Musulunci Da Dimokradiyya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MAKALAR YAU

Musulunci Da Dimokradiyya

Published

on


dahiraliyualiyu@gmail.com                    +2349039128220 (Tes Kawai)

Gabatarwa:

Na gabatar da wannan mukala mai taken “Musulunci Da Dimokradiyya” a dai-dai lokacin da bukatar hakan ta taso a shafukan sada zumunta, musamman na Facebook, tsakanin masu ganin babu alakar musulmi da dimokradiyya da kuma masu ganin ai dimokradiyyar dukanta addini ce. A tawa gudunmawar, na nuna alakar addini da dimokradiyyar bisa duba hakikokin tarihin Musulunci da kuma wasu daga nassoshin da sukai magana akan tsarin mulki. Da yake an riga an yi wa kalmar mummunar fassara, a wannan mukala na so na bayyana cewa dimokradiyya bata nufin mutane su mulki kansu. Dimokradiyya na nufin tsarin cigaban da mafi yawa suka aminta su tafi akai domin masalahar rayuwarsu. Larabawa kam suna cewa : sunaye basu da illa akan kansu. Wato dai bai kamata mu dinga ganin sunayen abubuwa muna saurin yanke musu hukunci ba. Kamata yayi duk abinda muka gani to mu auna ma’anar ba sunan da yazo dashi ba. Kada na cika mai karatu da gabatarwa. Bara na bari mai karatu ya shiga fagen don nutso acikin ruwan

Tsarin “shura” dadadden abu ne a tarihin Musulunci, amma hanyoyin tabbatar da shurar ne ba’a kayyade mana ba. Abu ne a bayyane cewa hanyoyin tabbatar da tsarin mulki yana canjawa dai-dai da yanayin gurin zaman mutane. Muna gani cewa wasu kasashen da suka cigaba ma suna iya canja tsarin mulkinsu dai-dai da yadda za su iya tabbatar da jin dadin rayuwarsu. Shura a tsarin Musulunci hanya ce da ake so a isar da adalci acikinta. Da shari’ar Musulunci da tsarin “secular democracy” duk hanyoyine da manufarsu kawai a tabbatar da adalci. Idan ya kasance bisa tsarin shari’ar Musulunci babu abinda za’a tarar sai zalinci, kisa, kwace da danne hakkoki to gwara “secularism” sau dubu akanta. Wannan shi ne abinda malamai suka hadu akai na cewa gwara shugaba kafiri matukar zai adalci akan shugaba musulmi matukar zalinci zai aikata.

Shura tana bayyana ta siffofi dayawa ba tsari guda daya da zai bawa malaman addini damar cin-kare-ba-babbaka ba. Mafi muhimmanci shi ne a tabbatar da wani tsari da hanyoyi da zasu tabbatar da cewa shurar tana aiki a zahiri. Ko ta hanyar zabe, ko ta hanyar tura wakilai, ko ta hanyar shawara a tsakanin manya ko talakawa da masu kudi. Wannan ana son gabatarwa ne don kada a danne hakkin raunana ko a hana masu karancin  jama’a magana. Daga tsarin din dimokradiyya ko a yau shine tana bawa masu karancin magoya baya damar su bayyana ra’ayinsu don a duba fahimta kuma shura ta inganta. Wannan tsarin addini ne ba wai yi wa mutum daya biyayya ko yayi daidai ko bai ba.

Na duba Alkur’ani baki daya sai naga yana magana akan “Ulul amr” wato masu rike da shugabanci amma bai taba cewa “waliyyul amr” ba! Wannan yana nunamaka cewa a tsarin addinin Musulunci mulki na jama’a ne ba na mutum daya ba. Jama’a su ne za su zabi wanda zai jagorancesu kuma bisa ra’ayinsu zai shugabanci ba wai shi kadai yace zai dinga hukunci bisa fahimtar da ya yi wa nassi ba. Haka muka gani a tarihin sayyidi Ali da mulkinsa shiryayye. Imam Aliyu bai halatta jinin wadanda suka ki binsa ba ko tarwatsa jama’arsu ba. Abinda aka rawaito ya fada shi ne, “ku tabbata akan ra’ayinku matukar ba za ku tada hayaniya ba kuma ba za ku zubar da jini ba”. Wannan ita ce maganar da ya gayawa Khawarij domin babban mutum yana kokarin ginawa ne ba wai rusawa ba. Abdullahi bn Shaddad yana cewa : “wallahi ba mu yake su ba har sai da suka zubar da jini kuma suka dinga kwace”.

