Gwamnatin Bauchi Ta Kafa Cibiyoyin Kare Yaduwar Cutar Sida   — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Bauchi Ta Kafa Cibiyoyin Kare Yaduwar Cutar Sida  

Published

on


Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa cibiyoyin kare yaduwar cutar sida (HIB) daga Uwa zuwa ‘Ya’Ya a cikin gundumomi dari uku da ashirin da uku (323) a daukacin fadin jihar ta Bauchi. Cutar sida wacce take karya garkuwar jikin bin-adama.

Shugaban hukumar yaki da cutar sida, tarin fuka, kuturta da cutar zazzabin cizon sauro (BACATMA) na jihar Bauchi, Dakta Mansur Dada shi ya bayyana haka a kwanakin baya a garin Bauchi yayin da ya karbi mambobin kwamitin tafiyar da al’amuran ilimantarwa na kungiyar masu rajin tabbatar da gaskiya da adalci kan sha’anin rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da sabbin jarirai, a garin Bauchi.

Dakta Dada ya ce kafa cibiyoyin kare cutar sida daga uwa zuwa jariri a cikin gundumonin jihar, zai taimaka wajen tabbatar da cewar dukkan mata masu juna biyu da aka tabbatar suna dauke da cutar sida sun samu cikakkiyar kulawa ta fuskar lafiya, yana mai cewar, “Wannan mataki ne na karesu daga yada cutar akan ‘ya’ya da suka Haifa,”

Ya kuma bayyana cewar, “tun kafin wannan gwamnati ta hau kan mulki a shekara ta 2015 muna da cibiyoyin kula da kare cutar sida daga uwa zuwa jariri guda dari da ashirin (120) ne kacal,” yana mai jaddada cewar, cibiyoyi 120 ne kawai suke iya cimma mata masu juna biyu da suke dauke da cutar sida a jihar.

“Don haka muna ga ya dace mu fadada su zuwa cibiyoyi dari uku da ashirin da uku (323), wanda hakan yana nufin cewar a yanzu haka muna da cibiya daya a cikin kowace gunduma a fadin jihar nan”, kamar yadda ya fada.

Dada ya kara da cewa, “Gwamnatin jiha ta himmatu domin shawo kan cututtuka biyar kamar cutar zazzabin cizon sauro, kuturta, tarin fuka, da cuta mai karya garkuwar jiki ta yadda za a samu al’umma mai cike da koshin lafiya”.

Dada ya ce hukumar ta horar da ma’aikatan kiwon lafiya guda dari bakwai (700) akan aikin kare cutar sida daga uwa zuwa jariri, yana mai karawa da cewar, “a yanzu haka muna da ma’aikatan kiwon lafiya guda biyu a cikin kowace cibiya,” A cewar shi.

“Muna samar masu da magungunan kariyar cutar da sauran kayayyaki domin tabbatar da cewar suna rayuwa mai cike da koshin lafiya. A bisa wannan tsoma hannu, muna da tabbacin ganin cewar zamu ga sauyi a lokacin daukar ciki da kuma haihuwa a tsakanin mata masu juna biyu kuma suke dauke da cutar sida”, a cewarsa.

Tun da farko, shugaban hukumar, BASSAM, Isa Ladan ya yi kira ga hukumar BACATMA da ta samar da alkaluma akan yawan mata masu dauke da cutar sida (HIB) a jihar tab AUCHI, “Domin tabbatar da mata masu dauke da cutar sida da suke karban maganin kare jariri daga harbuwa da cutar”.

Ya jaddada bukatar a rabawa uwaye da jarirai gidan sauro mai magani domin karesu daga cizon sauro.

Shugaban BASAM ya kuma yi kira ga hukumar ta tabbatar da raguwar kara-kainar sauro a cikin gidaje da daukacin jihar baki daya, musammam ma dai ga uwaye da jarirai domin samun raguwar mace-macensu.

Ya kuma yi kira ga hukumar gudanarwa da ta tabbatar da cewar,  an yi cikakken aikin raba gidan sauro mai magani wa iyaye mata da jariransu.

Shugaban hukumar BASSAM ya kuma yi kira ga hukumar da ta tabbatar da cewar, an samu raguwar cutar zazzabin cizon sauro a mataki na matsakaici, musamman ma a tsakanin mata da sabbin jarirai domin rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da sabbin jarirai.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!