Kungiyar ‘Water Aid’ Ta Nemi Taimakon ‘Yan Jarida — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Kungiyar ‘Water Aid’ Ta Nemi Taimakon ‘Yan Jarida

Published

on


Kungiyar Water Aid mai rajin samar da tsabtataccen ruwan sha da muhalli ta nemi taimakon ‘yan jarida game da wayar da kan jama’a musamman mazauna karkara domin inganta tsabtar muhalli da ruwan sha saboda a samu ingancin kiwon lafiya da kuma rage yaduwar cututtukan da ake samu ta hanyar gurbataccen ruwan sha ko rashin ingantaccen muhalli.

Kungiyar ‘yan jaridu mai ruhoto kan lamurran da suka shafi tsabtar ruwa da muhalli wato Wash Media Network ita ne ta yi wannan kira a Bauchi  a yayin taron manema labarai da suka suka kira a masaukin baki na Command Guest da ke Bauchi, inda suka ja hankalin kafofin watsa labarai da su himmatu wajen wayar da kan mutane da gwamnati don a

samar da ci gaba a fannin tsabtar mushalli da kuma samar da ruwan sha wanda zai taimaka wajen inganta rayuwar mutane.

Shugaban kungiyar ‘yan jaridun ta Wash Media Network Mista Wale Elekolusi shi ne ya yi wannana kira lokacin da ya ke ganawa da ‘yan jarida masu ruwa da tsaki kan aikin wayar da kan jama’a game da

inganta ruwan sha da tsabtar muhalli. Inda cikin jawabansa ya bayyana cewa wannan kungiya tana aiki da ‘yan jaridun Radiyo da talabijin da jaridun takardu don isar da sakon wayar da kan jama’a musamman mazauna yankunan karkara game da tsabtar ruwa da muhalli. Ya ce kungiyar Water Aid mai zaman kanta wacce ke samun tallafin wasu kasashe a duniya ita ne ta yi musu rijista da gwamnati  don a kara yawan ilmantar da jama’a da ake yia jihohi takwas da suke aiki wadanda suka kunshi Filato da Binuwai da Ekiti da Lagos da Bauchi da Abuja da Enugu da Jigawa yadda a kowace Jiha akwai wannan kungiya.

Kadan daga cikin ayyukan kungiyar ta wayar da kai shi ne halartar tarukan tsabtar muhalli na karshen wata da yin bitar halin da ake ciki game da tsabtar ruwa da muhalli tare da lura da irin taimakon da gwamnati ke yi da kuma irin kurar da mutane ke da ita game da wannan aiki.  A saboda haka suke shirya taron bita ga ‘yan jaridu kamar yadda tsarin mulkin su ya tanada don a kara zaburar da su game da yadda za su rika bin diddigin labaran da suka shafi tsabtar muhalli da samar da rowan sha mai kyau.

Wale Elekolusi ya kara da cewa kungiyar Water Aid ta fara aiki a shekarar 1996 kan wannan manufa  kuma Jihar Bauchi na cikin manyan wuraren da suke gudanar da aiki wa mutane yadda suke gudanar da wani babban aiki da bakunan  kasar Hong Kong da Shangai China  suke daukar nauyi, don haka ake da bukatar inganta wayar da kan jama’a game da wanka da wanki da wanke hannu da tsabtace muhalli tare da tabbatar da an samu ruwan sha mai tsabta a dukkan kananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi, saboda an tabbatar da cewa kashi 33 cikin dari na cututtukan da ake samu suna samo asali ne daga ruwan sha ko a sakamakon rashin magewayi mai kyau yadda mutane ke bayan gida barkate wanda ke zama musabbabin watsuwar kwayoyin cuta a ciki da wajen muhallan su.

Don haka yana daga cikin aikin wannan kungiya wyar da kan mutane ta kafafen labarai don su dauki gina magewayi da muhimmanci saboda shi ne zai taimaki kowa ya ji dadin muhallin da ya ke zaune a ciki, tare kuma

da samar da hanyar ruwan sha mai tsabta don amfanin yau da kullum.

Yadda ya bayar da misali ga ko bakunta mutum ya je idan an bashi daki abu na gaba da zai nema shi ne magewayi saboda muhimmancin sa ga dan adam. Don haka wannan kungiya ta Water Aid ke kashe mukudan daloli don gina magewayi a cikin garuruwa da makarantu ko kasuwanni da tashoshin mota, saboda a kare yaduwar cututtuka irin su kwalara da maleriya wadanda tushen su shi ne rashin ruwan sha mai tsabta ko rashin tsabtar muhalli Don haka ya ce kafafen labarai suna da muhimmanci wajen dagawa da nakasawa don haka suke son a tallafa don gwamnati ta ji manufar su kan wannan aiki don a ceci rayuwakan mutane. Inda ya kara da cewa  suna fiskantar matsala idan sun nemi tallafin hadin guiwa da gwamnati ko neman goyon baya game da gudanar da ayyuka amma akan yi dogon turanci da bata lokaci kan abubuwa masu muhimmanci da suke bukatar gaggawa domin amfanin mutane. Don haka ya kwadaitar da mutane da su rika aika koken su akai akai ga gwamnati don ta inganta musu muhalli da samar da ruwan sha, hakan shi ne zai taimaka su samu ci gaba a wannan aiki cikin gaggawa don a kare rayukan mutane daga kamuwa da irin wadannan cututtuka da idan an je asibiti sune suka fi kashewa da wahalar da mutane irin su maleriya da bakon dauro da kwalara da sauran su.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!