Matsalar Mulkin Nijeriya: Rashin Amfani Da Harshen Hausa (1) — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Matsalar Mulkin Nijeriya: Rashin Amfani Da Harshen Hausa (1)

Published

on


Gabatarwa

Tun shekarar 1960 da Nijeriya ta samu ‘yancin kai, ta ci gaba da dauwama cikin kangin bauta bangaren Mulki, da Siyasa, da Zamantakewa da Harshe, da Tattalin Arzikinta. Inda ake gudanar da duk huldodinta na ci gaba da bakon Harshe wato Ingilishi. Wannan ya sanya jama’a da ake mulka, da ita kanta gwamnati da ke mulkin ke da matsala ta fahimtar ainihin tsarin mulkin Nijeriya, da dakile ci gaban Nijeriya.

Bangarorin gwamnati guda uku da ake da su, bangaren Zartaswa, da na ‘Yan majalisa, da bagaren Shari’a, duk suna gudana ne cikin Harshen Ingilishi.

Me Kundin tsarin mulkin kasarnan ya fadi a game da amfani da Harshen Hausa a Majalisun Dokoki na Tarayya da na jihohi?

Sashe na 55 na Kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 cewa ya yi:

‘Za a gudanar da harkokin Majalisar Dokoki ta Tarayya cikin Harshen Ingilishi, da Hausa, da Inyamuranci da Yarbanci idan an yi wadataccen shirin yin hakan’

Amma hakan ake yi kuwa? Anya an taba gwada hakan kuwa? Ba abin mamaki ba ne a majalisunmu na dokoki muke ganin ‘yan dimama kujera birjik, da ke da sako daga jama’ar da suke wakilta, ko kudirin doka, ko ba da gudunmawa ga muhawara, da ke da matukar muhimmanci ga kasa da ci gaban al’uma, amma saboda suna tsoron tashi su yi turanci/Ingilishi a musu dariya, sai su yi zamansu ba sa cewa uffan. Wannan matsala ita ce ta jefa kasarnan cikin halin da ake ciki na ni-‘ya-su. Ba gaba ba baya, Dimokradiyyar ta zama ta ci gaban mai hakar rijiya, domin har yanzun talakawa ba su shaida ba.

Haka nan sashe na 97 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya yana cewa:

‘Za a gudanar da sha’anin Majalisar dokoki ta jiha cikin Ingilishi, amma Majalisa tana iya karawa wani Harshen ko wasu Harsunan da ake amfani da su a wannan jihar’

Majalisun dokoki na jihohi guda nawa ne a kasarnan suka taba gwada hakan?

Wani manazarci mai suna Emenanjo ya yi bayanin cewa babu wata al’uma ta duniya da ta taba ci gaba a rayuwarta muddin  tana amfani da Harshen aro na Nasara. Ya ce yawancin kas ashen Afirka sun ci gaba da durkushewa ne saboda sun rungumi Harshen da ba nasu ba, sun ara sun yafa sun mayar da nasu tsohon yayi.

Hakan ta sa ‘Yan majalisa yin magana da Ingilishin da har su mutu ba su iya shi ba, balle su nakalce shi, su ma talakawan ba su iya Harshen ba, ballantana su fahimce sa, har su san inda aka dosa da su.

Mece ce Gwamnati?

Gwamnati na nufin wata tsararriyar hanya da aka tanatar domin gudanar da sha’anin jama’a. Hanya ce ta bullo da wasu manufofi domin tabbatar da ana adalci ga kowa, domin kare wanda ba shi da karfi daga mai karfi, da kare talaka daga mai kudi. Don haka ake bukatar wani tsari da zai tafiyar da harkokin kowa da kowa a kullu yaumin bukatar hakan ta taso.

Gwamnati tana da bangarori uku kuma kowanne bangare akwai aikinsa kamar yadda tsarin muki ya fayyace.

  1. Bangaren Zartaswa da ke da hakkin yin tsare-tsare ko dokoki da aiwatar da su.
  2. Bangaren Majalisar dokoki, da su ne ke yin doka,
  3. Bangaren Shari’a da shi ne ke da alhakin fassara doka.

Gwamnati ce aka dorawa karfin ikon gudanar da sha’anin jama. Ita ke da alhakin tabbatar da dorewar tsaro da zaman lafiya. Duk abinda gwamnati ke yi, tana yi ne domin kyautata jin dadin ilahirin al’uma.

Ya kamata a ce gwamnati na tafiya tare da jama’a a yawacin aikace-aikacenta da take gudanarwa. Sai dai ya za a iya cimma hakan idan gwamnati na gudanar da komai cikin Harshen da bako ne ga jama’arta?

 

Wadanne Ayyuka ne suka rataya a wuyan gwamnati?

Gwamnati ce ke da hakkin yin dokoki a kasa, domin tabbatar da zaman lafiya da oda a cikin al’uma. Har ila yau hakkin gwamnati ne ta samar da abubuwan kyautata jin dadi ko more rayuwa, da dorewar doka da oda, da kare kasa, da rayuka da dukiyar jama’a, da samar da aikin yi, da tsara tsare-tsare da aiwatar da su, da daukaka aikace-aikace na tattalin arziki kamar su hanyoyin mota, da layukan dogo, da tashoshin jiragen sama da na ruwa da sauransu. Ita ke samar da ayyukan jinkaid a harkokin kasuwani da walwala.

Har ila yau gwamnati ke kula da al’amuran harkokin waje da tabbatar da adalci.

Bangaren shari’a ke sasanta duk wata takaddama tsakanin mutum da mutum, da kuma tsakanin mutum da gwamnati.

Dole ne a sha’anin gudanar da gwamnati a yi la’akari da bambance-bancen da ke tsakanin jama’a, da bukatar tafiya tare da kowa, wato damawa da kowa, su kuma jama’a su zama masu biyayya.

Sai dai ta yaya gwamnati za ta iya sanya kowa ya san ana damawa da shi, har su mata biyayya idan jama’a sun jahilci harshen da ake amfani da shi wajen jan ragamarsu?

 

Mece ce dangantakar Harshen Hausa da ci gaban kasa?

Muddin ana son bahaushe ya fahimci ayyukan ci gaba da gwamnati ke gudanarwa, dole a gabatar masa da komai dalla-dalla a cikin Hausa. Ta Harshe ne ake furta manufofi da tsare-tsare, da aiwatar da su. In har ana so ci gaban tattalin arziki ya yi tasiri ga rayuwar talaka, dole a gudanar da koma dalla-dalla cikin harshen Hausa. In har ana son gudanar da ayyukan da za su kyautata jin dadin talakan kasa, muddin ana bukatar bullo da al’amuran ci gaban masana’antu ga jama’a, sai an kasa komai a faifai cikin harshen da kowa ya fahimta, sannan a kai ga nasara.

Ba karamar asarar Hausa ake yi ba, a matsayinta ta sinadari ko gadar takawa domin tsallakawa ga ci gaban kimiyya da fasaha. Tarihin wayewar bahaushe, na nan tattare da harshensa na Hausa. Harshen Hausa babban jigo ne tsakanin gwamnati da jama’arta. Harshen Hausa ginshiki ne na tsarin zamantakewa da siyasa, domin kuwa babu wata dabara ta siyasa ko zamantakewa da mutum ko kungiya zai su tsara ta har ta kai ga nasara ko kankama ba tare da harshen Hausa ba. Hausarnan dai ita ce ko’ina.

Za mu cigaba a mako mai zuwa

 

Advertisement
Click to comment

labarai