Indiyanci Ne Ya Hada Dangantakata Da Finafinan Hausa –Farfesa Abdalla — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Indiyanci Ne Ya Hada Dangantakata Da Finafinan Hausa –Farfesa Abdalla

Published

on


A cigaba da tattaunawar da Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya ke kawo mu ku mako-mako tare da shugaban jami’ar NOUN, FARFESA ABDALLA UBA ADAMU, a makon jiya mun tsaya ne a inda mashahurin malamin jami’ar ya ke bayani kan yadda a ka yi ya samu takardar shaidar zama farfesa har sau biyu. A wannan makon ya dora daga inda ya tsaya, inda kuma ya tabo dalilin da ya sanya shi tsunduma nazari kan harkokin finafinan Hausa. A sha karatu lafiya:

 

To, sai a kai nazarin (naka) waje?

Eh, a ka kai takarduna da rubuce-rubucen. To, kuma Allah cikin ikonsa…

 

To, ina a ka kai a kasar wajen?

An kai Amerika, an kai Ingila, an kai Kanada…

 

An kai wa masana ne?

An kai wa masana su ka duba. Kuma duk gabadayansu babu wani Bahaushe, ba wani ma Musulmi, ba wani wanda ya san ni. Kawai abinda su ke sani (shi ne) rubutun da na ke yi. To, Allah cikin ikonsa duk su ka dawo su ka ce wannan abin ya yi. Sai jami’ar Bayero ta rubuto min takarda cewa yanzu an nada ni farfesa a ‘Media and Culture Communication’ (fannin sadarwa kan yada labarai da al’ada) a sashen ‘Mass Communication’ kuma na tashi daga ‘Education’ na koma Mass Comm, wanda ni a Mass Comm da ma can Ina da ofis. Jami’ar Bayero kuma ta bada kudi a ka kara kawata ofis din, a ka yi min bandaki, a ka yi kaza da kaza na farfesa guda. Ya zamanto mu ne farfesa na farko a wannan wajen bayan mutuwar Mike Egbon. Ya rasu (a lokacin), to sai ya zamanto ni ne farfesan farko.

 

To, duk wannan ka yi ta harkar rubuce-rubuce ne. Ya a ka yi kuma ka tsunduma a harkar finafinan Hausa?

To, wato abinda ya hada, Indiyanci ne. Brial Larkin ya na daya daga cikin mutanen da su ka zamanto sun ingiza mu a kan wannan nazarin. Shi ya rubuta wata makala a 1994, yayin da na zama farfesa (na farko), sai ya rubuta cewa, akwai kwatankwacin dangantaka tsakanin litattafan da a ke rubutawa na Hausa da kuma finafinan Indiya, wanda kuma su marubutan su ka su ba su yarda ba. Bala (Anas Babinlata) har kwanan gobe fushi ya ke da Brial Larkin, saboda ya ce su na kwaikwayon Indiya. Sai na ce, ‘a’a, Brial Larkin bai ce ku na kwaikwayon Indiya ba; cewa ya yi yadda ku ke fitar da jigo, ku ke fitar da tsarin rubutu, ku ke dire shi, ya yi daidai da irin yadda Indiyawa su ke yi, amma shi bai ce Indiyawa ne su ke kwaikwayon ku ko ku ne ku ke kwaikwayon su ba. To, daga nan a ka fara. A na hirar wannan sai wani ya ce, to ai finafinan ma da a ke yi na Hausa (a lokacin 1996/97 an dan fara), su ma akwai Indiyanci a ciki, kamar Indiya ne… Sai na ce ‘to bara mu duba mu gani’. To, ka ji inda mu ka fara… To, shi Brial Larkin ya ce akwai kwantankwacin dangantaka (tsakanin finafinan Indiya da finafinan Hausa), ni karara na fito na ce, ‘fim kaza, fim ne na Indiya kaza. Littafi kaza, fim ne kaza a ka yi’. To, ka ji inda na sam bakin jini a wajen wasu marubutan da kuma wasu ’yan fim din, saboda na ce fim (din Indiya) su ke kwafa, kuma daga baya da tafiya ta yi tafiya, su kansu masu kwafar Indiyan sai su ke ce ‘gaskiya ne Indiya mu ke kwafa kuma ba za mu daina kwafa ba har abada, saboda shi mu ka sani, shi mutane su ke so, shi ya ke kawo ma na kudii. Idan mun yi wani fim, wanda ba mu kwafa daga Indiya ba, ba ya yin ciniki. Saboda haka mu ba za mu daina kwaikwayon Indiya ba har abada, kuma wanda duk ya raina tsaiwar wata, ya hau ya gyara’.

 

Kamar sun tabbatar da maganarka kenan, maimakon su karyata?

