Fadar Shugaban Kasa Na Ci Gaba Da Yi Wa Obasanjo Fallasa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Fadar Shugaban Kasa Na Ci Gaba Da Yi Wa Obasanjo Fallasa

Published

on


Gwamnatin Buhari ta kara kaimi wajen kai hare-hare da farmaki ga tsohon Shugaban kasannan, Cif Olusegun Obasanjo, inda take zarginsa da kitsa tuggun da ya kai ga tsige gwamnoni biyar a shekarar 2000.

Mai magana da yawun fadar ta Shugaban kasa, Garba Shehu, ne ya fadi hakan ranar Lahadi da yamma cikin wata sanarwa da ya baiwa kafar sadarwa ta, ‘PREMIUM TIMES,’ inda yake cewa, mulkin Obasanjo na tsakanin shekarar, 1999 zuwa 2007, shi ya jefa kasarnan cikin wani mummunan yanayi sabili da yadda ya yi ta yi wa tsarin mulki karan tsaye.

Garba Shehu, ya zargi tsohon Shugaban kasan da iza wutar tsige tsaffin gwamnaoni, Joshua Dariye, Rashidi Ladoja, Peter Obi, Chris Ngige da Ayo Fayose, daga kujerun su. Dukkan su gwamnoni ne a Jihohin, Plateau, Oyo, Anambra, Anambra da Ekiti, bi-da-bi.

Ya kuma bayar da misalan taka tsarin mulkin da Obasanjon ya yi.

“’Yan Majalisu biyar ne suka taru da karfe 6:00 na safe suka tsige gwamna Dariye, na Jihar Flatau, ’Yan Majalisu 18 cikin 32 ne suka taru suka tsige gwamna Ladoja, na Jihar Oyo, a Jihar Anambra, ta hakan aka tsige gwamna Obi, na Jam’iyyar APGA, da misalin karfe 5:00 na asubahi, tare da ‘yan Majalisun da ba su kai adadin daya bisa uku ba, kamar yadda tsarin mulki ya tanada.

“Laifinsa kawai ya ki ya yi kari kan kasafin kudin Jihar shi. Shugaban gwamnatin na PDP, ya shaidawa Obi, ya manta da batun sake zabensa a 2007, in dai ba zai koma Jam’iyyar ta PDP ba, domin kuwa a cewar sa, ba zai taba mara ma wanda ba dan Jam’iyyar PDP baya ba.

“A Jihar Ekiti, gwamna Fayose, ya fuskanci tuhume-tuhumen rub da ciki kan kudade, da kuma na kisan kai, kin da ya yi na karba wa Shugaban kasan kan neman da ya yi masa na tsige Fayose kadai a bar mataimakiyarsa Madam Olujimi, wacce take Sanata ce ita yanzun, sai Obasanjon ya shelanta kafa dokar ta baci a Jihar bisa ikirarin cewa Jihar ta fada cikin yamutsi.

“Sai ya nada Janar Adetunji Olorin, a matsayin kantoman Jihar a ranar 19 ga watan Oktoba. Haka ya yi amfani da wasu ‘yan cikin gida a Jihar Anambra, domin tsige gwamna Ngige, ta hanyar amfani da wasu ‘yan bangan da gwamnatinsa ta dauki nauyin su.

“Ban gaji tsaurin ido ba,” kamar yanda akan ce, me zai kai wannan Jam’iyyar ta rubuta wa Majalisar dinkin duniya takarda, tana karyar cewa ana karya tsarin mulki ana yi wa dimokuradiyya karan tsaye? In ji Shehu Garba.

Jawabin na Shehu Garba, duk yana cikin cacan bakin da ake ta yi ne a tsakanin Shugaba Buhari da Obasanjo, inda Shugaba Buhari ya zargi Obasanjon da lalata dala bilyan 16 wajen aiwatar da aikin samar da lantarki, ba tare da an kai ga wata nasara ba.

Inda shi kuma Obasanjo ya mayar da martani ga Shugaban kasan, inda ya siffanta shi da jahilci kan zargin da ya yi masa na salwantar da kudaden wadanda kwamitocin bincike suka yi ta wanke shi a kansu a baya.

Takun sakan na su dai ya samo asali ne tun daga lokacin da Obasanjon ya rubuta wa Shugaba Buhari wasika inda yake shawartan sa da ka da ya nemi sake tsayawa takara a babban zaben 2019 don gudun jin kunya.

Shawarar da Shugaba Buhari ya yi fatali da ita, wacce hatta abokaninsa na aikin Soja kamar su Ibrahim Babangida duk sun ba shi wannan shawarar sabili da halinsa na rashin lafiya. A baya dai ya kwashe sama da kwanaki 172 ne ana duba lafiyarsa a wajen kasarnan, wanda hakan ya zama tarihi a tsakankanin Shugaban kasannan da suka gabata.

Jam’iyyar ta PDP ta yi watsi da duk wannan maganan ta Shehu Garba, ta siffanta maganan na shi da shirme, tana mai cewa duk za su koma ne kan Shugaban na shi.

“Duk wannan zage-zagen da wasa da hankalin da yake yi kan tsaffin Shugabannin ba zai taimaka masa cin zaben ba a 2019,” in ji Kakakin Jam’iyyar adawan, Kola Ologbondiyan, kamar yadda ya shaidawa kafar yada labarai ta PREMIUM TIMES, ta waya a ranar Lahadi da dare.

Ya kuma nu na mamakin sa kan yadda gwamnatin ta canza matakin nata kan Obasanjon, mutumin da suka rika dasawa da shi a shekarar 2015 lokacin da Buharin ya nemi goyon bayansa domin neman tsayawa takara.

Obasanjo ya goya wa Buhari baya a kamfen dinsa na shekarar 2015, inda ya yi ta kalaman batanci domin raunana Shugaban lokacin Jonathan.

Obasanjo, ya fice daga Jam’iyyar PDP ne a shekarar 2014, tun daga lokacin kuma ya ci gaba da nisanta kansa daga Jam’iyyar ta PDP.

Ya bayar da misalin ketarewar da Buhari ya yi wa Majalisar kasa wajen sayan Jiragen saman yaki a farkon wannan shekarar, a matsayin daya daga cikin karan tsayen da ya yi wa tsarin mulki.

“Ya aikata abubuwa masu yawa, da suka mayar da Dimokuradiyyarmu tamkar mulkin Soja,” in ji Mista Ologbondiyan.

“Kwanaki kadan da suka shige, yake bugun kirjin cewa da yana da hali da ya kulle bakidayan ‘yan siyasa a gidan yari,” ka ga wannan maganan na shi ta saba wa dimokuradiyya. Domin a tsari irin na dimokuradiyya, duk wanda ake zargi ba mai laifi ne shi ba, har sai shari’a ta tabbatar da laifin na shi.

 

Advertisement
Click to comment

labarai