Mataimakain Shugaban Kasa Ya Tsallake Rijiya Da Baya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Mataimakain Shugaban Kasa Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Published

on


Ranar Alhamis da ta wuce ne, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi

Osinbajo ya tsallake rijiya da baya,  yayin da jirgi mai saukar ungulu da yake ciki ya fara fitar da  hayaki.Hakan ya sanya aka tilastawa jirgin sauka a garin  Abuja kuma jirgin ya kai Yemi Osibanjo ne taro a kwalejin hukumar kwastam da ke Gwagwalada a cikin garin Abuja.

Osinbajo ya je kwalejin ne don halartar taron yaye manyan jami’an hukumar na wannan shekarar kuma dama jirgin ne ya kai Mataimakin wurin taron.

An ruwaito cewar, jirgin bai riga ya yi nisa da kasa ba, inda aka tilasata wa jirgin sauka bayan da ya fara fitar da hayaki, inda hakan ya sanya aka dauke mataimakin daga wurin ya tafi ta hanya

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!