Hukumar Kare Hakkin Dan Adam Ta Gargadi Sojojin Nijeriya Kan Hakkin Fararen Hula — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Hukumar Kare Hakkin Dan Adam Ta Gargadi Sojojin Nijeriya Kan Hakkin Fararen Hula

Published

on


Hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa, NHRC, ta shawarci Sojojin Nijeriya da su kare dukkanin hakkin fararen hula a lokacin da suke gudanar da ayyukansu, ko su fuskanci hukunci.

Babban Sakataren hukumar, Tony Ojukwu, ne ya shaida wa manema labarai hakan a Yola, inda ya ce kasarnan ta sanya hannu a kan dokar kare hakkin duk mazaunin cikinta.

A cewar shi, gwamnati ke da hakkin karewa, daukakawa da kuma tabbatar da hakkin kowane dan kasa.

Mista Ojukwu ya ce, gwamnatin tarayya ba ta aminta da keta hakkin dan adama ba, don haka, sai ya shawarci Sojojin da su tsaya kan dokokinsu na aiki, su kuma guji keta mutuncin dan adam a lokutan da suke gudanar da ayyukan na su.

“Mu kiyaye hakkin kowa a lokutan da muke yin aiki, mu kuma sani, duk abin da muka aikata za mu amsa tambaya a kansa.”

Kan rahoton kwannan nan na kungiyar kare hakkin dan adam ta duniya, ‘Amnesty International,’ inda kungiyar ta yi zargin cin zarafin da Sojojin ke yi wa al’umma a cikin kasarnan, cewa ya yi, zargin ba shi da tushe, domin bai bayar da wasu misalai na hakan ba.

A cewarsa, inda an sami bayanin wani abu mai kama da hakan, tabbas da an bincika kuma an hori duk mai hannu a cikinsa yadda ya dace.

Ojukwu ya ce, ayyukan hukumar na su, ba su takaita kan Sojoji ba kadai, sun shafi dukkanin al’umma ne.

“Ba wai mun sanya wa Sojoji ido ne kadai ba, a’a, kokarinmu shi ne yadda za mu hada kai mu taimaki juna.

“Kare mutane shi ne babban aikinmu, don haka idan har Sojoji za su tsayu da ayyukan kare al’umma hakan zai rage asarar rayuka da ake ta yi.

 

Advertisement
Click to comment

labarai