’Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Al’umma A Binuwai — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

’Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Al’umma A Binuwai

Published

on


‘Yan Sanda a Jihar Binuwai sun tabbatar da kisan wani shugaban al’umma mai suna, Godwin Gbaiur, wanda wasu ‘yan bindiga suka kashe shi a jijjifin ranar Asabar a Karamar Hukumar Katsina Ala ta Jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, Moses Joel Yamu, ya ce lamarin ya auku ne da misalin karfe 6:48 a gidan mamacin ranar ta Asabar.

“Wasu ‘yan bindiga biyu, sun kashe wani mai suna, Godwin Gbajur (shugaban garin Katsina-Ala, wanda aka fi sani da, Tor Gari) a gidansa da ke anguwar GRA, da ke bayan garin Katsina Ala,” in ji shi.

Yamu ya ce, wani shaidan gani da ido, ya ce ‘yan bindigan sun zo gidan mamacin ne bisa Babura biyu, inda suka tambaye shi, ko shi ne Godwin, inda ya amsa ma su da cewa, shi ne, kawai sai suka harbe shi har lahira.

Ya ce, sun tsinto kwanson harsasan bindigar AK 47, guda 80 a wajen da lamarin ya faru, inda ya ce, binciken farko ya nu na cewa, makasan ‘yan kungiyar, Terwase Akwaza ne, wadanda aka fi da sani da, “Ghana,” wadanda suka fi kowa aikata laifuka a Jihar.

Kakakin na ‘yan sanda ya ce, su na yin duk abin da ya dace domin tabbatar da an kamo makasan domin su fuskanci shari’a.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!