Ya Kamata Gwamnati Ta Ba Harkar Fim Tallafi Na Musamman -Abubakar Waziri — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Ya Kamata Gwamnati Ta Ba Harkar Fim Tallafi Na Musamman -Abubakar Waziri

Published

on


Wakilinmu BELLO HAMZA ya tattauna da daya daga cikin jaruman ‘yan fim din Kannywood da aka karrama a taron Arewa Mobie Award da aka gudanar a garin Katsina kwanakin baya, mai suna ABUBAKAR GARBA MUHAMMAD, an karrama shi ne da lambar “Best Actor in Supporting Role”, saboda rawar daya taka a fim din “Dan Baiwa”, ga dai yadda tattaunawar tamu ya kasance.

 

Za mu so ka gabatar mana da kanka?

Suna na Garba Muhammad, amma kasancewar sunana Garba sai ake kira na da Abubakar, to da Abubakar din ma duniya ta fi sani na, shi ya sa ake yi min lakabi da Abubakar Waziri. Shi Wazirin kuma nick name ne, lokacin muna yara akwai abokai da muka rika yi irinsu Sani Malasko, su Asko da sauran su, to ni ban yi irin wannan nick name din ba sai na lika wa kai na Waziri saboda akwai wani dan sarkin Hayin Dogo wanda a halin yanzu shi ne Sarki don ya gaji mahaifinsa,  kuma ina ce mashi Sarki saboda shi dan Sarki ne, to da yake aboki na ne kullum muna tare sai ina kiran kaina Waziri. To dalilin da na samu Abubakar Waziri kenan.

 

Zamu so ka gaya mana takaitaccen tarihinka, yadda ka sami kanka a harkar wasanni.

To, ni kusan ma da harkar wasannin na taso, saboda kusan tun muna yara yayyinmu ke yi muna zuwa muna kallon su har na yi picking interest in muka je kallon su sukan ko aiken ka aka yi kai zo a aike ka nan gidan irin wasan nan na dabe to kuma dai har na taso, daga nan kuma nayi sa a jami’ar ABU ta dauke mu aikin rawar Koroso a “Center for Nigerian Cultural Studies” sannu a hankali kuma sai cibiyar “Abuja Council for Arts and Culture” ta kuma dauka ta. To ina nan tare da Abuja kuma ina wasan kwaikwayo kwatsam sai na fara fim tunda dai daman harka tace, wannan shi ne kadan daga ciki.

 

Wadanne shahararrun fim ka fito a ciki zuwa yanzu?

Na yi fina- finai da dama, akwai irinsu Kisan Gilla, wani fin ne na Sadik Sani Sadik, akwai Dinyar Makaho da irinsu ‘Ya daga Allah, suna da yawa dai, irin su Hajiya Babba na fito a ciki, akwai wani fim mai suna “Suma mata ne”, na fito s fim da yawan gaske.

 

To an gabatar da wani makon kyaututtuka na karramawa ‘yan wasa, ya aka yi ka samu kanka daya daga cikin wadanda aka karrama?

Na’am, akwai fim da kamfanin Hamisu Iyantama, “Iyantama Multi–Media” suka gayyace ni wani fim dinsu mai suna Dan baiwa inda na je na yi wani “Role” a matsayin dan sanda ‘Detectibe’ to a wannan role din dana fito, da shi na samu wannan karramawa da wannan fim mai suna Dan baiwa wanda Hafizu Bello shi ya shirya, to bani da ma masaniya, sai Hamisu ni, yake cewa sun shigar da fim din su a takarar zaben da za a yi, amma kuma na yi sa’ar samun  karramawa a matsayin “Best supporting role” an gabatar sunayen mu bakwai ne. A Katsina aka yi taron na “Arewa Mobie Award” AMA a ranar 12 ga watan Mayu 2019. To da yake ina son harkar Fim, duk wata hidimar ‘yan fim na kan so a ce ina ciki saboda na zama cikakke mamba, tunda ina zama a Abuja ne kuma yawancin harkokin Fim na gudana ne a Kano da Kaduna da kuma garin Jos. Saboda haka duk abin da za a yi, indai aka ce taro ne na ‘yan fim, na kan yi kokarin in ga na kai kai na saboda in zama “Part of ‘yan fim”, to amma ko da na tafi Katsina na tafi ne ban sa ran nine za a ba “Award” din ba, saboda kusan mu bakwai ne  kuma dukkaninsu manyan jarumai ne, dan ko lokacin da na ji an kira suna na ban dauka suna na bane sai da aka sake kira, saboda ban taba tsammanin ni za a ba wannan Award din ba.  Sai aka bani a matsayin ‘Best Supporting Character’ wato “Best Actor in Supporting Role”.

 

Mene ne kake fatan cimmawa a harkar fim?

Babban burin abin da na fi fata ni shi ne zan so malaman addini kada su tsaya gefe suna sukar harkar fim, su shigo cikin harkar fim inda gyara yake su gyara, saboda yanzu shi wa’azi in ka dan sanya hikima mutane sun fi karbarsa, saboda haka da malaman addini zasu shigo cikin harkar fim su sa dukiyarsu mu habbaka addini ta fuskar wasannin kwaikwayo wannan shi ne babban abin da nake fata. Duk in muka yi fim ya zama daga karshe an sami wani sako da muka aikawa al’umma ko a addinance ko a al’adance. Wannan shi ne babban burina, sai na biyu kullum ina burin a ce masu kallon wasannin kwaikwayo su daina kallon mu a matsayin ‘yan wasan kwaikwayo su rika kallon mu a matsayin masu kawo fadakarwa, mutum ya lura da menene ya faru da Ali Nuhu kuma wane da na sani ya same shi kuma menene ya faru da Adamu Zango, Idan aka kalla hakan, sai jama’a su canza halayyarsu su zama mutanen kirki.

 

Ga kuma abokanan aikin ka ‘yan fim. wace shawara kake da shi gare su?

A duk da dai ni karami ne a cikin su, amma idan zan basu shawara ko in ce idan zan bamu shawara, shi ne farko mu hada kanmu, farko mu hada kanmu a cikin ita masana’antar kuma mu tabbatar da cewa duk abinda za mu yi, bamu yi abin da zai sabawa addini da al’ada ba, saboda mu din nan masu addini ne da al’ada, kar mu rika yin abu don son zuciya mu rika yin abu don mu taimaki al’umma ne, don haka ma muka shigo harkar.

 

Wanne kira kuma kake da shi ga gwamnati?

Gwamnati idan har zata dubemu da dubar fahimta, mu matasa ne a cikin mu akwai wadanda suka yi manyan karatu mai zurfi akwai wadanda kuma basu yi mai zurfi ba amma dai sun shigo cikin harkar, kuma gashi harkar fim wata masana’anta ce data sama wa matasa aikin yi, saboda haka inda gwamnati zata sanya hannu ta bada tallafi kamar yadda sauran kasashen duniya da suka ci gaba a harkar fim suke sanya manya- manyan kudade to ita kanta gwamnati zan so a ce ta sanya hannu ganin wani hannu ganin wani bangare ne da matasa suka sama wa kansu abin yi to ita kuma ta tallafa masu ganin ba mu tashi ba mu ce sai mun yi aikin gwamnati ba. Tunda muna da sana’o’inmu, wannan shi ne burina musamman in ta sa mana

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!