Dalilan Da Ya Sa Har Yanzu Ba Gama Fim Din Bilkisu Ba –Tudun Wada — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Dalilan Da Ya Sa Har Yanzu Ba Gama Fim Din Bilkisu Ba –Tudun Wada

Published

on


Tun a shekarar da ta gabata ne a ka fara aikin wani fim mai dogon zango (wato series) mai suna Bilkisu na kamfanin Amara Creatibe Studio, ‘series’ din da a ke ganin shi ne mafi girma da aka taba shiryawa a masana’antar finafinai ta Kannywood kuma fim din da ya tayar da kura tun daga lokacin da aka faa shirin aiki do kuwa an fara ne da samar da ’yan wasan da za su fito a fim din ta hanyar tara mutane a tantance su, inda aka zabo mutanen da ake ganin sun dade su taka rawa a fim din inda wannan ya tayar da kura tare da muhawara mai zafi a ciki Kannywood. Baya ga haka, tafiya aikin da aka yi garin Bauchi da iri dumbin jama’ar da fim din ya dauka tare da tsaown lokaci da aka shafe ana aikin shi ma ya zama abin magana, domin kuwa an shafe tsawon wata biyun cif ana aikin sai dai kuma aikin bai kammala ba har zuwa wannan lokacin.

Wannan ta sa LEADERSHIP A YAU LAHADI ta nemi jin ta bakin shugaban kamfanin Amara Creatibe Studio, UMAR SA’ID TUDUN WADA, wanda shi ne ya shirya fim din, don jin halin da fim din ya ke ciki a halin yanzu, kamar haka:

Me ya sa har yanzu fim din Bilkisu bai isa ga masu kallo ba?

To, a yanzu dai abi da zan iya ada maka shi ne, ba mu kammala ba har yanzu akwa ‘yan kananan abubuwan da suka rage. Kuma kamar yadda ka fada, wannan shi ne aro na farko don karamin kamfani kamar namu ya shirya fim mai dogon zango kuma fim ne da za a yi iamar shekara biyu ana yi, wanda za a yi Episode 108, kuma yadda muka tsara shi tun da abu ne sabo yawancin abubuwan da muka yi ba su samu a yadda muka tsaro ba. Domin har yanzu masana’antar nan ta Kannywood ba ta yi girman da ake bukata ba. Amma dai da hakan za a girma. Misali, yawancinjaruman da muka yi amfani da su, ba mu kadai muke iaki da su ba, don haka ba lokacinmu kdai suke da shi na aikin ba, saboda haka muna aikin wani ma zai zo yana bukatar aiki da su, don haka sai s tafi su yi aikin a wasu gurare. To haka aka yi kuma na biyu mun dauki abin da adi mun dauka da farawa za mu iya daukar kashi 26 a karon farko, amma dai ya yiwu mun yi akan, sai dai daga lokacin da muka tsara kasafin kudin zuwa lokaci da muka yi kashi 26 sai muka ga kudin kamar ya linka yadda muka kayyade za mu kashe. Don mu dauki lokac a kan wajen ma da za a yi fim din mai nisa, wanda idan ka kai mutane ba za ka sami rabuwar hankali ba. To Sai ya zama shi ma yan da tas amatsalar, sai ka kama musu otel, sai ka ba su abinci da wasu abubuwa. Sannan kuma mun tsara za mu yi kwana 40, amma sai da muka kwana 60 kuma a lokacin har bikin babbar Sallah ya shigo. Don haka sai ka kara kashe kudin da ba ka yi kasafi da shi ba. Saboda ka tara mutane ba su tafi gidajensu ba ka ga za ka samar musu da naman layyar da za su ci da wasu abubuwa. Wannan sun sa kudin da muka kashe sun haura yadda muka tsara. Amma dai yanzu fim din kawai sinasinai 7 suka rage, kuma su ma abu ne ya faru, wadanda ya kamata su yi abin a lokacin ba sa kusa sun tafi wani aikin, amma dai a yanzu duk mun kammala wannan kashi 26 dn sinasinai 7 din nan su suka rage mana, kuma an fara ace fim din. An ma yayyanka su kawai tacewa za a yi da kuma an kammala sinasinai 7 din da suka rage wanda muna sa ran a cikin wana biyu za a hada. Idan muka hada jarumanmu za mu je mu yi aikin. Sai da ya kamata mutane su sani, shi Bilkisu ba fim ba ne da za a gan shi a kasuwa ba, fim ne da za a yi yarjejeniya da wani gidan talabijin da su za su rinka nunawa. Kuma a yanzu haka akwai gidan talabijin din da muke magana da su, wasu ma suna ta iza mana wuta cewar mu suke jira. To amma dai abin da ya sa muke dauke lokaci don mu ne na farko da muka zo da irin wannan tsari, kuma idan muka kasa to za mu kashewa wadanda za su zo karfin gwiwa. Kuma idan muka samar da fim marar kyau da wanda ba zai ja hankali mutane ba to su kuma gidajen talabijin din za su ji tsoron karbar finafinai irin wadannan daga wajen mu. Don haka a matsayinmu na wadanda za su fara dole ne mu yi taka-tsantsan. Mu tabbatar da cewa mun fitar da fim in da masu gidajen talabijin din za su yi sha’awar karba, saboda ingancinsa.

