Ba Zan Yafe Wa Ramos Ba, Inji Salah — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Ba Zan Yafe Wa Ramos Ba, Inji Salah

Published

on


Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liberpool, Muhammad Salah ya bayyana cewa bazai taba yafewa dan wasan baya na Real Madrid ba Sergio Ramos bisa raunin dayaji masa a wasan karshe da suka buga a watan daya gabata na zakarun turai.

Wannan ne karo na farko da Salah yayi Magana akan ciwon dayaji tun lokacin da abin yafaru duk da cewa Ramos din ya tura masa sako inda yake masa fatan warkewa da wuri domin buga gasar cin kofin duniya.

A wasan dai an kuma zargi Ramos da buge mai tsaron ragar Liberpool akansa wanda hakan yasa mai tsaron ragar yayi wasu kura kurai guda biyu kuma aka zura musu kwallo a raga a wasan da Real Madrid tasamu  nasara daci 3-1.

Salah ya ce abin dariya ne Ramos yafito duniya ya ce wai nine nayi masa mugunta domin babu wanda zai yadda da wannan karyar tasa.

Yaci gaba da cewa tabbas Ramos ya tura masa ta sako ta waya amma bai mayar masa da amsa ba kuma bai gaya masa cewa komai ya wuce ba kawai dai ya karanta sakon ne kamar yadda ya turo da abinsa.

Salah yakara da cewa duk mutumin daya saka kuka ko kuma ya saka dariya zai iya cewa yayi maka komai koda ace karya yake saboda anga abinda yasaka kuma ba hurumin Ramos bane ya tambayeshi ko zai iya buga gasar cin kofin duniya.

Tun bayan komawarsa Liberpool dai tauraruwarsa take haskawa inda ya zura kwallaye 32 a cikin wasanni 38 na gasar firimiya sannan kuma ya zura kwallaye 10 a gasar cin kofin zakarun turai.

A karshe dan wasan ya ce yana fatan zai bugawa kasarsa ta Masar wasan farko na gasar da zata fafata da kasar Uruguay amma kuma ya ce sai abinda likitoci suka ce.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!