A’a, ba su karyata ba, sun tabbatar cewa tabbas ‘mu finafinan Indiya mu ke kwafa’. Kuma ni gidana da na ke zaune a jami’ar Bayero, Allah cikin ikonsa ban san abinda ya sa ba, ’yan fim sai su ka zo su ka ce a gidan za su rika yin fim, kuma ba wani babban gida ba ne, gida ne kamar na kowa, to amma (watakila) saboda an gaji da finafinan da su ke yi a otel, sai su ka fara neman guraren da za su yi fim. To, wani sai ya roke ni don Allah na ba su gidana su yi. To, a lokacin ne na hadu da wasu daga cikin jarumai, takamaimai mata. Sai daya daga cikinsu; ba zan fadi sunanta ba, sai ta ke cewa, ‘ai Malam, ka ga fim kaza? Kaset din a ka dauka a ka ba ni, sai a ka ce akwai wata a na kiran ta kaza a fim din, to duk abinda ta yi ki zauna ki saurara. Ita za ki kwaikwaya’. To, ka ji yadda abin ya faru. Saboda haka ni karara na fito na ce akwai dangantaka tsakanin fim kaza da kaza. Yanzu bari na ba ka misali da Mohabbatain, don na nuna ma ka yadda nazarin nawa ya shigo. Mohabbatain fim ne na Amitabh Bachchan da Shahrukh Khan. Ni ban ma sani ba, don ba na kallon finafinan Indiya, don ba na kaunar finafinan Indiya ko kadan, to amma sai (Darakta) Hafizu Bello ya dauki wannan fim din ya mayar da shi (sunan) ‘So’, wanda kuma fassarar So din kamar fassarar Mohabbatain din ne. A fim din na Mohabbatain an yi shi ne a Indiya, to amma su kansu Mohabbatain din ba ainihin na Indiyan ba ne; wani fim ne na Amerika, a na kiran sa ‘Dead Poets Society’ na Robin Williams a kan wata makaranta, su Amitabh Bachchan su ka mayar da shi Mohabbatain, sai Hafizu Bello ya dauka ya mayar da shi So. Saboda haka nazarin da na yi shi ne, wane canje-canje a ka samu a sako tsakanin fitar da shi daga masu kallo a Amerika zuwa wanda Indiyawa ne za su gani zuwa kuma wanda Hausawa ne za su gani. To, ka ga irin yadda nazarin namu ya ke diddinkewa kenan.

Kazalika, wakokin Indiya za ka ga ga su nan an rera su. To, sai mu yi nazari a kan waka. Mu dauki waka sai mu ga me a ka canja. Za ka ga wani lokaci a na amfani da abinda a ke cewa ‘onomatophia’, wato kwatankwaci. To, sai ka ga ka dauki sunan wakar Indiya kuma sai ka ga sunan Hausan, ba fassarar na Indiyan ba ne, amma za ka ga ya tafi daidai-wa-daida. To, har a cikin lazafin ma idan a na wakar. Yanzu ka duba kamar wakar ko Mohabbatain, wacce su Ibro su ka yi da shi da Tsigai, wanda shi ma wata wakar Indiya ce su ka dauka su ka yi wannan. kamar yadda dai yaran Hausawa su ke dauka wakokin Indiya na da su ke cac-canja su, kamar misali ‘atahas agare kina jaho’ ita ce a ke cewa ‘har-har-har Mahadi’. To, sai ka ji yaro ya na cewa, ‘mun je yaki mun dawo, Ina Jubayya Ina Sarki’. To, wannan canje-canjen da a ke yi daga na Indiya din zuwa na Hausan shi ne alkiblata; nan na fi mayar da hankali wajen nazari a kai. Babu wani zancen an yi daidai ko ba a yi daidai ba, babu zancen yakamata a yi ko bai kamata a yi ba. Babu ruwana da wannan…

 

Kawai ka na fito da bayanai ne, mai karatu shi zai yanke hukunci?

Shi zai yanke hukunci. Dangantaka tsakanin wannan da wannan, ga yadda dangantakar ta ke. To, abinda ke ba wa Turawa mamaki kenan, sai su ce ‘ah! abin mamaki, ga shi-ga shi-ga shi-ga shi’, saboda bayan na zama farfesa na biyu sai na yi abinda a ke cewa ‘inaugural lecture’ ta biyu. Bayan na zama farfesa na farko a 1997 na yi ‘inaugural lecture’ a shekara ta 2004. Allah cikin ikonsa da na zama farfesa na biyu sai na yi tawa a 2014. Ka ga shekara 10 ne tsakani. To, a ta biyun da na yi na riga na jawo hankali ne a kan yadda a ke musanya wakoki, a ke musanya labarai na Indiya don a Hausantar da su su zama kamar na Hausa, amma kamar yadda na gaya ma ka, babu wani daidai ne ko ba daidai ba ne, an iya ko ba a iya ba.

 

To, ya a ka yi kuma daga baya a ka ga ka dan watsar da harkar finafinan Hausa a ka ga ka koma harkar Rap ko Hiphop na Hausa?

Zagi ne ya yi mi ni yawa! Kullum zagi! Kai har rediyo an fito an ce ni jahili ne! An ce ni mai karamin tunani ne! An ce ni makaryaci ne! An ce ni ban san abinda na ke yi ba!

A makon gobe za mu ji abinda ya yi zafi haka idan Allah Ya kai mu Ya nufa.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!