Ana Tsumayar Shelanta Dokar Ta-baci A Sashen Ilimi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

Ana Tsumayar Shelanta Dokar Ta-baci A Sashen Ilimi

Published

on


A

watan Janairu na wannan shekarar ne, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta shirya tsaf  don ayyana dokar tabaci a sashen ilimi na kasarnan a watan Afrilu na wannan shekarar. A lokacin da ya bayyana hakan, sai kuma ya bukaci dukkanin gwamnatocin jihohi da su ma su bi sahu wajen kaddamar da dokar tabacin a Jihohin su kan sashen na ilimi. A watan Maris, watau wata guda kafin kaddamar da dokar tabacin, Ministan na Ilimi, ya kara nanata aniyar gwamnatin ta tarayya a garin Lafiya ta Jihar Nasarawa, na ba gudu ba ja da baya, kan aniyar ta gwamnati na kaddamar da dokar tabacin a sashen na ilimi cikin watan Afrilun kamar yadda gwamnatin ta tarayya ta alkawarta tun da farko. Har ma ya yi nu ni da abin takaici na tulin yaranmu da ba sa zuwa makaranta, lalatattun kayan aiki a makarantun, rashin tsayayyun malamai kwararru da makamantansu, a matsayin abubuwan da suka tilasta kaddamar da dokar tabacin.

Kasantuwan rashin jin komai daga Minista Adamu Adamu, da kuma yadda gwamnatin tarayya ta rufe bakinta ta yi gum ba tare da cewa uffan ba kan batun shelanta dokar tabacin, ga shi kuma lokaci ya karato, kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa, ASUU, sai ta kalubalanci Ministan na Ilimi, inda ta nu na mashi cewa, shi fa ba yaro ne ba, ya kamata ya zama Dattijo mai fada da cikawa, ya hanzarta cika alkawarin da ya dauka na shelanta dokar tabacin  a sashen na ilimi, wanda kungiyar malaman na Jami’a ta ce, yin hakan zai sa ‘yan Nijeriya su ji cewa ashe dai akwai fata mai kyau na sake dawowar martabar ilimi a makarantun namu. Shugaban kungiyar Malaman Jami’o’in na Jami’ar Ibadan, Dakta Deji Omole, wanda shi ne ya tunatar da gwamnatin wannan alkawarin da ta dauka, ya yi nu ni da cewa, in ko dai har wannan alkawarin da Ministan ya yi, zance ne kawai irin na ‘yan siyasa, to abin takaici ne, wanda ya isa ya sanya ‘ya’yanmu su dora hannu a ka su rinka rusa kuka, don hakan na nufin cewa babu fa wata fata tagari kenan ga ‘ya’yan namu a nan gaba.

Matsayin ilimi dai a Nijeriya shekara da shekaru sai kara tabarbarewa yake yi, wanda hakan ya shafi kusan komai da ke sashen na ilimi, kama daga makarantun yara kanana, Firamare har zuwa ga manyan makarantun namu, wanda hakan ya yi sanadiyyar yawaitar yaranmu sama da milyan 11 da ke gararamba a tituna ba tare da zuwa makaranta ba, adadi mafi yawa kenan a duk wata kasa ta duniyar nan. Makarantu na masu neman kudi, watau masu zaman kansu, tuni suka sha kan makarantun na gwamnati wajen samun koyarwa nagari da kuma samar da wuraren karatun da sauran kayan aikin da suka dace a makarantun.

Maganan da muke yanzun haka, ana iya samun daliban makarantun Firamare, kai har ma da na Sakandare a Jihohi masu yawa na kasarnan da suke yin karatun na su a karkashin inuwar bishiyoyi, gine-ginen da ba a yi masu rufi ba ko kuma su na karatun ne zaune a kan dabe, wannan fa duk yana faruwa ne bayan mun yi shekaru 58 da samun ‘yancin kai. Ya kamata mu lura fa, Hukumar kula da halin da ilimi ke ciki ta duniya, UNESCO, ta bayar da shawara ne ga dukkanin kasashe, na cewa, kowace kasa ta tabbatar da akalla kashi 26 na kasafin kudinta yana tafiya ne a sashen na ilimi, amma abin takaici, mu a nan Nijeriya sashen ilimin namu ba ya samun dan abin da ya haura kashi Bakwai in ya yi wuta kashi Takwas daga kasafin kudin namu, domin a mafi yawan lokuta ma, ilimin bai samun abin da ya haura kashi Shida na kasafin kudin, wanda a hakan ma, in an bi ta daga-daga, a karshe za ka taras rabin hakan ne ma a hakikatan sashen na ilimin namu ke amfana da shi a karshen shekara. Duk maganan guda ce a Jihohi. Duk wannan yana daga cikin sanadiyyan da ya sanya babu wata Jami’a a kasarnan tamu Nijeriya da ke cikin jerin nagartattun Jami’o’in duniya 800, ko kuma ma nagartattun Jami’o’in Afrika guda goma, karin takaicin ma, ba abin mamaki ne ba ka taras da mai digiri da ya kammala karatun Jami’a a Nijeriya ga digirin shi a ka, dogogo, amma bai iya karatu ba ballantana rubutu, dalili kenan da ka ke ganin masu daukan ma’aikata suke ribibin daukar masu takardun shaidar kammala karatun su daga kasashen waje, hatta ma fa wadanda suka kammala karatun daga kasashenmu na nan Afrika, sun fi wadanda suka kammala a nan cikin gida tsada a wajen masu daukan aiki.

Ya wajaba mu bayyana cewa, daga cikin matsalolin makarantun namu na gwamnati, akwai yanda ake karkasa rabon kowace Jiha a wajen shiga makarantun.  Sannan kuma ga dan karen cuwa-cuwa da ake yi. Ana iya fahimtar dalilan da suka sanya gwamnatoci ba sa mayar da hankali ko ma suka yi watsi da makarantun na gwamnati, domin kuwa a fili yake, duk wani mai fada a ji ko mai kumbar susa, ‘ya’yan shi ba a makarantun na gwamnati suke yin karatun ba. Hakan yana nufin ‘ya’yan talakawa ne kadai suke a cikin makarantun na gwamnati.

Gwamnatocin da suka gabata sun kasa tagaza abin a zo a gani a sashen na ilimi, na tabbatar da samar da ingantattun malamai. A lokacin da a baya can, dan aji shida na makarantar Firamare, daidai yake da malaman da ke karantarwa a makarantunmu a yanzun. Baya ga batun mayar da hankalin gwamnatocin namu a kan sashen na ilimi, wani kuma bambancin da ke tsakanin takardun shaidar kammala karatun na da can da na yanzun shi ne, su takardun shaidar kammala karatun na da can, da gaske ana samun su ne kadai bisa cancanta ta hanyar yin karatun tukuru.

A yau, da aka ce za ka iya zama malamin makarantar Firamare ne in ka mallaki takardar shaidar karamar Diploma ko takardar malanta ta NCE, tare da hakan sai korar malaman ake ta yi masu dauke da wannan kwalin a sabili da ba su san komai ba, sun ma kasa cinye jarabawar da aka yi masu ta yara ‘yan aji hudu na Firamare.

Don haka, matukar dai wannan alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi, ba kuwa zancen ne na ‘yan siyasa ba, to muna jira mu gani a kas, mun yi zurum, mun zuba wa gwamnatin ta tarayya na mujiya, shin alkawarin na siyasa ne ko na dattijan kirki ne.

A nan mun dai yi imani da cewa, muhimmin sashe kamar na ilimi, ya wajaba a yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da an farfado da shi.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!