Nau’o’i Da Salailan Fassara A Idon Masana Da Manazarta (5) — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

ADABI

Nau’o’i Da Salailan Fassara A Idon Masana Da Manazarta (5)

Published

on


Ida kuwa aka ce jimla mai kunshe da maganar hikima to ana nufin cikakkiyar Magana kuma dunkulalliya wadda take da ke babbiyar ma’ana. (Sarbi 2005:10/2008:100). Don haka, yadda ake sanin kalma da yadda akae amfani da ita a cikin Magana, haka ake sanin maganar hikima da yadda ake yin amfani da ita a cikin Magana. To sai dai ita maganar hikima, yadda take a cikin kowane harshe, haka ake fadarta bat a sauya wa kamar yadda sauran jimloli suke yi . Misali, ana  iya cewa zanta ko tafiya zan yi ko zan je. Amma mai makon shurin masaki babau dama a ce haurin masaki saboda tunanin cewa, shiuri da hauri ma’anarsu daya. Amma ana iya cewa, ya shure ni ko ya haure ni. Haka kuma babu dama a ce kwanta hagu/ hauni mai makon kwanta dama don kawai an san cewa da dama da hagu duk sassan jiki ne. Saboda haka, masu cewa a fede biri har bindi/ jela su gane cewa fadar haka ba daidai ba ne. sai dai a fadi maganar hikima yadda take, watau a fede biri har wutsiya, ma’ana a fadi komai da komai.

Saboda haka, ida ana son fassara maganar hikima, to sai an yi taka-tsantsan. Idan kuwa bah aka ba  to babu mamaki a kaucewa ma’ana ta asali(wadda take cikin tushen fassara) zuwa wata ma’ana daban(a cikin harshen fassara). Yin hakan kuwa babban kuskure ne a cikin aikin fassara.

Kafin a ci gaba, ya kamata a bayyana kamanci da kuma bambancin da tsakanin maganar hikima da kuma Karin Magana domin tantance tsakaninsu. Da farko dai dukkaninsu hanyoyi ne na dunkule harshe(Magana) a cikin zance. Sannan yawanci sukan kunshi ma’ana mai fadi kuma kebabbiya. Dangane da bambancinsu kuwa, Karin Magana cikakkiyar jimla ce mai cin gashin kanta. Amma maganar hikima wani yanki ne na jimla. Misalai Karin Magana:

Hausa:       Komi dadin talala, saki ya fi ta.

English:      Independence is preferable to the most benebolent Subjugation.

Ko kuma:

Hausa:      Saboda kaza bay a hana a yanka kaza.

Inglish:      Familiarity with a hen does not prebent it from  being  decapitated.

Misalin Karin Magana ken an. Amma maganar hikima, yanki ne na jimla wadda daidaikun kalmomin cikin maganar ba za su bayar da ma’anar maganar ba. Misali,

Hausa:   Gudun gara a haye wa zago.

Anan ida an lura sai a ga cewa gudu yana nufin kawar da jiki wani wuri. Hayewa na nufin hawa wani abu. Gara kuwa mace c eta wani kwaro mai launin kasa, wanda ya yi kama da tururuwa kuma yake da barnar itatuwa da ciyawa. Zago kuwa, namiji ne na wannan kwaro wanda ya fi matar barna kuma yake gina shuri. Idan an hada wadannan  kalmomi gudu da haye wad a gara da zago wuri daya dangane da ma’anar kowace daya, sai a ga cewa ba  abin da maganar ke nufi ken an ba, wato ba Magana ake a kan  gara ko zago a matsayinsu na kwari ba, balle ma a yi tunanin barin wani a kai ga wani, To run from female to the male termite: abin da ake nufi kurum shi ne:

Ingilishi:  going from bad to worse situation.

Saboda haka takwararta(ma’anarta) a cikin hikima ita ce:

Jumping from fraying pan into the fire.

