Gudanar Da Zabe Da Na’urar Kwamfuta: Darussa Daga Kadunac — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

Gudanar Da Zabe Da Na’urar Kwamfuta: Darussa Daga Kadunac

Published

on


Jihar Kaduna ta bude sabon shafi a fannin gudanar da zabe a tarihin kasarnan, inda ta kasance Jiha ta farko da ta gudanar da zabe ta hanyar yin amfani da na’urar Kwamfuta cikin nasara. Gudanar da zabukan kananan hukumomi ga gwamnatocin Jihohi ba karamin aiki ne mai wahala ga Jihohi da yawa ba, inda har abin yakan kai wasu Jihohin ga hakura da gudanar da zaben, su koma ga kafa Shugabanni na riko a kananan hukumomin na su na tsawon shekaru.

A lokacin da masu jefa kuri’a suka fito domin su zabi Kansiloli da Shugabannin kananan hukumomin da suke so a Jihar ta Kaduna, ranar 12 ga watan Mayu 2018, kadan ne suke da tunanin yanda zaben zai kasance. Da yawa sun yi tunanin lamarin zai kasance kamar yadda aka saba ne a baya can, inda kowa ya san sakamakon zaben.

Domin kuwa, shekaru da yawa, kowa ya san mawuyaci ne a gudanar da zabe ba tare da magudi daban-daban ba. don haka, al’adar ita ce, Jam’iyyan da ke mulki a Jiha, ita ke lashe dukkanin zaben, ta bar ‘yan adawa da cizon yatsa. Amma ba hakan ta kasance a zaben na ranar Asabar waccan ba a Jihar ta Kaduna. Wanda hakan ya bayar da alamun sa rai ga Jam’iyyun adawa, su ga cewa lallai, ashe za su iya tsayawa zaben kananan hukumomi wanda kuma Jam’iyyar mahukuntan Jihar ta shirya, su kuma yi nasara.

Gwamnatin Jihar, ta yi farin ciki da irin nasarar da yadda aka gudanar zaben ya samu. Inda ta yaba wa masu kada kuri’a a Jihar da ma dukkanin wadanda su ka sanya zaben ya samu nasara, watau gwamnatin Jihar, Masu jefa kuri’a da kuma hukumar da ta tsara gami da gudanar da zaben lami lafiya cikin nasara.

Masu sa ido kan yadda aka gudanar zaben daga waje, sun yaba da yadda aka gudanar da zaben in an kwatanta shi da zabukan da aka rika gudanarwa a baya, suka ce, tabbas wannan zaben ya gudana ne cikin tsari da kwanciyar hankali, sabanin yadda ake gudanar da mafiya yawan zabukan kananan hukumomi, inda za ka taras, duk Jam’iyyar da ke mulki ita take wawashe komai, amma zaben Kaduna, ya nu na wa sauran Jihohi hanya na gudanar da zabe a bisa turba ta gaskiya, ta yadda hatta Jam’iyyun adawa ma za su iya cin zaben.

Mun lura, baya ga samun karin masu jefa kuri’a ma da hakan ya samar, gudanar da zabe ta hanyar Kwamfuta, ya fi arha, yana kuma kara wa masu jefa kuri’ar karfin gwiwa, yana kuma kara tabbatar da cewa, ana yin Dimokuradiyya ne. Daya daga cikin amfanin yin zabe ta hanyar Kwamfutan shi ne, tabbatar da rashin tababa da kuma hanzari. A namu ra’ayin, zaben da ya gudana a Jihar Kaduna, ya kamata ya zama linzamin sauya yanda muke gudanar da zabukanmu a baya. Yana da mahimmanci, gwamnatin tarayya ta jarraba yiwuwar yin amfani da wannan hanyar wajen gudanar da zaben Jihar Ekiti da ke tafe, da nufin fadada abin har ya zuwa babban zabe na kasa bakidaya da ke tafe a shekarar 2019.

A nan, muna bayar da shawara ga Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, da ta yi koyi da samfurin yadda aka gudanar da zabe a Jihar Kaduna, wajen shirya zabe na kasa bakidaya. Yana kuma da kyau hukumar da ta dukufa wajen wayar wa da al’umma kai kan mahimmancin gudanar da zabe ta wannan hanyar da kuma amfanin sa.

Ta hanyar gudanar da zabe da Kwamfuta, ba za ka sami lalatattun kuri’a ba, nan take kuma Kwamfuta za ta kidanya sakamako, wanda hakan ya kore a yi ta nanata kirga kuri’u, wannan hanyar kuma za ta baiwa jami’an zabe daman iya bayyana sakamakon zaben nan take. Hanya ce mafi sauri da inganci wajen bayar da sakamako.

Kamar dai kowace irin sabuwar hanya da tsari da aka fara kawowa, gudanar da zaben ta hanyar Kwamfuta yana iya sa wasu su ji zafi. Ya kamata gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen wayar wa da al’umma kai kan mahimmancin wannan sabuwar hanyar. Kamar dai yadda masu iya Magana ke cewa, ci gaba shi ne babban jari a duniya. A nan, ci gaban da muke gani shi ne na yadda za a iya gudanar da zabe ta sahihiyar hanyar da ba coge, sannan kuma a rana guda ba tare da wani jeka ka dawo ba.

Ginawa da tafiyar da tsarin zabe a kasa, abu ne da yake da bukatar yin tsari da samar da kwarewa da kuma fahimta yanda ya dace. A lokuta da yawa, kasashen kan nemi karin ilimin abin daga wasu kasashen da suke da ilimi da kwarewa kan lamarin, suka kuma saba har ma gudanar da tsarin ya zaman masu jiki. Yana da kyau hukmar zabe mai zaman kanta ta kasa, ta nemi shawarwari da hadin kan kwararru domin samun horon da ya dace na yin aiki da wannan na’urar yanda ya dace.

Kamar yanda muka fada tun da farko, mun yaba wa hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kaduna, wacce ita ce ta farko wajen fito da wannan sabon tsarin, wanda ya baiwa dukkanin Jam’iyyu da ma ita gwamnatin kanta damar neman kuri’u daga wajen al’umma a bisa turban gaskiya da adalci.

Mun kuma yaba ma su kansu mutanan da suka yi zaben, a bisa yanda suka kasance a yanayin da ya nu na fahimta da wayewa a lokacin gunar da zaben. Muna ganin wannan a matsayin wani alami mai kyau na dorewar mulkin Dimokuradiyya a wannan kasar tamu.

 

Advertisement
Click to comment

labarai