CBN Ya Shirya Fara Sayar Da Kudin Chana — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

CBN Ya Shirya Fara Sayar Da Kudin Chana

Published

on


Sakamakon yarjejeniyar da aka kulla a watan Mayin shekarar 2018,na musayar kudi tsakanin Bankin alumma na kasar Chana (PBOC) da babban bankin kasa (CBN) za a fara sayar da kuin kasar ta Chana ga dillalan da aka amince dasu.

Idan za a iya tunawa, a cikin watan Mayu ne CBN ya rattaba hannun da bankin na alumma na kasar Chana mai suna (PBOC).

Yarjejeniyar zata bayar da damar gudanar da kasuwanci a tsakanin kasashen biyu da kuma kara karfafa kudin musaya na kasar waje, inda wannan ya sanya Nijeriya ta zama ta uku a nahiyar Afrika bayan kasar Afrika ta Kudu sai kuma kasar Masar da itama ta rattaba hannun da

kasar da Chana.

Yarjejeniyar tsakanin bankunan biyu zata baiwa kasashen biyu damar musayar kudi da suka kai jimmalr  biliyan sha biyar ko  naira biliyan 720 ko kuma sama da haka a cikin shekaru uku masu zuwa.

Har ila yau, jarjejeniyar, za a iya kara fadada ta a bisa yadda kasashen biyu suka amince.

Daraktan sashen kasuwancin kudi na  CBN Dakta Alban Ikoku ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar alhamis data wuce, inda ya ci gaba da cewa, yarjejeniyar ta musayar kudin, hakan zai bai wa bankunan biyu   damar daukaka kasuwanci da zuba jari a tsakanin kasashen biyu ta hanyar saye da sayar da takardar kudi ta Yuan ta kasar ta Chana a bisa takardar kudi ta naira.

A cewar CBN, jarjejeniyar zata kuma yi amfani da ita wajen dorewa akan kasuwar kudi wadda aka sanya rai cewar bankunan zasu amince da hakan.

CBN ya kara da cewar, don samun dama shigar daukacin dillan da aka amince dasu a cikin harkar zasu bude asusu na  Renminbi wanda ya yi daidai da bankin tare da kuma shawarar CBN itama  tare da bayanan asusun ta na Renminbi wanda kuma zai iya kasancewa da banki na cikin gida ko na waje dake kasar  Chana.

Wadanda suke da nufin shigo da kaya daga kasar Chana, zasu karbi takarda ta shigo da kaya a matsayin takardun da ake bukata na yin rijista don samar da kudin musaya na kasar waje na saye  wanda ba wadda za a yi amfani dasu bane wajen biya akan cinikayya ba wanda kuna

wadanda zasu amfana ba daga kasar Chana suke fito ba.

A cewar CBN, dillan da aka amince baza su bude asusun banki wanda baya aiki ba a dikin asusun bankuna na masu yin ajiya ba.

Don cimma wadannan jarjejeniyar, dillalan da aka amince dasu zasu dinga ajiye kudi a bankuna da kuma bankunan ‘yan kasuwa.

A cewar CBN sayarwar ta  renminbi, za a dinga yin ta ne kawai don baiwa kasuwanci goyon baya ta hanyar cinikayya, inda bankin ya kara da cewa, masu shigo da kaya da kuma fitar dasu, zasu ci gaba da biya kudin tara akan kayan da aka shigo dasu da kuma kayan da aka fitar baki daya.

Dillalan da aka amince dasu, ana bukatar su tattala kudi a cikin awowi saba’in da biyu daga ranar da aka saba, haka kuma dole a dinga maido da kudin zuwa ga CBN don sake saye akan farashin na bankin.

CBN ya kuma sanar da cewar, zai dinga cirewa daga dillan  da aka amince dasu a cikin babban asusun banki na ajiya a ranar da aka bayar da dauki wanda ya yi daidai da naira a bisa bukata ta renminbi.

CBN yana da ‘yancin kin sayarwa idan a ra’a yin sa ba’a bayar da farashin da  for the don tabbatar wa a tsaknin takarfar naira da kuma takardar Yuan ta musaya wanda  CBN zai iya zabar wani dauki babba na kasuwa ko sayarwa na kudi ko na gaba zaya.

Advertisement
Click to comment

labarai