Bayan Shekara Uku Tare Da Buharin Najeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

Bayan Shekara Uku Tare Da Buharin Najeriya

Published

on


Kimanin shekara 15 talakan Najeriya ya kwashe ya na taya shugaban kasa, Muhammadu Buhari, fafutukar darewa kan karagar mulkin kasar ba tare da haka ta cimma ruwa ba. Amma a shekara ta 16 a na yin wannan yunkuri na fafutukar ganin Buharin ya hau, sai a ka samu nasara, inda ya tandara shugaba mai ci a wancan lokaci, Gooddluck Jonathan, da kasa. Wannan ita ce bajinta irinta ta farko a tarihin siyasar Najeriya kuma abu mai wahalar yiwuwa a siyasar Afrika ma. Buharin da Jonathan duka sun samu yabo a wajen kasashen duniya.

Buharin an yaba ma sa ne bisa jajircewarsa kan yadda duk da a baya ya na samun tazgaro wajen cimma burinsa na hawa mulkin kasar, amma hakan bai sa ya yi kasa a gwiwa ba, ya cigaba da kai bara ya na dannawa har haka ta cimma ruwa. Shi kuwa Jonathan dole ne a ka yaba ma sa, saboda ya hakura ya amshi faduwa ya mika mulki, sabanin irin yadda mafi yawan shugabannin kasashen Afrika ke yi na kin amsar faduwar zabe, wanda hakan ke haifar da asarar rayuka da dukiyoyi a kasashensu.

Najeriya ta dauki iskar murna da farin ciki, musamman daga talakawan cikinta. Wasu daga cikin talakawan Arewa ma ji su ke yi tamkar bai taba samun farin ciki a rayuwarsu irin yadda samun nasarar Buhari a 2015 ta ba shi ba. Wasu ma har hatsari su ka rika yi a ababen hawansu su na jin raunuka su na mutuwa, saboda murnar hawa mulkin Buhari.

Tabbas ba a banza talakan Najeriya ya yi wannan zumudi da murna ba. Da farko ya yi ne saboda bai gamsu da yadda a ke tafiyar da mulkin kasa a baya ba. Talaka ya na ji a ransa cewa, shugabannin baya ba adalai ba ne kuma ba su bin tsari na gaskiya wajen tafiyar mulkin kasar. A ganin talaka duk wahalar da ya ke ciki, shugabannin wancan lokaci ne su ke saka shi a ciki.

Bayan haka kuma sai talakan ya ke ganin cewa, babu mai fitar da shi daga waccan matsala face Buhari. Talakan kasa ya na karfin gwiwa kansa, ya na jin cewa, da zai samu damar sake mulkar kasar ko da kuwa zango guda ne kawai, hakika da yanzu kakarsa ta yanke saka, saboda Buhari mai gaskiya ne kuma ba zai bari wani ya aikata abinda bai kamata ba a cikin gwamnatinsa.

Wannan na daga cikin makasudi ko ginshikin da ya sa talakan Najeriya ke iya zuba kudinsa da ya saka karfinsa ya kuma bada lokacin a kan yakin neman zaben Buhari, domin a ganinsa tamkar adashi ne, wanda zai dauka, idan har ya dare karagar mulki ta hanyar samun saukin rayuwar da daidaituwar al’amuran kasa, kamar tattalin arziki, ilimi, ruwa, hanyoyi, tsaro, lafiya da sauran muhimmai kuma ginshikan rayuwa. Wannan ne ya sa ko a lokacin da gwamnatin Buhari ta janye tallafin mai, sai talakan kasar ya ki yi ma ta tawaye irin wanda ya yiwa gwamnatin Jonathan, saboda kyakkyawan zaton da ya ke yiwa Buhari kuma talakan ya ki biye wa kungiyar kwadago ta kasa a yunkurinta na tafiya yajin aiki.

A yanzu dai shekara uku kenan da cikar wancan buri, wanda shi talakan ke gani a matsayin matakin kai shi ga cimma babban burinsa na samun ingantuwar rayuwa. To, amma fa kawo yanzu za a iya cewa, ba kai ga hakan ba; karewa ma wasu na ganin cewa, talaka bai taba tsintar kansa a matsin rayuwa na tattalin arziki irin wannan lokaci ba.

Hakan ba ya nufin gwamnatin Buhari ba ta yi komai ba, ko kusa; hakika ta yi iyaka kokarinta, musamman ta fuskar gajiyar da kungiyar Boko Haram, wacce a ’yan shekarun baya ta ke mallakar wani bangare na Najeriya. To, amma duka sauran abubuwan rayuwa a yanzu sun tsananta ne; magani ya yi tsada, abinci ya yi tsada, gidan haya ya na neman gagarar talaka, ilimi ya kasa ingantuwa.

Tabbas wasu na da ra’ayin cewa, Buhari ya dauko tafarkin dora kasar bisa tafarki nagari mai dorewa ne; shi ya sa a ke shan wannan wahala. Hakika hakan za ta iya yiwuwa, to amma a sani cewa, koda Buhari shekara takwas zai yi ya na mulki, kawo yanzu ya kusa rabin tafiyar fa, domin shekara uku daga cikin takwas ta kusa rabi kenan, amma har yanzu tsanani ne ke karuwa, kaya sai tashin gwauron zabo su ke yi, wadanda farashinsu bai tashi ba kuma kudin sayen su kullum kara wahala ya ke yi. Shin ina amfani badi ba rai?

Kenan da alama rayayyen talakan Najeriya a yanzu, ba zai

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!