Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

yadda Dubun Wani Kasurgumin Kwarto Ta Cika A Legas  

Published

on

Jami’an ‘yan sanda dake yankin Idimu cikin jihar Legas,  wadda mataimakin kwamishi nan ‘yan sanda ACP Augustine Akika sun cafko wani mutum tsirara bayan satar hanyar shiga gidan makwabcin sa don ya kwana da matar makwabcin sa.

An ruwaito cewar, lamarin ya auku ne a kan titin dake NNPC a yankin Ejigbo cikin jihar bayan da ‘yan sanda suka kai samame a gidan.

Wanda ake zargin mai suna Mista Ben Chimaeze,inda Chimaeze ya yi kokarin baiwa mijin matar naira miliyan daya toshiyar baki amma mijin matar cewar sai dai ya biya naira miliyan biyar ko kuma ya kashe Chimaeze a cikin gidan.

Har ila yau, an ruwaito cewar Chimaeze ya jima yan jan ra’ayin matar mai suna  Nneoma duk da yana sane cewar matar aure ce.

Ance Chimaeze ya sha fita da Nneoma zuwa wajen da ake sayar da farfesu da kayan tande-tande  ya kuma sha bata kudi wanda kuma take karba.

Duk da irin wannan alherin da Chimaeze yake yiwa Nneoma, taki yarda ta kwana da Chimaeze duk da bukatar da yasha yi akan hakan.

A ranar da dubun su ta cika, ance  Nneoma ta bukaci naira 100,000 da kuma naira 50,000 da ban-da-ban wanda Chimaeze ya tura mata a cikin asusun ta ajiyar ta na banki.

Bugu da kari, Chimaeze ance ya gayyaci Nneoma zuwa wani otel don su kwana amma taki, inda ta shedawa Chimaeze cewar mijin ta sananne ne domin in suka je otel, wadanda san shi zasu iya ganin su.

An ce, Nneoma daga baya ta yanke shawarar Chimaeze yazo gidan mikin ta tunda mijin nata ya yi tattaki, inda hakan zai fi masu sauki don su kwana su hantse.

Wata majiya tace,  Chimaeze ya amince da tayin na Nneoma,inda har ya sayo mata abincin Mista Biggs don suji dadin harka.

Majiyar ta ci gaba da cewa, da Chimaeze ya iso gidan, Nneoma ta gaya masa cewar, bata son ya yi amfani da kororon roba, inda ta umarce shi ya shiga kewaye don ya watsa ruwa.

Ba tare da sanin Chimaeze ba, ashe Nneoma da mijin ta, sun nadawa Chimaeze tarko ne.

Wata majiyar ‘yan sanda ta labarto cewar, a lokacin da Chimaeze ya cikin kewayen ne, ma’aura tan da suka hada baki da ‘yan sandan suka shigo cikin gidan suka fara nada a faifan bidiyo, inda suka fara tambayar Chimaeze ko me yake yi a cikin gidan a wannan lokacin.

‘Yan sandan sun kwace sutturar Chimaeze, inda mijin Nneoma ya bashi gajeren wando san nan ‘yan sandan suka tasa keyar Chimaeze zuwa rundunar tasu.

A rundunar Chimaeze ya rubata bayanin sa, inda kuma ya amsa laifin sa cewar yaje gidan ne don ya kwana da  Nneoma bayan amincewar da Nneoma ta yi na zata bashi hadin kai alhali bai san cewar an nada masa tarko bane.

An ce mijin na Nneoma ya dage sai  Chimaeze ya bashi naira miliyan biyar, inda mijin ya umarci ‘yan sandan na shiyya ta biyu dasu ci gaba da tsare masa Chimaeze har sai in ya biya kudin.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: