APC Akida: Sun Zubo Wuta Allah Ya Zubo Ruwa… — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MAKALAR YAU

APC Akida: Sun Zubo Wuta Allah Ya Zubo Ruwa…

Published

on


Maganar APC Akida na daga cikin abubuwan da suka dauki hankali musamman a kafafen yada labarai na zamani (wato Social Media) wanda ga dukkan alamu ya yi wa wasu dadi ya kuma bata wa wasu rai. Daman haka duniya take wata ranar asha zuma wata rana asha madaci.
Ita wannan magana ta APC Akida tana da asali da kuma dalilin yin ta da kuma wadanda za su amfana, sai kuma wadanda za su sha wahalarta ko kuma su rasa aikinsu, na karshe sune wadanda aka yi wa dakuwa cikin riga domin su gane cewa Annabi ya kaura, su farka daga barcin da suke yi tun da wuri.
Sai dai ga alama wannan batu ya zo da wani sabon salon siyasa a jihar Katsina inda wasu daga cikn ‘ya ‘yan jam’iyyar APC musamman wadanda suka yi takarar gwamna da sauran mukamai suka koma daga gefe guda suka fasa kuka suna cewa ba a yi masu dai dai ba.
A tarihin siyasa babu inda aka waye gari an yi wa kowa dai dai, saboda haka wasu ke ganin ba za a fara a wannan karon ba, sai dai anan ganin an kwantanta wani abun da ba a taba yi ba, inda bayan da aka gama batun yin takara wanda ya ci zabe ya bi sauran ‘yan takara ya ba su hakuri domin su zo a yi tafiyar tare da su.
Kamar yadda na ce wasu daga cikin wadanda suka kunno wuta akan maganar APC Akida suna da dalilin yin haka, babban dalili anan shi ne ba su sami yadda suke so ba, koda nine ban samu yadda nake so dole sai an gane domin yana wahalar boye wa.
Kazalika akwai wasu zarge zarge da suke yawo akan wadanda suka shirya wannan yinkuri na raba kan jam’iyyar APC a jihar Katsina, wanda su dama sun kwarai wajan neman na tuwo ta irin wannan hanya, tunda ba wani abin da suke yi kuma ba wanda ya ba su aiki.
Akwai ra’ayoyi ma banbanta tun daga lokacin da wannan maganar ta bullo daga bangaran wadanda abin ya shafa kai tsaye da kuma wadanda ba su da alaka da siyasa ko ‘yan siyasa, wannan ya ba kowa damar tofa albarkacin bakinsa game da wannan babban batu.
Sannan akwai masu ganin cewa babu abin da zai biyon APC Akida sai nadama da kuma hangen giwa zata fadi kowa ya kwashi ganima, saboda haka bari su sharewa su wane da wane hanyar idan sun amince shikenan idan kuma ba su amince ba kowa ya kama gabansa.
Haka kuma akwai bangaran masu rike da madafun iko masu ganin an zubo wuta sai abin da Allah Ya yi, wasu na ganin kamar sun ci taliyar karshe a siyasar jihar Katsina, a ya yin da wasu ke ganin wane da wane sun hana ruwa gudu saboda ya kamata a yi magninsu kowa ya sarara.Sai dai kuma, ba nan gizo ke sakar ba, ‘yan APC Akida fa, ba su da wani wuri da za su je a karbe su in banda APC, saboda suke murza gashin bakin domin ko dai a saurare su kuma su kawowa tafiyar cikas, ta hanyar samun nasu rabon.
To, amma kamar yadda na ce zamu bi su daya bayan daya muga wanene yake da ta cewa a yankin da ya fito, kuma wane tasiri suke da shi a siyasa, sannan wace irin gudunmawa suka bada kafin yanzu, ya ya suke da mutanansu, idan an bada sako suna kaiwa ko ko, domin da ganin wannan babban motsi akwai alamun an bada sako akai wa jama’a Bari mu fara da Dakta Usman Bugaje wanda ya ce lallai gwamnatin jihar Katsina mai ci yanzu bata yi ma su daidai ba, yana da gaskiya domin shi a wurinsa dai dai shi e a wayi garin ya dare kana kujerar gwamna, to daga wannan rana ne za a fara dai dai a kan ko menene a Katsina amma indai ba a yi haka ba to da sauran runa a kaba.
Dakta Usman Bugaje dan siyasa ne kwararai, kuma yana da jama’a sannan yana son kujerar gwamna, saboda yana neman yadda za ayi samu, ko dai hanyar zabansa ko kuma babban mai gidansa ya samu, suma su shana yadda ya kamata, saboda haka Usman Bugaje yana da dalilin cewa an yi ba dai dai ba, kuma gaskiyar magana ana yi ba daidai ba.
Abin da mafi yawan jama’a suke hange shi ne, wace hanya suka bi wajan ganin sun maida wannan gwamnati da suke zargi da aikata ba dai dai ta dawo cikin hayyacinta idan kuma abin ya gagara sai su bullo ta wannan sabuwar hanyar Alhaji Sada Ilu yana daya daga cikin ‘yan takara kuma kafin zuwansa ya yi takara an tabbatar masa da cewa shi ne zai yi nasarar cinye zaban fidda gwani, amma kash daga karshe an ji yana cewa daligat ya fi dan boko haram zama barazana acikin harkokin siyasa.