 

To, daga yanzu zuwa wanne lokaci a ke sa ran za a je karashen wannan aikin?

A yanzu dai kamar yadda na fada maka muna jiran wasu jarumanmu ne da suka tafi yin wani aiki a was kamfanonin kuma ga shi an shiga azumi, amma dai da yardar Allah bayan slalah za a kammala. Kuma idan har mun cimma yarjejeniyar da muka fara ammalawa da gidajen talabijin ina tsammanin nan da kwata ta uku ko ta hudu na wannan shekarar za afara nuna fim din.

 

Da ya ke wannan shi ne karo na farko da ka yi irin wannan aiki na fim mai dogon zango, ko wane darasi ka samu?

To, mun yi finafinai a Amara, sai dai ba irin wannan mai dogon zango ba, don mu fi mayar da hankali kan tallace-tallace, amma dai babban darasin shi ne, gaskiya ya kamata duk wanda zai yi fim irin wannan to ya tanadi kudi kuma idan an samar da kudin an tsara kasafinsa to kada a yarda a kawo canji don kuwa darasin da muka samu in dai ba kudi ne da kai a ajiye ba, to kada ka dauki otal wajen ajiye ma’aikatanka, gara ka kama gida za ka sauke jarumanka da sauran ma’aikata. Idan kuma otal da ka kama, to ka tabatar ka tanadi kudin da za ka biya su a dunkule. Haka wajen abinci kodayake shi ba mu samu matsala sosai ba. Saboda mun saba da yadda ake tsara abinci. Wadanda muka yi aiki da su suna da wannan kwarewar. Sannan kuma ka tanad kudi da za ka biya jaruman da sauran ma’aikatan da suka yi maka aikin, duk da mun biya su, amma akwai inda muka samu dan tasgaro wato otal. Su kudinsu ba a dunkule muka ba su ba, duk dai mun biya. Don haka idan ba a kiyaye ba za a iya samun matsala irin wannan. Saboda haka idan ka fara aiki irin wannan ka tabbatar kudin da za ka yi amfani da shi yana hannu ko ba ma shi za ka ci to ka tabbata kudin ya zo hannunka kafin ka fara, domin idan aka samu wani dalili da aka tsayar da aikin, to tsada ce za ta karu, dk abin da ka kashe a baya sai ka za ka sake sabin kasafi. To, wadannan sune darussan da muka samu.

 

Ko mene ne sakonka na karshe?

To ni babban sakona shi ne, gaskiya ina godiya ga mutanen da suka yi aiki da mu sun nuna kwarewa kuma sun nuna hakuri da juriya. Su ma jaruman suna bukatar godiya saboda irin jajircewar da suka nuna. Ina fatan nan gaba idan muka zo da wani aikin idan muka bukace su za su zo don muna bukatar su zo din. Akwai abubuwa da dama da muka samu wajen tantane jaruman tun kafin a fara iakin wanda shi ma abu ne a muka zo da hsi sbao. Wasu sun samu shiga, wasu kuma ba su samu ba, don haka wadanda ba su samu ba su duaka haka Allah ya kaddara, kuma su sani duk lokacin da muka tashi yin fim nan gaba ba za mu manta da su ba, daman dai tsari biyu ne ko dai ka zabo da kanka ko kuma ka taro mutane ka tantance, wannan shi ne tsarin da masana’antar fim ta duniya ta yarda da shi, kuma mu abin d aya sa muka mayar da hankulanmu wajen tantancewa shi ne ta nan ne ake fitar da sabbin jarumai. Don haka ina godiya ga kowa kuma masu kallo su kara hakuri fim din Bilkisu yana nan ya kusa kammaluwa.

ce ma na gaba a al’amuranmu, amin.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!