Tamkar kowane mulki, dimokradiyya tana da wadanda suke wasa da ita. Masu son juya tunani da sunanta kuma su raina hankali a bayanta. Akwai wadanda suke son kashe mutane kuma da sunan kare mutane! Akwai mai son rushe yanci da sunan kare yanci! Acikin dimokradiyya akwai wannan. Haka acikin addini akwai mutanen da suke tafiya don neman kudi da tara duniya da sunan ayoyin Allah! Da masu kisa, yanka mutane da dasa boma-bomai da sunan tabbatar da shari’a. Ba zai zama adalci a zagi dimokradiyya don kawai wasu basa amfani da ita daidai ba kamar yadda bai dace mu zagi shari’a saboda acikin masu cewa za su tabbatar da ita akwai Abubakar Shekau da Abubakar Albaghdadiy ba.

Wadansu ba su fahimci Dimokradiyya ba sai suka ce ai tsari ne da yake nufin jama’a su mulki kansu da kansu. Su kuma masu tutiyar dabbaka shari’a suna ganin za su tabbatar da tsarin Allah ne ba tsarin jama’a ba. Abinda ba su fahimta ba shi ne, ai tsarin jama’a shi ne tsarin Allah! Tsarin da zai taimaki jama’a kuma suke so to shi ne tsarin Allah. Lokacin da Allah yace a rantamasa bashi wa yace a bawa? Jama’a! Lokacin da Allah yace a gina dakinsa su waye aciki? Jama’a! Don haka iyakokin Allah su ne iyakokin jama’a. Abinda jama’a suka nutsu da shi shine tsarin Allah. Bai halatta ga dayanmu yace shi kadai ne yasan tsarin Allah ba amma banda sauran jama’a. Alkur’ani littafin Allah ne amma fahimtarsa sai jama’a sun taru. Babu wani mutum ko wata kungiya guda daya da zata ce ita ta fahimci maganar Allah dukanta!

Wadanda suke cewa tsarin “Democracy” ya faro ne daga masana falsafar Greek sun yi kuskure. Kalmar ce kawai turawa suka dauko daga can amma tsarin yana nan acikin addini. Addinin Musulunci yana bukatar tsarin mulkin jama’a don jama’a ne ba wai tsarin fahimtar wani don ya mallake jama’a ba. Acikin Alkur’ani Allah ya bamu labarin Fir’auna yana cewa shi ba abinda jama’arsa za su gani sai abinda ya fara gani! Amma Allah ya bamu labarin Bilkisu sai yace ita kuma tana cewa da jama’arta su bata ra’ayinsu kafin ta yanke hukunci! Kenan masu son su dauko littafin addini ba tare da bin ra’ayin jama’a ba suna bin hanyar Fir’auna ne tunda suna ganin iya ra’ayinsu shi ne addini kuma shi ne shari’a! Tabbas mutane su ne suka fi sanin sha’anin duniyarsu, don haka babu wani mutum daya da zai tilasawa wasu bin fahimtarsa da sunan yakar dimokradiyya.

Akwai wadanda sun haddace nassoshi ne kawai ba tare da tunanin gane manufofinsu ba, me addini zai yi da irin wadannan? Addini yana bukatar wadanda suka san shi ba iya ga sunaye ko kalmomi ba. Wanda yake yakar adalci da sunan rusa dimokradiyya bai fahimci addini ba. Wanda yake kaunar zalinci da zubar da jini da sunan shari’a shi ma bai fahimci addini ba. Addini agunsa bai wuce sunaye ba amma ba manufofi ba. Addini yafi bukatar manufofi ba sunaye ba. In banda zalincin masu tutiyar tabbatar da shari’a babu yadda za’ai mutane su karbi dimokradiyya fiye da shari’a. Kenan dai masu tutiyar tabbatar da shari’a sai sun gane dalilin da yasa jama’a suka fi son dimokradiyya fiye da tsarinsu saboda shari’arsu suna ce kawai amma babu manufofi. Lokacin da zaka dinga yakar yancin dan Adam da sunan tabbatar da shari’a hakan yana nufin baka kaunar yancin dan Adam kenan. Ta yaya kake zaton zaka samu karbuwa agun mutumin da yake son yanci fiye da komai a rayuwarsa? Akwai bukatar mu sake duba ma’anar ayoyi daidai da zamaninmu ba komawa zamanin baya don neman amsar abinda yake damunmu a yau ba. Mutanen baya suna da tsarin shurarsu kuma muma muna da tsarin tamu.

Rufewa :

Ku turomin da fahimtocinku, shawarwarinku da kuma ra’ayoyinku ta imel dina dake sama. Wadanda sukai bayani na ilimi za su samu damar samun fage a shafin Mukalar Talata a wannan jarida.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!