Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Yadda Aka Kauce Wa Zubar Da Jini Tsakanin Jami’an Tsaro Na  Kamfanin Topline Da Sojojin Ruwa

Published

on

Kiris ya rage a zubar da jini a yankin Ilashe daura da Ilade-Odo Atlas Cobe, lokacin da jami’an topline da suka ikirarin kamfanin NNPC ne ya basu kwangilar kare bututun mai dake yankin.

Lamarin wanda ya auku ne a ranar talatar data wuce, a shekarar 2014 ce Gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar kare bututan mai mallakar kamfanin NNPC.

Jirgin ruwa na Jami’an sojin na  ruwa, sun zagaya da wakilan kafafen yada labarai da suka fito daga sauran kafafen yada labarai don duba bututan man.

A lokacin da sojojin suka suka isa wurin, sun iske daruruwan jarkon litar mai da  aka cika su da mai  aka kuma zuba su a cikin motoci biyar kirar sports utility (SUB).

Jami’an na kamfanin topline wadanda a lokacin kansu ya yi zafi, sun kalubalanci sojojin, inda sojojin suka yi kurarin bude wuta akan kowa da kuma nufin su cinnawa jarkokin man wuta.

Sojojin sun fara rera wakokin yaki, inda su kuma jami’an na kamfanin Topline  suka fara shirin yin harbi da kuma nufin aukuwa sojojin.

An shafe kimanin  sama da mintuna arba’in ana chachar baki tsakanin sojojin da jami’an na kamfanin topline  inda jami’an kamfanin suka hana  ‘yan jaridar barin wurin kafin lamarin ya kazan ta, har suka jami’an tsaron na topline suka tare  hanyar suka fara auna ‘yan jaridar da bindiga, amma daukin da kwamandan sojojin Okon Eyo ya yi aka dakile zubar da jini.

Sojojin sun yi yunkurin kwace jarkokin man sama da 3000 dake cike da man daga gun jami’an na kamfanin topline, amma jami’an na kamfanin na topline suka ki yarda.

Man ance jami’an na kamfanin topline, sun sato shine daga bututan mai na NNPC  da ake turowa Atlas cobe dake Apapa zuwa Ejigbo zuwa  Mosemi cikin jihar  Legas zuwa jihar  Ogun.

Da aka isa sansanin sojojin kwamandan  Okon Eyo ya shedawa ‘yan jaridar sojojin zasu gana da mahukuntan na  NNPC, don sabunta daukar aikin da suka yiwa jami’an tsaron na Topline.

Eyo ya kara da cewa, sojojin zasu gano in har an baiwa tsagerun na topline damar daukar bindigogi.

A cewar sa, kun ganewa idonuwan ku abinda ya auku a Ilashe, gefen rafin inda bututun mai na  NNPC suke.

Ya bayyana cewar, Jami’an na tsaron na  topline, sunyi ikirarin cewar, an basu kwangilar kare bututun man da suka taso daga Atlas cobe zuwa garin Enigbo, Mosemi da kuma wadan da suka wuce zuwa garin Ilorin da

sauran sassan kasar nan.

A cewar sa,“ kun kuma ga abin tir din da jami’an na topline suka yiwa ‘yan sojojin wajen harzuka su don su mayar da martani.”

Kwamandan yace, “jami’an na topline sun yi ikirarin cewar, kamfanin NNPC n ya  basu kwangilar kare bututun man kuma kunga yadda suke dauke da bindigogi.

Amma kwamandan tsagerun mai suna Tiamiyu Jeremiah da aka fi sani da JayJay, wanda daga baya ya kyale ‘yan jaridar akan alkarin yin hira da ‘yan jaridar, ya yi ikirarin cewar, suna hana su gudanar da aikin su.

Yace,“mun gaji da barazanar da sojojin suke yi mana da kuma na sauran jami’an soji.

A karshe yace, “sun gaya mana cewar, zasu tsire daga ambashin mu idan man ya bace.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: