Abin Da Ya Fi Tada Min Hankali A Aikin Jarida – Bobi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Abin Da Ya Fi Tada Min Hankali A Aikin Jarida – Bobi

Published

on


A yau filin dan jarida ya zakulo wani tsohon dan jarida da ya taka rawar gani musamman a bangaren radiyo. Sunansa ba boyayye ba ne ga duk mai sauraren labarai a gidan radiyon jihar Neja a bangaren Hausa da Turanci. Ko bayan neman labarai ya gabatar da shirye- shirye da dama kamar ‘Da bazarku’ wanda ya yi fice a bangaren siyasa. Muhammad Sa’idu Bobi, haifaffen garin Bobi ne da ke karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Da farko ya fara bayani ne a kan yadda ya tsinci kansa a aikin jarida…

Maganar gaskiya da farko ba aikin jarida nai sha’awa ba, kasancewar mahaifina soja ne hakan ya ba ni sha’awar son aikin soja, duk da cewar ban samu cimma burina ba, bayan mun halarci ‘training’ har mun kai matakin karshe kwatsam sai aka ce shekaru sun ci ni, dan haka ba zan samu shiga aikin soja ba, kuma a lokacin daga karamar hukumarmu mu goma ne muka je neman aikin amma a karshe mu uku muka rage kafin nima daga karshe a dawo da ni. Cikin wadanda muka je a lokacin akwai Shehu Mariga wanda shi yanzu yana aikin yana Fatakwal da aiki. Ganin cewar ni ba raggo ba ne na fada kasuwanci inda na fara da sana’ar kayan miya daga baya kuma na fara cin kasuwannin kauye ina sayen dabbobi da hatsi ina sayarwa.

Allah cikin ikonsa na yi nasarar samun aiki da kamfanin PW a nan Chanchaga masu aikin gine-gine, na zama jami’in da ke kula da lokacin shiga da fita da tattara bayanai a kan motocin da ke shige da fice a kamfani da kuma kula da dauka ko sallamar ma’aikata. Mu muka yi aikin gadar Kpakungu ta cikin garin Minna da wasu muhimman gadoji a hanyar Bida da cikin garin Minna. Bayan shugaban kasa a lokacin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya dawo da birnin tarayya daga Legas zuwa Abuja kusan manyan gine-ginen da aka yi a birnin tarayyar wadanda PW ta yi da ni aka yi su, idan ka duba Cathedral Church na Abuja mu muka yi shi, da kuma aikin bataliyar soja ta biyu mu muka yi shi. “Bayan na bar nan kuma na dawo na cigaba da harkokina sai na hadu da wani Kawuna, wato Shuwa Muhammed Bobi wanda dan kwangila ne, na zama direbanshi kuma yana tura ni wurare dan sanya idanu a kan ayyukan da yake yi.  “Wata rana na tafi ziyara a gidan Radio lokacin yana can wajen Railway dan in ga wani sai na hadu da wani maigidana ana ce mashi Umar Muhammed wanda yanzu shi ne babban darakta na hukumar talabijin ta jiha. Na nuna mai sha’awata ta shiga aikin amma kuma da fargaba saboda na saba amsar kudi kullun ba sai wata ya kare ba. “Lokacin da na fara ba kullun nake zuwa ba, sai ya hada ni da Alhaji Aliyu Kanko Wushishi, a lokacin yana gabatar da shirin ina yi karanto masa, sai ya gabatar da shirin sai ina jina sai kuma dada sha’awar abin ya shige ni sosai, daga baya kuma aka ce a je a gwada muryata, bayan an gwada aka ce zai yi kyau da labarai, sai na koma sashen fassara.

 

Ko akwai wani kalubale da Bobi ya fuskanta a bakin aiki da ba zai manta ba?

