Hukumar NIS Ta Cafke Gungun Masu Fataucin Mutane A Katsina — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Hukumar NIS Ta Cafke Gungun Masu Fataucin Mutane A Katsina

Published

on


Hukumar shige da fice da ke shiyyar Jihar Katsina, ta bayyana cewa daga watan Janairu zuwa yanzu ta sami nasarar ceto mutanan da aka yi yunkurin safararsu zuwa wajen kasar nan su 38, inda kuma ta yi nasarar cafke gungun dillalan muguwar sana’ar a jihar.

Kwanturolan hukumar na Jihar, Mista Ajisafe Joshua, ya bayyana hakan ga manema labarai a lokacin da yake nuna masu wasu mutanen da suka ceto daga dillalan safarar mutanen su tara a shalkwatar hukumar da ke Katsina.

Ya bayyana sunayen mutanan da suka ceto kamar haka, Obike Blessing, Joshua Adewolu, Bukola Femi Emmanuel, Ogu Prosfer, Ebeze Doris, Olajide Sunday Olakunle, Rotimi Olufemi, Chinedu Micheal, Musagwo Farida, wadanda ya ce duk suna a tsakankanin shekaru 21 zuwa 40 ne.

Mista Ajisafe ya ce, uku daga cikin dillalan na safarar mutanan daga Jihar Ogun suka fito, sauran dillalan kuma sun fito ne daga Jihohin Abiya, Oyo, Imo, Edo, Osun da Jihar Enugu.

Ya kuma ce a daidai wurin duba ababen hawa na garin Caranci ne suka samu nasarar damke dillalan safarar mutanan.

“Daga Legas ne suka taso da nufin bi ta Nijar inda suke nufin samun kafar izinin shallawa Amerika, daga Ofishin Jakadancin na Amerika da ke a can Niamey ta Nijar din. wanda wani dillalin da suke tare da shi mai zama a can Niamey din mai suna, Balogun Taiwo,  yake kokarin shirya masu bizar shiga Amurukan.

A cewar sa, za su hannanta mutanan ne ga shalkwatarsu da ke Abuja domin ci gaba da gudanar da bincike.

Sai dai ya yi kira ga al’umma da su taimaka ma hukumar na su da bayanai masu amfani kan munanan ayyukan na masu fasakwarin bil-adaman da ma masu cin zarafin yara kanana a ko’ina suke a cikin jihar.

A halin da ake ciki kuma, jami’in yada labaran Hukumar shige da ficen ta kasa, DCI Sunday James ya fitar da wata sanarwa da ta ce hukumar tana farin ciki bisa ci gaban da ta ke samu wanda a karkashin kulawarta ne rundunar da ke duba kan iyakoki ta tashi tsaye a kan aikin nata na yaki da masu safarar mutane da kuma masu cin zarafin yara kanana gami da masu yin fasa kwarin ‘yan gudun hijira.

“Jami’anmu da ke kan iyakan Charanci, ta Jihar Katsina, sun sake yin wani wawan kamun, inda suka nu na cewa, in har mun toshe kofar da muggan mutanan kan bi wajen aiwatar da muguwar sana’ar na su, sai su sake bulla wata kofar, kamar yadda dai ya faru a kwanan nan, inda jami’an namu suka yi kame-kame da daman gaske a Jihohin Neja, Nasarawa, Seme-Legas, Oyo, Edo da Jihar Katsina. Wanda hakan ke nuna sabbin dubarun da hukumar tamu ta fito da su suna haifar da da mai ido, ta hanyar kame-kamen da muka yi masu yawa”, in ji sanarwar.

Jami’in yada labaran ya kuma bayyana cewa matsalar safarar mutane da fasa kwaurin ‘yan gudun hijira, abu ne da ke farawa daga ‘yan ku ci, ku bamu na nan cikin gida, wadanda suke hannanta mutanan da suka kama ga shahararrun abokanan burminsu da ke wajen kasar nan a kan iyaka.

“Ayyukan mabarnata wajibi ne a fara yakarsu tun daga tushensu, da matsugunnan da ake tsugunar da su har ya zuwa ainihin kasashen da ake kaisu, domin a bata duk wani shiri na su, a rika dirar masu ba kakkautawa kuma gabakidaya domin samun natijan abin a dukkanin kasashen da lamarin ke ci ma tuwo a kwarya, a samar da kan iyakokin da ke da cikakken tsaro”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

 

Advertisement
Click to comment

labarai