Kudi Ruhin Aure (3) — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

HANGEN NESA

Kudi Ruhin Aure (3)

Published

on


Daya gada cikin abubuwan da mafiya yawan masu zaben abokan aure ba su sani ba shi ne, kudi ba sa iya biyan bukatun zuci! Yayin da muke tattaunawa ko yin tuntuntuni game da yadda muke so rayuwar aurenmu ta kasance, a kalla, kowanmu ba ya rasa lissafa abubuwa guda uku, yayin da wani yakan kai har abubuwa bakwai. Ya danganta dai da tsari da kuma yawan burin na kowane mutum. Amma abin mamaki shi ne, yayin da muka zo zabar abokin zaman sai mu dauki daya daga cikin ukun can, mu yi la’akari das hi, tare da watsi ko mantawa da ragowar biyun. Haka nan kuma masu duba abubuwan das u ka kai bakwai sukan zabi abubuwan biyu, idan har su ka ga alamunsu a tare da mutum, su manta da sauran abubuwa biyar da a baya su ka gama ayyana said a su ne rayuwar auren za ta kai ga zama cikakkiya. A mafi yawan lokaci kuma ba ma fahimtar ashe ma idanuwanmu ne su ka rufe, ba mu dubi yuyuwar samuwar mafiya yawan bukatun namu ba. Abin takaici ma kuma shi ne, abin ma da ya ja hankalinmun sai mu tarar kimarsa ba ta kai wadda muke kaddarawa ba.

Wannan muhimmin abu daya day a fi daukar mana hankali tare da sawa mu manta ko mu ki yin la’akari da sauran, shi ne kudi. Wato yayin da muka ga kudi a mafiya yawan lokaci sai lissafinmu ya sauya. Amma babbar matsalar da take tattare da kudi ita hana zuciya cikakken ‘yancin samun kulawa da soyayya. Wannan kuma bai tsaya ga jinsi guda ba. kodayake, ana iya cewa kamar ya fi kaiwa matukar takurawa ga mata.

A mafi yawan lokaci, Maza suna tsammanin yayin da su ka wadata iyalansu da dukkanin abubuwan bukatu na rayuwa, to ba su da wani bakin korafi kuma.” Kenan tunda komai kike bukata akwai shi a kusa da ke. In ma babu in kika ka yi magana za a nemo miki shi, komai tsadarsa, ai an kai makura wurin yi miki gata. Don haka duk wani korafi kuma da za ki yi daga baya, ya zama butulci kenan.

Haka kuma, sanannen abu ne cewa, kamar yadda kusan kowace mace, auren mai kudi take kallo a matsayin farin cikin rayuwar aure. Haka ma da yawan mazan suke ganin auren mace mai kudin ko ‘yar mai kudin shi ne abin da zai fi bayuwa ga samar da jin dadin raruwar auren. Sai dai kuma sau da dama, bayan sun tare a gidan auren suna fahimtar ashe dai wani katon gari su ka gina, wanda yake karkashin mulkin sarakuna biyu, masu daraja ta daya, kuma kowannensu mai cikakken iko.

Kodayake dai, da yawa suna ganin matan sun fi shiga damuwa idan ana maganar tataburza ko rashin samun cikar buri irin na kulawa a zaman.

Jamil da Jummai sun kasance cikin kangin talauci, lokaci mai tsayi bayan aurensu. Daga baya sai budi ya zo musu. Nan da nan kuma su ka yi arziki. Dukkannin bukatu na abubuwan more rayuwa suna samuwa. Amma tare da haka, abin da ya daure wa Jamil kai shi ne, kullum Jimmai a cikin korafi take!

A da can, yayin da suke cikin rashin wadata. Jamil yana iya fahimtar irin damuwar da take ciki, ta rashin samun sukuni da walwala da sauran abubuwa da za su ba ta damar more rayuwa. Saboda shi ma yana cikin irin yanayin. Kuma yana ganin dukkan kalubalen nasa ne. A matsayinsa na wanda dawainiyar gidan ta rataya a wuyansa. Don haka duk lokacin da ta yi wani korafi, shi ne zai zauna ya yi duk abin da ya san zai iya har sai ya kwantar mata da hankali. Amma a yanzu da suke da kudi, yana ganin ba ta da wani dalili na yin fushi kuma. Abin mamaki kuma, dukiyarsu tana kara bunkasa, rikici da damuwa a cikin zamantakewarsu ma suna kara ta’azzara!

