Fahimta Fuska — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Fahimta Fuska

Published

on


Assalamu alaikum. Malam, akwai matata da muka rabu da ita bayan na yi mata saki biyu,

yanzu ta yi aure har sun rabu da mijin. Idan na dawo da ita wancan saki biyun yana nan ko tunda ta yi aure ya rushe?

Akwai Malaman da suke ganin bai rushe ba, amma sakamakon ganin a duk lokacin da mutum ya yi ganganci ko ya yi kuskure ya saki matarsa sau daya, to ko shakka babu sai ya yi saki na biyu. Kazalika, galibi idan ma’aurata saki ya shiga tsakanin su suka sake dawowa a karo na biyu, sakewarsu da mu’amalarsu ba ta cika komawa kamar ta farko ba saboda yi wa kansu dameji da suka yi.

Saboda haka, a nan kamata ya yi a yi muku fatawa irin wadda Imamu Shafi’i ya yi cewa, idan aka yi wa mace saki daya ko biyu bayan ta yi aure a wani wuri, wannan sakin da aka yi mata ya rushe. A takaice dai wannan saki biyun da ka yi mata tunda dai har ta sake yin wani auren ya rushe kamar yadda Imamuna Shafi’i ya fitar da fatawa don ku samu saukin rayuwa.

Assalamu alaikum Malam. Don Allah ko akwai wata Sura ko Aya da idan mutum yana karantawa babu shi babu talauci har abada?

Ko shakka babu duk wanda ka ga ya zama talaka shi ya so kuma shi ya ga dama, na biyu kuma babu wata Aya ko Sura da mutum zai karanta ta yi masa maganin talauci ko da Izawaka da ake cewa a karanta, ba ana cewa a karanta don ta yi maka maganin talauci ba ne, a’a tana taimakawa wajen karin samun albarka ne amma dole sai da asali. Babu yadda za a yi mutum ya yi girbi a gonarsa ba tare da ya yi shuka ba, kamar yadda babu yadda za a yi mutum ya yi shuka bai sawa gonar taki ba, bai cire ciyawa ba, bai yi bar ruwa ba da sauran su ya kuma samu amfanin gona.

Haka shi ma arziki yake, wato shi arziki hanyoyi ne guda uku: ko dai ka sha wahala ka samu, ko wani ya ba ka ko kuma ka samu wata hanya da za ta rika kawo maka kudin fiye da bukatunka. Duk da dai cewa arziki da talauci yin Allah ne, amma fa ba na kaddarar cewa dole ka zama talaka ko mai kudi ba, a’a Allah Ya yi duniya don mutum biyu ne, mai kudi da talaka amma fa ba tare da an ayyana mai kudi da talakan nan ba, an ajiye talauci, an ajiye arziki wanda duk ya yi kokari ya zabi daya zai tafi a kan sa. Ala ayyu halin, duk wanda ka ga ya zama talaka shi ya ga dama, sannan babu wata Aya da mutum zai karanta ta yi masa maganin talauci.

Haka zalika, koda addu’o’i da Annabi (SAW) ya koyar, duk wadanda suka karanta suka samu wadata suna da sana’ar yi ingantacciya, sannan a lokacin da aka ba su addu’ar suna cikin matsi akwai kuma abinda zai taimake su su samu wannan kudi, kamar mara lafiya ne, da zarar an ce mutum yana da ciwon Tibi ko tarin Fuka, dole ne duk inda ya kai da shan magungunan wannan tari sai kuma likita y ace da shi ya rika hadawa da abincin mai gina jiki, don ba zai yiwu shan magani kadai ya warkar da mutum ba alhali jikinsa ba shi da matallafi, shi yasa masu ciwon HIB ke shan matukar wahala saboda jikinsu ba shi da wannan matallafin da zai rika tallafawa jikinsu, ma’ana garkuwar jikin ta karye baki dayanta dole kuma sai an dawo da ita.

Kowane mara lafiya zai iya samun sauki ne idan jikinsa akwai wannan garkuwa  da za ta taimaki maganin da zai sha saboda kowane magani na mutum, a jikinsa yake, maganin da mutum zai sha da abincin da zai ci su karfafar jikinsa suke yi. A takaice dai arziki yin Allah ne wannan ko shakka babu, amma ba zai yiwu ka same shi ba sai ta hanyar ko dai ka nema ko a baka ko kuma ka gada duk da cewa, kyauta da gado ba sa sanya mutum ya zama mai kudi, don sau tari ba su ma da albarka, idan ka ga sun yi albarka to dama can kai ma kana da naka ko kuma a lokacin da ka same su ka bi ka’ida ko kuma ka tsaya a kan neman kudi fafur.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!