Nau’o’i Da Salailan Fassara A Idon Masana Da Manazarta (6) — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

ADABI

Nau’o’i Da Salailan Fassara A Idon Masana Da Manazarta (6)

Published

on


Fassarar Maganar Hikima (Hausa Zuwa Ingilishi)

1a  Hangi nesa(yin tunani mai zurfi kafin a yanke hukunci) kamar a ce:

Shugaban ya yi hangen nesa da ya ba wa Sani shugabancin sakandire.

Kamar a ce:

The chaireman has chewed the cud in placing Sani as the principal of the srcondary school.

2a  A karya  a kan gaba (fada ko yin daidai) kamar a ce:

Daga zuwansa muka fahimci ko muka san zai karya a kan gaba.

2b   Hit the nail on head (said the right thing). Kamar a ce:

The moment he came we knew that he will hit the nail on the head.

3a  Satar fage (fara yin wani abu kafin a bayar da izini)

Kamar a ce:

Buba ya yi satar fage a gasar tseren da aka yi bara.

3b   Steal a march (on somebody)(gain an adbantage).

Kamar a ce:

Buba stole a march by beating the gun at the race last year.

4a  Tsallake rijiya da baya ko auna arziki(kai wa gaci da kyar).

Kamar a ce:

Fataken sun wuce ke nan sai ga ‘yan fashi. Lallai sun tsallake rijiya da baya ko sun auna arziki.

4b  To sail close to the wind (to land too dangerously near the  approbed limit). Kamar a ce:

The merchants passed immediately before the coming of robbers. They realy  sailed close to the wind.

5a   (yi) jifan gafiyar Baidu(biyu babu). Kamar a ce:

Ida ba ka yi takatsantasan ba, za ka yi jifan gafiyar baidu.

5b    Fall between two stool(fail to achibe either ambitions). Kamar a ce:

If you are not carefull you will falla between two stools.

Wadannan su ne misalai kadan da aka kawo karkashin wannan salo domin nuna dacewa da kuma ingancin yin amfani da maganar hikima wajen fassara maganar hikima, wato samar da abokan burmi tsakanin tushen fassara da kuma harshen fassara. To amma fa ya kamata a lura fa cewa, kasancewar kowane harshe na cin gashin kansa, nu ne kan cewa, ba kowace maganar hikima ce za ta samu abokin burmi ba, daga wani harshe zuwa wani, wata za ta iya samun takwara ammam wata ba za ta samu ba. Idan babu takwara, hanya ma fi sauki ita ce ya yi amfani da salon fassara mai ‘yanci. Saidai wurin da gezo yake yin saka shi ne, tilas dai mai fassara ya sani ko ya binciko ma’anar maganar hikimar a harshen da take kafin ya yi amfani da salon na fassara mai ‘yanci wajen ma’anar cikin harshen fassara.

Kammalawa

A wannan takarda an fayyace tsakanin nau’I da salailan fassara ta yin la’akari da yadda masana da manazarta suke kallonsu. An tattauna, tare da misalai a kan muhimmancin nau’in fassara da cikas din duk wanda yake da cikas. A ciki an yi hannunka mai sanda game da salailan fassarar da za kauracewa bisa dalilai. An kuma karfafa gwiwa game da salailan da suka fi dacewa don yin ingantacciyar fassara.

Allah ya kawo mu karshen wannan makala, wadda ta koyar da masu karatu dimbin ilimi a kan fassara, da fatan kuma ta amfar da masu karatu, shi kuma marucin kasidar Suleiman Sarbi muna yi masa fatan alheri bisa wannan ilimi da ya fito da shi, mu kuma muka yada domin amfanin al’umma.

Advertisement
Click to comment

labarai