To bayan na koma sashen labarai, na karanta labarai kamar sau uku sai aka samu matsalar maimaicin wasu kalmomi haka, sai manaja a wannan lokacin Solomon Enyaze ya ce lallai a cire ni daga wajen, sai suka yi fito na fito da wannan Umarun daga karshe sai na cigaba da karanta labaran Hausa ranakun Asabar da Lahadi, saboda labaran Asabar da Lahadi ba su cika yawa ba. Kafin daga baya kuma in koma dukkanin ranakun aiki. A sashen fassara a lokacin muna da yawa, akwai su Garba Sule, da marigayi Ibrahim Abubakar da ma wadanda ban iya ambatonsu ba ma. A hankali wasu na murabus mu kuma ana matsawa da mu har muka kai a matsayin da muke a yau, wanda sau tari akan aiko da wasika dan yin rahoton musamman wanda kuma mafi yawan lokuttan mu ake turawa. “Ganin kwazon da muka nuna a aikin sai hukumar radio ta ce, ya kamata duk wani aikin nemo labarai musamman rahotanni mu ma a rika tura mu idan an kawo gayyata, sai mu tafi mu dauko rahoto mu rubuta da turanci mu bayar. Amma abin da ya fi tada min hankali a aikin nan bai wuce idan kana hutu ba kuma a sanya ka aiki. Misali koda kana hutu sai ya zama wanda ke aiki a lokacin ya dan samu matsala kai kuma ba tare da an sanar da kai ba, ana ganin ka sai a ce kai ne za ka gudanar da aikin a lokacin, wanda kai ba a san naka uzurin ba balle a sarara ma hakan za ka daure ka je kai aikin.

Akwai abin da ya faru da ba zan taba mantawa ba, wata rana na tafi aiki na dawo, sai na hadu da wasu baki sun shigo ofis dinmu, suka ce suna bukatar in yi masu wani aiki wanda kuma an aiko su ne daga wata kungiya cewar su nemo dan jarida daga nan jihar Neja, wanda ake son ya wakilci jihar a wajen aikin Makka. In kana hulda da jama’a ya kamata ka san ko su waye dan akwai ‘yan 419 da sauransu, sai suka ba ni adireshinsu na Abuja, a lokacin da na tafi hukumar alhazai ta Abuja, sai aka sa ni cikin kwamitin alhazai na fadar shugaban kasa, na kuma samu amincewar hukumar radio ta jiha a kan in tafi in yi aikin. “Na yi wannan aikin ne a shekarar farko ta aikin AMIRUL-hajj na mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar da shugaban kasar lokacin Olusegun Obasanjo ya nada shi Amirul-hajj na shekarar 2006-2007. Shugabanmu a lokacin shi ne Umar Bala, shugaban hukumar alhazai ta jihar Kano na yanzu, da Garba Danbatta, da Haruna Aliyu Hadeja, da Abdullahi Musa Suleja NTA, da Aliyu Abubakar wanda ya wakilci jaridar Dailytrust wanda yanzu yana aiki da NNPC a bangaren ‘yan jaridun ke nan. Babbar nasarar da zan ce na samu ita ce sauke farali da na yi, tun da ban taba tunanin zan yi aikin hajji ba amma albarkacin aikin jarida na sauke farali a tawagar mai alfarma sarkin Musulmi. Na biyu kuma na yi aure da ‘ya’ya kuma alfarmar Manzon Allah da wannan aikin sunana ya fita, dan yanzu a zagayen jihar nan ba sai na maimaita sunana ba. Ina kira da babban murya ga masu tasowa, su sani aikin jarida dama ce ba fifiko ba ne, dan haka idan ka samu dama ka jawo tsoffin hannu kusa da kai dan yin shawara, Hausawa na cewa hannu daya ba ya daukar jimka, kuma a cire kwadayi da hangen samun wani abu, domin kowa rabonshi yake ci. Na uku ka zama jajirtacce mai kwazo marar nauyin jiki, idan ka bi wadannan shawarwarin duk abin da kake a aikin jarida za ka same shi.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai