An Kashe Mutum 27 A Sabon Hari A Zamfara — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Kashe Mutum 27 A Sabon Hari A Zamfara

Published

on


Rahotanni daga Zamfara sun tabbatar da kisan mutum 27 a wani mummunan harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Gidan-Labbo dake yankin Gidan-Goga a karamar hukumar Maradun ta jihar.

Sai dai Jami’in watsa labaran rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara, DSP Muhammad Shehu ya bayyana cewa mutum 7 ne hukumarsu ke da labarin an kashe a shekaran jiya.

Ya ce, wasu ‘yan ta’addan da ba a san ko su wanene bane suka kai hari dajin Malikawa dake kauyen Gidan Labbo ranar Jumma’a inda suka kashe mutane yayin da suke sharan gona a shirye shiryen fara noman bana.

“Da muka samu rahoton abin dake faruwa, nan da nan muka tura mutanen mu inda suka ga gawar mutum 7 da aka kashe”.

Ya kara da cewa, rundunar ‘yan sandan da sauran rundunoni samar da tsaro a jihar sun baza dakarunsu domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Ya kuma bukaci al’umman jihar dasu ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da zai kai ga dakile harkokin ‘yan ta’adda.

Sai dai majiyarmu daga kauyen ta tabbatar mana da cewa an kashe mutum bakwai ne a gona, bayan kuma da aka je kwaso gawarwakinsu don yi musu sutura da sallah, sai maharan suka sake dawowa inda suka kashe mutum har 27.

An ruwaito cewa, jiya Gwamna Abdul’aziz Yari, ya bayyana cewar, a halin yanzu ‘yan ta’addan suna rubuta wasikun barazana ga manoma inda suke bukatarsu su guji gonakinsu in ba haka ba zasu kashe su.

Gwamna Yari, ya yi wannan bayanin ne a yayin kaddamar da sayar da takin zamani domin harkokin noman bana a garin Nasarawar-Burkullu dake karamar hukumar Bukkuyum. Ya ce, wannan barazanar abin takaici ne musamman ganin cewa, yawacin jama’ar jihar Zamfara manoma ne, ya kuma yi alkawarin haduwa da shugaban kasa da shugabannin rundunonin tsaro a kan matsalar.

Advertisement
Click to comment

labarai