Babu shakka ya zo da kudin a hannu, kuma ya bi jama’a neman goyan bayan kuma zahiri an nuna masa ana yin sa, amma da yake siyasa kamar caca take ba a tashi da shi daga wasan ba, wannan ya nuna cewa Alhaji Sada Ilu yana da dalilin cewa a fasa kowa ya rasa.
Sai dai ya nuna dattako domin wadanda suka je wajansa domin tattaunawa da shi akan ya zo ayi wannan tafiyar da suke kalubalanta, babu wata tantanma sai kawai ya amince. Lallai ya nuna cewa shi ma da ne har da rabi, an yi mashi alkawari kuma an cika, shi ya sa wasu ke ganin bai kamata a ganshi cikin ma su kunno wuta a jam’iyyar APC ba.
Abubakar Sama’ila Isah Funtua shi ma ya shiga takara an kara da shi, sai dai bai jure ba, kafin rana ta fadi ya tabbatar cewa wannan harka ba irin ta su ba ce, saboda haka ya nuna hakuri tun a filin wasa. A tunanin jama’a ya barwa Allah abin, ashe da sauran rina a kaba… domin kuwa shi ma yana daga cikin wadanda suka ja daga a gefe guda watau APC Akida.
Kada a manta Abubakar Sami’ila Isha Funtua suruke ne ga madugu uban tafiya wato shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kuma da ne acikin manya wadanda ba su yafe laifi idan an taba Buhari, kuma yana da abin hannusa sai dai an ce alkawari ya yi sai idan an zabe shi sannan zai bada, da ba a zabe shi sai ya kulle bakin aljihunsa nan take.
Abdul’Azeez Labo Mahuta Ya tsaya takarar neman kujerar shugaban jam’iyyar APC amma bai yi nasara ba duk da cewa jama’a da dama sun nuna zai iya kai labari sai kawai ta canza zane, ya sha kaye kuma ya hakura, ashe hakurin damo ya yi, jira yake a samu wata dama irin wannan sai gashi ya fito a mutun ya bayyana yadda yake kallon kowa.
Yana da jama’a so sai, ya san abin da yake shi yasa ma wasu ke kallon da shi ne shugaban jam’iyyar APC da bata lalace haka ba, sai dai an ce baya dauka raini kuma yana da wahala ya rika yin biyayya sannan yaron daya daga ‘yan takarar ne wannan ya taimaka wajan dafa kasa da ya yi a lokacin zaban jam’iyyar.
Barista Abbas Machika kwararan lauya ne wanda ya san abin da yake kuma ba inda za a boye masa a siysar jihar Katsina da shi aka yi komi, da shi aka yi duk wani fadi tashi, sai dai daga karshe aka tashi da shi, lokacin da ya nemi kara tsayawa takarar dan majalisa mai wakiltar Kananan hukumomin Kankara, |Faskari da Sabuwa sai kawai aka yi masa fafalolo.
Abbas Machika ya kamata ya koma daga gefe ya ce bai yarda da duk motsi da ke tafiya cikin wannan gwamnati, sai dai ance idan an ciza to a hura, domin ya ci gajiyar jam’iyyar APC… ta yadda aka tsaya tsayin daka sai da aka kwato masa kujerarsa.
Barista Gambo Musa Danmusa shima an dama da shi, kuma ya ci albarkacin su wane da wane, sai dai an zarge shi da rashin girmama wadanda suka mara masa baya inda suka nuna masa ta yaro kyautake bata karko.
Tun kafin ya sake tsayawa takarar ya tabbatar da abin da zai faru, wannan ma na iya zama dalilin da zai sa ya ce APC Akida ya ke ba APC… to amma ya zama butulu ke nan ko ko?
Sanata Abdu ‘Yandoma Jarumin dan siyasa ne, kuma an shaida shi da cewa shi ne kadai dan siyasar da zaka gani alokacin da kake so, ba tare da shan wahala ba, sai dai an ce ko biri bai kai shi tsallake-tsallaken jam’iyyar ba wanda haka ya yi tasiri wajan lalata siyasarsa musamnnan a yankin Daura.
Har gobe yana son komawa kujerarsa ta Sanata sai dai kuma ba a san ta inda zai fara ba, kasancewar tun farko an zarge shi da yi wa jam’iyya angulu da kan zabo, bayan ya bi wasu ‘yan takara da suka yi hannun riga da nasara.
Kabir Murja Malamin siyasa wannan shi ne sunansa kuma ya cancanci wannan suna domin a yanzu babu wanda ya sha wahalar siyasa a Katsina kamar shi, haka babu kuma wanda ya ke dandana sakamakon sabawa siyasa kamar shi, saboda haka babu laifin idan ya ce APC Akida yake yi.
Sauran wadanda lokaci ba zai bari a yi bayani akan su ba, jira kawai suke giwa ta fadi su kwashi rabansu, saboda haka kullin sai sun Zubo wuta, to dai ga dukkan alamu Allah Yana zubo ruwa shi yasa ma yanzu abin ke neman wucewa ba tare da wani tasiri ba a siysar Katsina.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!