Mata Masu Kudi Sun Fi Talakawan Cancantar Nuna Damuwa.

Dr. John Grya yana cewa: “Attajirin likitan kwakwalwa ne kadai zai iya fahimtar ainishin irin damuwar da mace attajira take ciki!” A tunanin mutane, musamman mijin matar, babu wani dalili da zai sa ta kasance cikin damuwa ko korafi game da zamantakewarta ta aure, kamar yadda sauran mata ke yi. Saboda ya girke mata kusan duk abubuwan da za ta iya bukata a rayuwa. Kuma yan aganin tunda ta san irin yanayin harkokinsa, ba wani dalili da zai sa ta kasa yi masa uzuri.

Bana mantawa, kwanakin baya, wata daga cikin matan manyan mutane a garin nan ta taba ce min. “Don Allah ka turo min duk tsofaffin rubuce-rubucen da ka yi a kan zamantakewa.” Na tura mata kusan duk wadanda da lalubo kuwa. Bayan kwana biyu sai ta ce da ni: “ Ka yi kokari matuka kuwa, ka taba bangarori da dama. Amma ni har yanzu ba ka taba bangaren abin da ya dame ni ba!”

A wancan lokaci na yi mamakinta, amma daga baya waccan maganar ta sa na fahimci abin da take nufi.

A tunanin mutane, matar da take da arziki ba ta kuma da wani bakin yin kuka, ko korafi ko ma wani dalilin yin fushi. Amma abin da ba a lura shi ne, kasancewarta mai kudi ko mai wadata ba ya canza ta daga ainishin dabi’arta ta mace. Ba Kuma ya dauke mata bukatu da al’adu irin na mata. Don haka mace mai tarin dukiya ma, kamar sauran mata, tana da waccan dabi’a ta suffantuwa da Igiyar-ruwa da muka tattauna a darasin da ya gabata wancan mako. Wato dai, tana iya kasancewa cikin farin ciki lokaci mai tsayi. A irin lokutan da igiyar ke yi tsiri sama. A Wannan lokaci za ta kasance mai yawan nuna so da faram-faram da mutane, da yawan kyauta. Amma kuma katsam wataran sai igiyar ta murda ta yi kasa. A lokacin ne za ta koma lissafin dukkan abubuwan da ta rasa a rayuwa. Musamman na kulawa daga mijinta. Har ma sai ta kalli wata daga ma’aikatanta wataran ta rika tunanin ina ma dai ita ce kamar ta!

A irin wannan lokaci sau da yawa takan dauki tsawon lokaci fiye da ‘yar’uwarta talaka, wadda mijinta ke kusa da ita a lokuta da dama. Saboda ita nata mijin watakila ba zai sami lokacin da zai saurari batutuwanta ya fuskance ta da wuri ba. Sakamakon karancin lokaci da yake da shi.

Wani abu muhimmi kuma da akan kuskure a irin wannan lokaci shi ne yadda ma za a fahimci menene ainishin bukatar da take da ita. Shin me ma take so a yi mata? Ko me ya kamata a yi mata in ta shiga damuwa? Kai ture batun mijin, a gida ma tsakanin iyayenta da dangi, korafinta bai cika samun tagomashin kulawa da rarrashi da tausayi ba. domin da zarar ta nuna damuwarta za a ce “Ked a Allah Ya taimaka, kina zaune asirinki a rufe, kowa yana sha’awarki.” Abin da mutanen bas u sani bas hi ne, ita ma tana sha’awar wadanda suke sha’awarta din.

Abin mamaki ne a ce mutane sun manta cewa, kowace mace tana bukatar mijinta ya mu’amulancewa ta da irin yarenta na soyayya. Wanda a wurinsa kadai za ta iya samunsa.

 

Advertisement
Click to comment

labarai