Salo Dokin jigo: Tsokaci A Kan Wakar Kalubale Ta Akilu Aliyu (1) — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

ADABI

Salo Dokin jigo: Tsokaci A Kan Wakar Kalubale Ta Akilu Aliyu (1)

Published

on


Wannan ita ce  makalar da Dakata Salisu Garba Kargi shugaban Sashen Nazarin Harsuna Da Al’adun Afirka ya gabatar a cikin shahararren littafin nan na ‘Champion Of Hausa Cikin Hausa’ wanda Sashen Nazarin Harsuna Da Al’adun Afirka Na Jami’ar Ahmadu Bello Da ke Zariya ya wallafa domin karrama Shehin Malami Farfaesa Dalhatu Muhammad. Za kuma mu ci gaba da gutsuro muku wannan makala har karshenta. Muna kawo wadannan makaloli ne a wannan shafi saboda muhimmancin da kasidun ta fuskar ilimantar da jama’a.

Tsakure: Wannan makala mai taken ‘Salo  dokin jigo’ ta nazarci irin dimbin gudummawa da salo da ake bayarwa ne wajen isar da sako. Makalar ta mayar da hankali ne wajen nazartar salon almara da salon fassara kalmomin aikatau dan aji hudu da kuma irin yadda hakan ya yi tasiri a kan saukaka fahimtar jigon wannan waka. Byan haka kuma makalar ta gano cewa, lallai komai muhimmancin jigo, salo ne zai iya daukansa zuwa zukatan masu saurare ko karatu kuma ya bayyanar da kwarjini da armashin sakon a zukatansu. Domin haka, idan salo mai armashi ne, to,sako ma sai armashinsa ya bayyana, idan kuma ragon salo ne, to, komai muhimmancin jigo sai ya zama rago a cikin zukatan jama’a. wannan makala ta fahimci cewa zabin aikatau dan aji hudu da wannan fasihi ya yi domin sarrafawa cikin wannan waka, hakika, hakan ya yi tasiri kwarai wajen mayar da wakar mai armashi da karsashi, wanda kuma hakan ne ya sa wakar take burge jama’a kuma take jan hankalinsu.

Shimfida

Wannan waka ta kalubale shahararriya ce ainun a cikin wakokin wannan hazikin fasihi, Akilu Aliyu. Sannan kuma shahararriya ce a wajen Farfesa Dalhatu Muhammad musamman yadda ya kebeta da sharhi na musamman a cikin bincikensa na 1977, saboda sha’awarsa ga armashin salonta. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa aka zabeta domin kara fito da wani nau’in gwanintar da wannan fasihi ya sarrafa a cikinta, tare da kwadayin kara cusawa wannan Shaihin nazarin waka(wato, Dalhatu)sha’awarta da kuma debe masa kewa. Haka kuma bayan jkasancewarsa malami a gare ni, kuma ciakken jagora a fagen nazarin waka, musamman ta Akilu Aliyu, kuma shi ne dan kasa na farko day a zurfafa bincike da nazari a kan wannan fasihi, tun a shekarar 1977. Ana fatan wanna makalar ta zama mabubbugar farin ciki a gare shi, saboda ganin kwayar da ya shuka ta tsiro har kware labulen abin begensa.

Manufar Wakar Kalubale

Babbar manufar wannan mashahuriyar waka ta Akilu Aliyu kamar yadda Muhammad(1977:295 da 1978: ii) suka bayyana ita ce fadarkawa game da sha’anin ilimi. Wato, ka’idojinsa da falalarsa da kuma illoli da kaskancin da ke tattare da jahilci.

Manufar Wannan Makala

Muhimmin kudurin wannan makala shi ne, nazarin salo a matsayin ‘yancin zabin marubuci, tare da bayyana salon sarrafa aikatau dan aji hudu da Akilu Aliyu ya yi a cikin wannan waka tasa ta kalubale. Sannan kuma makalar ta kuduri aniyar fayyace irin tasirin  da wannan zabi nasa ya yi a kan wannan mashahuriyar waka da kuma masu saurare ko karatu.

Haka kuma  yana daga cikin kudurin wannan makala, yin dori a kan wancan nagartaccen sharhi da wannan zakakurin  Shaihin nazarin waka ya yi, a cikin bincikensa na 1977, a kan wannan waka. Bukatar wannan dori kuma ya taso ne saboda a tabbatar da abin da Muhammad 1977:295 ya bayyana shi a matsayin dunkulallun manufofin wannan waka cewa, lallai ilimi kogi ne. Sannan kuma makalar na da burin gwada cewa lallai aikin fasihai, irin su Akilu Aliyu sai dai a buncina, sannan a zurfafa bayani, amma ba dai akewaye aikinsu da wani sharhi kwaya daya ba. Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!