Rikicin Makiyaya Da Manoma Ya Yi Sanadin Kashe Shanu 38 A Riyom — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Rikicin Makiyaya Da Manoma Ya Yi Sanadin Kashe Shanu 38 A Riyom

Published

on


Kimanin shanu 38, ne ake zargin ‘yan kabilar Birom, sun kashe wa Fulani Makiya a kauyen Tanjol da ke cikin karamar hukumar Riyom, a wani sabon hari da aka ce matasan Birom sun kai a farkon makon nan.

Shugaban matasa na kungiyar Fulani makiya’ya na Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria [MACBAN], reshen jihar Filato, Ibrahim Yuusuf, ya shaidawa manema labarai a Jos fadar gwamantin jihar cewar matasan Birom dauke da muggan makamai sun farma rugarsu suna harbin kan mai uwa da wabi, inda suka yi ta harbin shanun ba sassautawa suka kashe talatin da takwas suka kuma raunata masu yawa.

Ya kara da cewar bayan sun kai rahota wa jami’an tsaro ne aka hadasu da wadansu jami’an tsaro na soja inda suka tarad da wadansu shanun guda goma shabiyar da suka harba da bindiga  sun sami mummunan raun,i sai suka umarci jami’an tsaro da a yanka su amma duk da ganin jami’an tsaro din matasan Birom  sun  sake bude masu wuta.

Da yake magana akan kai harin Jami’in watsa labarai da sadarwa na rundunar tsaro ta Operation Safe Haben, Major Adam Umar, ya tabbatar da aukuwar al’amarin, amma bai kididdige ko shanu nawa ne ba ‘yan kabilar Birom suka kashe.

A wata sabuwa kuma  makamanciyar wannan ,ita ma majalisar Dokoki ta Jihar Filato, ta nuna matukar damuwarta bisa abin da yake haifar da irin tashe tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma a kananan hukumomin Barakin Ladi, Riyom da Bassa dake cikin jihar.

Shugaban Majalisar Dokoki na jihar Hon. Peter Azi, ya umarci ‘yan kwamitin lura da tsaro da kwadago, na majalisar da su hada kai da jami’an tsaro da kungiyoyi don gano musabbabin tashe tashen hankula irin wadannan.

Da yake maida jawabi akan maganar rikicin makiyaya da manoma da dan majalisar Dokoki na jihar daga yankin  karamar hukumar Barakin Ladi, Hon. Gyandeng, ya gabatar wa majalisar tun farko,  wanda ya ce, ,makonni masu yawa da suka gabata yankin Barakin Ladi ya zama fagen daga inda a sanadiyar haka ne, rayukan mutane da dama sun halaka.

Advertisement
Click to comment

labarai