Kuri’arka ‘Yancinka — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

Kuri’arka ‘Yancinka

Published

on


Kasancewar a halin yanzu kullum kwanaki sai kara karato wa suke yi na zabuka musamman zaben shugaban kasa da gwamnoni da kuma ‘yan majalisa. Wannan ta sa masu fada a ji a cikin al’umma suka tashi tsaye wajen fadakar da jama’a kan muhimmancin mallakar katin kuri’a, wanda da shi ne za ya dukkan wadannan zabuka.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ma ba a bar shi a baya ba, wajen shiga sahun masu irin wannan kira, sannan kuma ya bukaci dukkan wanda ya karbi wannan kuri’a ya tabbatar da ya zabi wanda yake da tabbas a kansa, wanda yake ganin zai kawo ci gaba kasa da na al’umma baki daya. Haka malaman addini a wuraren wa’azozin da wurin taruwar al’umma sun dage wajen fadakar da al’umma kan nuna musu muhimmancin mallakar wannan kati na kuri’a.

Mallakar katin kuri’a kamar yadda kowa ya sani ita ce hanya daya tilo da dan kasa ke iya samun damar yin zabe, wanda zai zabi wanda yake so, kuma da wannan katin ne ake kayar da wanda ba a so. Saboda haka ya zama dole ga duk wanda ke bukatar zabar wanda yake ganin shi ne mafita wajen ci gaban al’umma da raya kasa da ya  mallaki wannan kati na kuri’a.

Saboda haka a kowane matsayi da al’umma ke son zabar wanda zai wakilci ce su, dole sai sun mallaki katin kuri’a.

Tabbas kuri’a ‘yanci ne na mai yin zabe domin ita za ta ba shi dama ko tabbatar da ‘yancin da tsarin mulki ya yi masa tanaji na ya zaba ko a zabe shi a kowane matsayi matukar ya cika sharudan yin hakan.

Don haka, wannan babban kalubale ne ga al’umma musamman wadanda sakamakon wani abu da ya faru tsakaninsu da wakilan da suka zaba na rashin gudanar da abin da ya kamata su yi, ya sa suka ji haushi har ma suka fara tunanin ba za su sake yin zabe ba.

Wannan babban kuskure da bai kamata al’umma su sake su afka a ciki ba. Domin kuwa matukar sun afka cikinsa, to fa a bin nan da ba sa so shi zai sake faruwa, ta yiwu ma ya fi na baya muni.

Saboda babbar hanyar huce takaici ita ce a mallaki kuri’a yadda duk wanda ya yi wa al’ummar da suka zabe shi ba daidai ba, in ya dawo su juya masa baya.

Juya bayan nan kuma ba zai yiwu ba sai ta hanyar mallakar katin kuri’a, wanda da ita ne za su juya duk wanda ya juya musu baya. Saboda haka ya zama wajibi ga duk wanda ya isa yin zabe namiji ko mace da ya tabbatar da ya mallaki katin zabe.

Kuri’arka ‘yancinka, wannan batu tabbas haka yake, Saboda haka duka wanda ke bukatar samun ‘yanci na ya zabi wanda yake so dole sai ya mallaki kuri’a.

Bayan mallakar kuri’ar kuma wani abu da al’umma ya kamata su kiyaye domin su tabbatar sun amfana da damar da suke da ita ta zabar wanda suke so, shi ne su guji yaudarar da wasu ‘yan siya za su iya yi musu  ta hanyar ba su, kudi domin su zabe su ko su zabi wadanda suke goya wa baya. Matukar al’umma ta fada wannan tarkon to tamkar sayar da ‘yancin kai ne. Duk kuwa wanda ya sayar da ‘yancin kansa karshen al’amari shi ne ya zama bawa.

Idan al’umma suka tsinci kansu a cikin irin wannan halin abu ne wanda ba zai haifar musu da da mai ido ba. Saboda haka ya zama wajibi gare su da su farka, yadda za su tunkari wannan babban kalubale da ke gabansu na zabar wanda ya cancanta, wanda suke ganin shi zai kare mutuncinsu, ya kuma kawo ci gaban yankinsu, in kuma a matakin kasa ne ya kawo ci gaban kasa.

Saboda haka ya kamata al’umma su gane cewa, karbar katin kuri’a na da matukar muhimanci wajen bayar da ‘yancin zabar wanda ake so da kawar da wanda ba a so.

Advertisement
Click to comment

labarai