Hakika, idan aka yi la’akari da yanayin maganar hikima da yadda kalmomin ciki suke rikida su samu sabuwar ma’ana, sai a ga cewa, tabbas fassara maganar hikima aiki ne da yake bukatar kwarewa da kuma jajircewa wajen bincike da karance-karance. Ba nan kadai ta takaita ba, tilas ne mai fassara ya mallaki dukkan rukunin fassara kafin ya iya fitar da ingantacciyar ma’ana. Masu iya magana na cewa, “Da rashin ta yi a kan bar araha”. A nan duk da irin shigar burtu da kalmomi suke yi a cikin maganar hikima, ana iya samar da daidaitacciya ko makusanciyar ma’anarta daga tushen fassara zuwa harshen fassara, kamar daui yadda ake iya gani a cikin bayanai masu yawa da aka fassafa daga wani harshe zuwa wani kuma maganar hikimar nan ta bayyana a nau’o’in bayanai daban-daban kamar siyasa ko tattalin arziki, ko ilimi ko zamantakewa, ko addini ko adabi da sauransu. Sannan ana fassara wadannann  nau’o’in bayanai cikin harsuna daban-daban. To amma fa idan ana son fassara maganar hikima, sannan aka yi la’akari da ma’anar kalmomin ciki kamar yadda aka sani yau da kullum, tabbas, ba za a samu ingantacciyar ma’anar maganar ba. Saboda haka salon day a fi dacewa a yi amfani das hi wajen fassara maganar hikima shi ne salon yin amfani da abokin burmi (takwararta), wato fassara maganar hikima da take cikin tushen fassara da takwararta da take cikin harshen fassara. Idan babu takwarar, ko mai fassara bai sani ba ko kuma ya sani ammbai tuna da ita ba, to sai ya yi amfani da salon fassara mai ‘yanci wato ya bayyana ma’anar  a harshen fassara. A duba (Adullahi 2001:41) da (Yakasai 2001:25) da ( Sarbi 2005:144 da 2008:98).

A wannan sashin an kawo misalan maganganun hikima da abokan burminsu daga Ingilishi zuwa Hausa. Sannan an yi irin haka daga Hausa zuwa Ingilishi domin amfanin dalibai da sauran masu sha’awar aikin fassara. Manufar anan ita ce, a amfana da sanin makama game da maganganun hikima da ake da su, da kuma salon da za iya amfani das hi wajen bayar da ma’anar maganar hikima.

Fassara maganar hikima (Ingilishi zuwa Hausa)

1a  A loss of face (humiliating act). Kamar a ce withdrawing  our first words amounts to a  loss of face.

1b Kwance (since) zane a kasuwa (yin abin kunya) kamar a ce idan muka janye maganarmu ta farko , to mun kwancewa kanmu zane a kasuwa.

2a Get  it in the neck (run into trouble). Kamar a ce if she dare abuses Sani, she will definetly get it in the neck.

2b Dandana kuda (shan wuya/ wahala). Kamar a ce:

 

Idan ta kuskura ta zagi Sani tabbasa za ta dandana kudarta.

On shank’s mare/ shake’s pony (on foot). Kamar a ce

3a I am not opportune to get a seat in the bus, so  I habe to go on sank’s mare.

3b Taka ko taki sayyada (tafiya a kasa ko a kafa). Kamar a ce:

Ban samu wuri a motar ba saboda haka zan taka sayyada.

4a Keep a straight face (refuse to laugh). Kamar a ce:

The comedian did a lot to amuse the audience but they kept a straight face.

4b (yi) fuskar shanu (bata rai ko kin yin dariya). Kmar a ce:

Cali-cali ya yi duk abin da zai iya domin ya ba masu kallonsa dariya amma sai suka yi fuskar shanu.

5a A show down (an open clash). Kamar a ce:

The workers saida that  the gobernment should pay  their allowances or face a show down.

5b  Fito-na-fito (rigima tsakanin sassa biyu). Kamar a ce:

Ma’aikatan sun ce gwamnati ta biya kudadensu na alawus ko kuma a yi fito-na-fito.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!