da al’umma ke samun ci gaba.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Alhaji Maharazu Ibrahim Adamu, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin shi dake birnin Kano.

Maharazu Ibrahim wanda har ila yau shi ne manajan daraktan kamfannin sufurin motoci na Gizna, ya ce, babu shakka matukar musulmin kasar nan suka yi amfani da watan mai albarka kan samun zaman lafiya da yardarm Allah za a samu nasara domin alfarmar watan.

Musamman rashin tsaro da ake fama da shi a wasu sasssan kasar nan, sannan kuma mu tuba zuwa ga Allah tunda wata ne da yake zuwa sau daya ashekara. A matsayin shi na dan kasuwa ya jawo hankulan ‘yan kasuwa, musammam ga wanda suke sayar da kayayyakin da aka fi bukatarsu a watan na Ramadan wajen yin rangwame da tausayawa ta yadda mai karamin karfi zai iya mallaka.

Maharazu ya koka ga wasu ‘yankasuwan da sai a watan na Ramadan suke karin farashin kayyaki maimakon yin rangwame albarkacin watan na Ramadan. Sannan kuma abubbuwan alhairi da aka siffatu da shi a lokacin Ramadan yana da kyau a cigaba da aikatawa ko da bayan watan na Ramadan ta wuce, kamar karatun alkur’ani tallafawa marasa karfi da kuma marayu, domin duk wanda ya rangwanta Allah zai rangwanta ma shi ranar gobe kiyoma.Sai ya yi addu’ar allah ya ba bu dacewa.

Ya yi amfani da wannan dama da kira ga gwamnatin kasar nan da taimaka masu sufurin motoci wajen gyara hanyoyin da suka lalace, wanda hakan ke kawo asaran rayuka da dukiyoyin al’umma .Duk da cewa harkokin sufuri na bayar da gudunmawa ga cigaban tattalin arzikin kasarnan tare da samar da aikin yi ga a’umma musamman matasa har ila yau da kuma

samar da haraji ga gwamnati.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!