Kungiyar  ‘Yan kasuwa Za Ta Goya Wa Buhari Baya A Zave Mai Zuwa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Kungiyar  ‘Yan kasuwa Za Ta Goya Wa Buhari Baya A Zave Mai Zuwa

Published

on


Kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa ta bayyana ma tsayinta na cewa, a zave mai zuwa za ta goya wa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya domin ganin ya zama shugaban kasa karo na biyu, a karkashin mulkin farar hula.

Shugaban kungiyar na kasa, Dakta Bature Abdul’aziz ne ya bayyana haka ga manema labarai a garin Kano. Haka kuma shugaban ya bayyana cewa, kungiyar ta su na da dalilai masu karfi da suka sa su yanke wannan shawara.

Ya ce, daga cikin dalilan nasu akwai samun tsaro. Kamar yadda ya ce al’amarin tsaro abu ne wanda yake da matukar muhimmanci a rayuwar al’umma. Domin kuwa duk wani abu da za a yi sai an samu zaman lafiya zai tabbata. Rashin samun zaman lafiya a kasa na sa komai ya rikirkice.

Dakta ya waiga baya wanda ya ce kowa ya san yanayin da muka fito daga waccan gwamnati, wanda muka tsinci kanmu a cikin halin rashin aminci da junanmu. Duk inda aka ga dayanmu  ba mai yarda da wani.

Haka kuma, mun san lokacin wurin ibadojinmu inda nan ne za ka je ka samu nutsuwa domin bautawa Allah, amma sai da aka mayar da wuraren ibadunmu wajen fargaba, ya zama duk lokacin da mutum ke yin ibada ba shi da cikakkiyar nutsuwa, saboda bai san me zai biyo baya ba.

Ta kai ga babu aminci a asibiti ballantana a kasuwa ko tashar mota dukkanain wadannan wurare da na lissafa da ma wadanda ban Ambato ba, an kashe mutanen da ba za a iya gane yawansu ba , an kuma yi asarar dukiyar da ba za iya lissafa ta ba.

Saboda haka cikin rahamar Allah ya kawo mana gwarzon shugabn kasa Muhammadu Buhari, a yanzu hakan wannan fargabar ta kau daga cikin zukatan al’umma. Jama’a sun dawo cikin hayyacinsu. Dalibai na ta karatu manomna na yin noma mu kuma ‘yan kasuwa muna ci gaba da kasuwancinmu.

Saboda haka babban fatanmu shi al’amura ci gaba da gyaruwa kamar yadda aka fara a halin yanzu.  Wannan gagarumar gudummawar da muka samu a wannan kasa Allah ne ya ji tausayinmu ya sa muka zavi Buhari ya zama shugaban kasa.  Kuma Allah ya ba shi ikon aiwatar da kyawawan manufofinsa.

Saboda haka ga shi yanzu wa’adinsa na farko na neman karewa, shawara a nan ita ce kamar yadda kowane dan Nijeriya zai iya zama shaida a kan ci gaban da aka samu a wannan gwamnati, ya kamata mu yi wa kanmu kiyamul laili mu sake zaven Buhari domin ya ci gaba da farfado da kasar nan daga cikin suman da ta yi na tsawon shekaru.

Da ya juya kan batun samun walwala da ‘yanci da ‘yan Nijeriya ke yi a karkashin wannan ya ce, a baya ba tava samun irin wannan ‘yancin ba na fadar albarkacin baki, a matsayin damar dan kasa a mulkin dikmokaradiyya.

Ya ce saken ma da aka yi har wasu mutanen ke neman wuce gona da iri. A wannan gwamnati ne mutum ke sukarta kai tsaye ya zauna ba tare da wata barazana ba, saboda sakarwa mutane mara domin su aiwatar da ‘yancinsu na dimokaradiyya.

Dakta ya ci gaba da bayyana cewa, sanin kowane cewa, wannan gwamnati ta daira damarar farfado da harkokin noma yadda zai yi daraja kamar sauran sana’o’i, yanzu haka dukkan dan nijeriya zai zama shaida ganin yadda aka samu ci gaba a fannin noma. Yadda yanzu manomi ke alfahar da cewa shi manomi ne dimin yana da sana’ar kowa ke sha’awar yinta, wanda a baya ba haka abin yake ba. Saboda haka kokarin wannan gwamnati a fannin bunkasa nona ya ci nasara matuka.

Saboda haka wadannan su ne abubuwan da ya kamata a ce mutane ke kula da su wajen zaven shugabanni. Ya kamata al’umma su dawo cikin hayyacinsu su dubi baya, watau irin halin da kasar nan ta fito daha cikinsa da kuma halin da muke a yanzu. Wannan ya isa mu kara godewa Allah kuma mu ci gaba da yaba kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari, mu ba shi cikakken goyon baya yadda zai ci gaba da samun nasarar aiwatar da kyawawan manufofinsa wadanda za su amfani al’umma da kasa baki daya.

Bisa la’akar da ire-iren wadannan ci gaban da aka samu ne a wannan kasa kungiyarmu ta ‘yan kasuwa ta kasa ta yanke shawarar goya wa Muhammadu Buhari baya a zave mai zuwa. Kugiyar ‘yan kasuwa ta kasa, kungiya ce da ta hada dukkan kabilun kasar nan da kuma dukkan wa vangare da ke fadin kasarnar. Saboda haka bisa amincewa ‘yan kasuwarmu da ke fadin kasar nan da ke da harshe daban-daban da addini daban-daban muka amince da cewa, za  mu bayar da cukakkiyar gudummawa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari don ganin cewa, ya sake samu nasarar ci gaba da zama shugaban kasa karo na biyu a wannan kasa, wannan take bukatar jajirtattun mutane irinsa.

Haka kuma kamar yadda kowa ya sani da Allah ya jarrabe mu da cewa wani ne ya ci gaba da mulkin gasar nan to daba mu san halin da za mu kasance ba. Amma bisa dukkanin al’amu da abin bai yi kyau ba.Domin kuwa ko ba komai mun ga irin yadda ake jefa bama-bamai a dukkan wuraren taruwar al’umma, wanda kuma ke yi musu sanadiyyar mutuwar kare-dangi. Kawo karshen dasa irin wadannan bama-bamai ya isa mu godewa Allah kuma mu yaba da kokarin wannan gwamnati.

Saboda haka muke shawartar ‘yan Nijeriya da su daure su ci gaba da bai wa wannan gwamnati goyon baya, sannan kuma su mara wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a zave mai zuwa, domin ya karasa dora kasar nan a kan kyakkyawan harsashe.

Dakta Baure ya yaba wa mambobin kungiyar ta su bisa hadin kan da suke da shi na tafiya tare a dukkan al’amura duk da cewa suna da bambancin harshe da yanki da kuma kabila. Bisa haka ne ma ya nuna cewa sauran al’umma za su yi koyi da wannan kungiya tasu da an kara samun zaman lafiya a kasa da taimakon juna. Saboda haka ya ce dukkan ‘yan kasuwarsu da ke cikin wannan kungiya sun amince da cewa, za su mara wa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a zave mai mai zuwa.

A karshe ya yi kira dab bar murya ga daukacin al’ummar kasar nan da su bi sahun wannan kungiya ta su wajen marawa shugaba Buhari baya a zaven da za ayi na gaba.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!