Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Sace Tare Da Sayar Da ‘Yar Shekara Biyar A Kan Naira 30,000

Published

on

Rundunar tsaron farin kaya ta musamman (OPSH), da aka dorawa nauyin tabbatar da zaman lafiya a jihohin Filato da Bauchi da kuma Kudancin jahar Kaduna ta yi bajin kolin gungun mutanen da ake zargi masu sace mutane ne akan mayar da ‘yar shekaru biyar mai suna Fabour Shagun dake yankin Bukuru a cikin karamar hukumar Jos ta Kudu dake jihar a matsain ‘yar su.

Lokacin da yake baje kolin wadanda ake zargin a shalkwatar rundunar dake garin Jos, kakakin rundunar Majo Umar Adams ya ce, jami’an sun cafko wani mai suna Kenneth Nnanna a ranar litinin ta 21 ga watan Mayun 2018, da yarinyar a karamar hukumar  Sanga dake cikin jahar Kaduna.

Majo Umar yaci gaba da cewa, wanda ake zargin an cafko shi ne da misalin karfe  11 na dare tare da yarinyar a cikin motar sa,inda da jami’an suke tuhumi  Kenneth, ya gaza fadar sunan yarinyar duk da ikirarin da Kenneth ya yi cewar yarinyar ‘yar sace.

A cewar Majo Umar, wanda ake zargin ya yi kokarin arcewa daga gun da abin ya auku lokacin da aka cafke shi, inda aka kawo shi zuwa rundunar don zurfafa bincike.

Majo Umar ya sanar da cewar, “Kenneth ya sanar da cewar ya sato yarinyar ne tare da taimakon wata matar aure mai suna Esther Dabid, wadda kawa ce ga mahaifiyar yarinyar bayan da ya biya  Esther Dabid naira 30,000.

Ya sanar da cewar, za’a mika wanda ake zargin ga hukumar data dace don zurfafa bincike.

Wanda ake zargin Kenneth Nnanna, ya shedawa kafar Daily Post cewar, wani mai suna Mista Emaka ne ya tuntube shi don ya dauki yarinyar a matsayin mayar da ita a zaman ‘yar sa  akan 58,000, inda ya yanke shawarar haduwa da Esther Dabid, mai ‘ya ya hudu in har zata bayar da

daya daga cikin ‘yayanta mata.

A cewar Kenneth, Esther ta ce masu su hadu a Bukuru,inda ta nuna masa yarinyar ‘yar shekara Fabour,inda ya ja hankalin yarinyar data biyo shi, bayan ya biyar naira 30, 000.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: